Sashe 57
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
karanta yayi tsaki, shifa ya fara gajiya da shirin nan, yanzu mace zai fada ma wannan abunda Armstrong ya rubuta? Raini ne be so, to raini ma na yaushe tunda har zai kalla wannan yar karamar yarinyar ya kirata da "*my Forever *" dole ta rainashi ko nan gaba, balle yanzu wannan kalamen da Armstrong ya typo mai, wai ya ma Ziyada forwarding, guntun tsaki yayi ya mata forwarding, kalamai ne masu ratsa zuciya, be san ta inda zai fara maganganu da mace ba, be san me ake ce ma mace ba, tun daga randa ya hadu da Ziyada, a fili ko a waya, duk abunda ya fada mata, shirin Amstrong ne, sai abunda aka karanto mishi yake karanta ma Ziyada shi, sai ka rantse da k'wak'walwarshi yake karanto mata, tsaki yake tayi, wannan shine hardest pretense, yana jin wani iri a duk lokacin da ya ma Ziyada wani maganan k'auna, ko na So, tsaki yayi ya kwanta kan Gado. Ta fito first lecture dinta tayi receiving message dinshi, kalaman Soyayya ne, sai a karshe ya sanar da ita ba zata samu ganinshi ba sai nextweek saboda yaje wani aiki a Abuja, zatayi missing dinshi sosai, saboda a 'yan kwanakin nan, tayi sabo dashi ba na wasa ba, reply ta mishi da "take care of yourself for me, i'll miss you Handsome". Text din na shiga ta latso Majeed tace mishi "na gama lectures" ya shaida mata gashi nan zuwa shi da Najwa. * Ta Moneygram zata karbi kudin da Paapa ya turo mata, Najwa ta bada Details din da Paapa ya mata sending, tayi claiming ownership Kudin da ya turo 300usd kusan duba dari da goma a kudinmu na Nigeria. (MoneyGram: Account ne da banks ke budewa k'ark'ashin kasashen Waje, Normally In zaa turo maka kudi daga India Misali kana Nigeria, ta Moneygram zaa tura ma, bata account numbernka ba sunanka zaka bada, abunda akeyi, shine shi me turo Kudin, zai ba shi wanda zaa tura ma Kudin wasu Secret Questions and Answers don da Question and answers din za ka karbi kudinka in kaje Bank, in kaje Banki, zaa a baka form, sai kayi filling stating the senders details and amount da aka turo ma, you withdraw on the counter, with the Provided details, thats how you claim ownership, Ina Fatan mungane?). Tsayawa tayi a cikin Bankin gudun kar a samu matsala ko wani ya fizge mata kudi don ta har yanzu tana tsoron yan Nigeria, tana nan zaune cikin bankin har Majeed yazo, ya shigo "Pure Heart meyasa kika fito baki gaya min ba?" sadda kai k'asa tayi, ya girgiza kai tare da Murmushi yace "Oya muje mu dauko Zuzu a School, tace ta gama Lectures" gyada mai kai tayi, su ka fita daga Bankin, tana so ta bashi kudin amma ta rasa yanda zata bashi, rikewa dai tayi suka shiga mota, a cikin Motan ne yake bata labarin su Na'eela, har ranta ta tausaya ma Nura Kurma. ** Tana shiga Parlornsu taji k'amshin shi, tayi amanna shi ke da k'amshin nan, me zai kawo shi Gidansu? Amma dai turaren ne, da sauri tace "YaMaji munyi bak'i ne?" Majeed ya kalli gabas da yamma ko zai ga Na'eela ko Nura be gansu ba, yace "No, Me kika gani ne?" tace "kawai na tambaya ne" Majeed ya Murmusa yace "Mun k'aru ne, Naeela da Yayanta zasu dan zauna da mu for sometime" bata da damuwa, bata tsaya tambayan ko su waye ba, tace "barin je na watsa ruwa ta shige dakin Zaineema, Majeed ya maida Hankalinshi kan Najwa cikin muryan rada yace "Pure Heart kinyi breakfast kuwa?" Kai ta gyada mai, yace "PureHeart" ta daga kai ta kalleshi suna hada ido yace "Wallahi ina sonki" da sauri sauri ta shige dakin Hajjo tana dariya, Ya bita da kallon k'auna. * Da rana Zaid ya leka Parlo ya ga ba kowa, cikin sanda ya fita, har ya fita faga gidan ba wanda ya ganshi, Cikin Motan Amstrong ya shige, da yake Motan na da Tint, yana shiga ya sauke Ajiyar zuciya "i hardly breathe in there (da k'yar nike numfashi a cikin gidan)" dariya Armsyrong yayi ta yi, sai da Zaid ya wurga mai harara, da sauri ya juya baya ya dauko Basket, ya bubude ya zuba mai a plate, bayan ya ja mai kujera baya, kamar mayunwaci Zaid ya fara cin Abinci, sai da ya ci ya k'oshi, kafin ya dora da gwangwanin kalan lemun da yake sha, Amstrong ya bashi powder din da ya kawo mai, ya mai bayani cewa a abinci za a zuba, ya karba, Amstrong ya tambayeshi in ya ga "Ziyada" harararshi yayi ya bude K'ofa ya wuce, Amstrong ya bishi da daria, sai da ya shige gida Amstrong ya ja Mota ya wuce. Kamar baki, yana shiga Parlor sai ga Ziyada ta fito daga dakin Hajjo, kallon kallo suke yi, Ziyada ta fara jin k'amshin nan, mutane basu dameta ba, amma sai ta samu kanta da ce mai "Ina wuni" shiru yayi kamar be ji ta ba, a ranta tace "ko dai be ji ba?" ta bude murya ta sake cewa "ina wuni" sai ma ya kawar da kai kamar be ga kowa ba, Ziyada ta samu kanta da jin ba dadin rashin ansa gaisuwarta, ta bude baki tace "Ina wuni?" kamar dole, "wannan kurman Banzan ki ke gaidawa? Mummy ce me fadan hakan, Ziyada tace "Mummy ban gane ba" Mummy tace "baki ga wata kazama dakin Hajjo ba, Yayanku ya kawosu, wai basu da gida waye waye, shi me Orphanage house, ko ince shi me Safety House, duk wanda be da gida ko yake neman taimako sai ya kwaso ya kawo gidan nan, nan gaba Mata da Miji da Yaranta zai kwaso, wannan Kurma ne, nan gaba sai gurgu, kuturu ko makaho, ko wa yace ma Boy ana taimakon mutane yanzu, wasu zaka musu dare su maka rana, hausawa na cewa tsintaciyar mage bata mage" ina sam hankalin Ziayda baya kan Mummy, a hankali take takawa gaban Nura, tausayinshi ya mamaye ranta, Allah ta tuba ya zaa ce wannan kurma ne be ji be magana, bak'i ne, amma ta ga kyaunshi, Mummy tayi saurin shan gabanta ta ja ta suka wuce dakinta. Da daddare Majeed ya ja hannun Zaid sukaje Masallaci Sallah, Majeed sai nan nan yake da Zaid har suka dawo gida. Zaid ya ma Naeela text cewa ya ajiye mata powder din da zata zuba musu abinci gobe, yana nan karkashin dogon kujera, wurin sha daya da kowa yanna daki ta fita ta dauko, ta boye a zaninta, Washegari bayan Yara sun tafi School, Mummy na Abinci, Naeela ta faki idonta ta zuba maganin a Abincin nan, bayan sunci Abincim ko mintuna goma ba a rufa ba, suka buge da bacci, daga Mummy, Majeed, Hajjo, Zaineema da Daddy banda Najwa da ko fitowa batayi ba, saboda tana Azumi, Bedroom dinsu Mummy Zaid ga nufa ya fara bincikenshi hankali kwance, ya kusa mintuna sha biyar be ga wani abu me amfani ba, tsaki ya buga da k'arfi, duk girman gidan ba komai ciki, efforts dinshi zai zama a banza, so yake ya mallaki gidan nan ko ta halin k'ak'a, ba wani takardun Gida ko wani abu, aikin banza yakeyi kenan? Bata lokacinshi yake yi a gidan nan? To zamanshi a gidan be da wani amfani, rai a bace ya fita ya koma dakinsu, yanzu ya zaiyi, meye abunyi? Wani tunani yazo mishi, why not ba zai tsaya ya ga ya shariar Mairo da Nakowa zai kasance? Sai yayi using shariar akansu, in Nakowa bai ci Shariar ba to duk wani plan dinshi zai rushe, Nakowa ne last hope dinshi kan Gidan nan, Allah yasa yaci Shariar kawai, zaijira tunda Jibi ne zaa sake zaman Kotun. **** Bayan kwana Daya**** Ga yanda Najwa ta fuskanci Na'eela, ta gane Yarinya ce mai Ilimi, duk yanda Naeela ta so maida kanta Jahila wacce bata san komai ba, Najwa ta gane akwai Ilimi tattare da ita, ba dai tace mata komai ba, shiyasa duk yanda Naeelah ta so jin k'wakwaf kan dangantakarta da yan Gidan ta k'i gaya mata, kawai ce mata takeyi ita bakuwa ce, har yau Najwa bata hadu da Nura ba. Naeela ta kan ba su labarin Kurumtan Yayanta, harda kuka saboda tausayi Najwa da Hajjo keyi. ** Idan zatayi waya dasu Maama ta fiso taje BQ don nan zatayi waya hankali kwance, in daria zatayi to tayi da kyau, in kuka zatayi sai tayi da kyau, da sauri sauri tayi hanyar BQ, daga nesa ta hango bayan mutum mamaki take waye wanan? Saboda daga ganin bayan ta san ba Majeed bane, Majeed yafi wannan tsawo, waya yakeyi, kawai sai ta samu kanta da labewa bayan wani bishiya ta kasa kunne tana sauraron abunda yake cewa, "Arm, am sick and tired of this house, no aircondition, well there is but its outta gas, it is useless(Ni nagaji da gidan nan, ba Ac, ko da yake akwai amma ba gas, be da amfani)" "ya buga tsaki saboda abunda Armstrong yace " Yeah One more Day, until they are done with the Court, they'll see me for who i truly am, maybe not(Eh saura kwana daya, da sun gama da Kotu, za su ga ko ni waye, kila kuma ba a lokacin ba)". Gabaki dayansu sukaji muryan Majeed, a hankali Zaid yace "will call u back Arm" ya tura wayar cikin Aljihhu, yak'i juyowa, Duk abunda yakeyi a idon Najwa, duk da taji me yake cewa amma sama sama, ba zata ce ga abunda yake nufi ba, tana ganin Majeed ya k'araso, Nura ashe kana nan, ya kamo hannunshi, yace "mu koma ciki" sokoko Nura ya bishi a baya. Abu daya Najwa ta fahimta, wannan shine Yayan Naeela, Wannan shine aka ce Kurma, amma ita shaida ce tayi magana, karewarta waya taga yakeyi, haka kurum taji bata yarda dasu ba, da kunnenshi taji yana magana maana ba kurma bane, and one thing is clear, they are after 'yan Gidansu Majeed, ba zata bari su cuce su ba, ba zata bari su zalunce su ba, zata saka musu ido har sai ta gano me suke so da su Majeed, da ta gano su zata yi exposing dinsu, a baiyane tace "Nura, i wont let you