← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 54 OF 128

Sashe 54

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

mai formatting komai" Daddy yace "da sauki tunda ba su mishi komai ba, kaje ka ganshi ko?" Majeed yace "eh naje, daga chan nake yanzu" Mummy ta lula duniyar tunani kawai tace "Alhaji Nakowa ne ya turo mishi barayin nan" duk suka bita da ido tace "haba, ga abu a baiyane, Alhaji Nakowa ne, ya zaayi ace Armed Robbers su tare ka, su karbi wayanka suyi wiping komai? Su maida maka wayanka ba tare da ko dunguran ma kai sunyi ba? Wallahi they were after that recording" Daddy yace "Maryam, ki tsarkake tunaninki, kila ba haka bane, maybe they were after something else" Hmm Mairo tace, ita dai tana da tabbacin Alhaji Nakowa ne yayi aiken nan, saboda recording dinnan, su Daddy ba zasu gane ba, don ba su san wainar da ake toyawa ba, saboda an kai mai sammaci shiyasa yake neman hanyar salwantar da evidence dinsu ko? Dole tayi taka tsantsan, kawai dai su hadu Kotu, sunci nasarar kwace na hannun Aliyu, amma ita ba zata bari ba, bari ta kira Lawyer dinta ta tura mai, komai ta fanjama fanjam kawai. B A Y A N K W A N A B I Y U Kullum sai sunyi waya da su Maama, ta sa Kaveri ta nemo mata numbern Aisha, suna chatting sosai, ta bata labarin abubuwam da suka faru da ita bayan rabuwarsu, Aisha tace "i told you so ai, yanzu you need to be very careful, ki kula da kanki" nan ta sake bata shawarwari. kwana biyu ta na cikin walwala, ba ita kadai ba, duk Ilahirin Familyn Abba Abu, ba su da wata damuwa, kwana biyu, suna zaman su lafiya, ina ma wannan farinciikin dawamame ne? Ina ma su kasance haka har karshen rayuwansu, ba su da damuwa, ba su da wata matsala. Kullum Majeed ke kai Ziyada Makaranta ya daukota, da Muhsin ya dawo Makaranta, zai rugo da gudu wurin Najwa wai ta koya mai Homework, zata karba tayi guiding dinshi, in bata gane ba sai ta tura shi wurin Ziyada, ita kuwa Zinatu tafi k'arfin Najwa ta koya mata Homework, haka take damun Daddy ko Ya Majeed su koya mata, don ta san ko kallonta Ziyada baza tayi ba. ** Kamar mara gaskia, Mummy na fita da Mota yayi Sallama dakin Hajjo, Hajjo tace "Abdallah, har ka dawo daga kai Ziyadatun Makaranta? Yace " Eh Hajjo, jikarki zaki ara min, zamu dan fita" Hajjo na lura da Najwa, tunda Majeed ya shigo dakin bata da sauran sukuni, Hajjo ta murmusa irin yanda manya keyi, tace "a dawo lafiya" Najwa tayi kamar bata ji me suke cewa ba, sai da Majeed yace "Muje ko Pure Heart?" kanta a kasa ta tashi, dama akwai Hijab a jikinta, tace "naje" Hajjo tayi dariya tace "bahausa, kin tafi zakice ba naje ba" sukayi dariya. Kasancewar Daddy ya fita da dayan Motar ya sa Majeed tsaida musu keke Napep, ya dan kallota yace "kin ta6a hawa?" kai ta gyada mai, yace "Oh hakane ko? Tuptup kuke ce mai a India" murmushi kawai tayi, yace "PureHeart, ki dinga bude baki kina min magana kinji?" ta dan turo baki, yace "you look cute" ta sa Hannu a fuska ta rufe, yayi daria, yace da me adaidaita sahu, "Rijiyar Zaki zaka kaimu, ta wurin Islamiyan Mallam Sanda?" suka shiga suka fara tafiya, shiru shiru ba wanda yayi magana sai Majeed yace "baki ce ina zamu ba?" tayi shiru yace "Ehen Ina jinki" a hankali tace "i trust you" murmushin jin dadi yayi. Daidai Islamiyan suka tsaya, naira 500 ya ciro ya ba mai adaidaitan, yace "jirani ina zuwa" gyada mai kai tayi, yayi gaba ta bishi da ido. "Assalam Alaikum" Majeed yayi Sallama a gaban shago, Wani dan Dattijo mai sanye da Alkyabba fara da Charbi zungurere ya amsa mai da "Waalaikum Salam, Bismillah" Majeed ya dan sunkuyar da kanshi don K'ofar bata da tsayi ya shiga, bayan 'yan gaisuwa, Mallam Sanda yace "saidai ban ganeka ba" Majeed ya dan Murmusa yace "AbdulMajeed ne, na wurin Alhaji Abba Abu" Mallam Sanda ya fadada fararsa, "to to, AbdulMajid ne? Haka ka koma? Ka zama magidanci, rabona da kai tun randa kazo min bankwana zaka tafi Makaranta Turai" Majeed ya Murmusa yace "gaskiya ne, an kwan biyu" nan suka sake kwasar wani gaisuwan. "Allah gafarta Mallam, tare nake da wata a waje, Mahaifanta na tare da wani Matsala, haifaffun Nigeria ne, amma rana tsaka suka hada kayansu suka bar K'asar, yanzu ba su iya tuna komai game da Nigeria, ko Garin da suke ba zasu iya tunawa ba, kuma duk randa suka shirya zuwa Nigeria, InshaAllahu sai wani abu yayi sanadiyar rashin zuwan su, shine nake so in akwai taimakon da zaa iya yi?" Mallam Sanda ya danyi shiru, chan yace "Shigo min da yarinyan" Majeed ya tashi ya fita, tana nan rak'ube, yace "PureHeart, ki shigo, munzo wurin Mallam ne, zai miki tambayoyi, ki bashi amsa kinji? Trust me, everything will be fine". Ta bi bayanshi, suka shiga Shagon, kusa da AbdulMajeed ta zauna, ta gaishe shi, Mallam Sanda ya dinga mata tambayoyi tana bashi Amsa iya saninta, Mallam Sanda ya kalli Majeed yace "Kurciya ce aka musu" Majeed yace "Kurciya?" Mallam ya gyada kai alamun eh yace "Kurciya ce, ana yin shine a lokacin da ake so a nesanta mutum da wani wuri, ko a musu farakku, maana a musu katanga, an shiga tsakaninsu da Mahaifarsu, Yanuwa da Abokan Azziki, yana iya yiwuwa wani ke hassadarsu, ko k'yashinsu" kan Majeed yayi zafi, yana mamakin mutanenmu, how can someone be so heartless? Sai yaji ya k'yamaci hassada a zuciyarshi, ya kyamaci me hali irin na Hassada. Majeed yace "Mallam, yanzu me abun yi?". Mallam Sanda ya dan Muskuta yace "Addua, Addua zamu tayi, da Ikon Allah da yardan Allah Sihirin zai karye, kila ayi k'aik'ayi koma kan Mashekiya, maana abun ya koma kan wanda ya musu, ni da Dalibai na zamu sauke Alkurani Maigirma har lokacin da zasu baiyana, ba zamu bari ba, har sai randa suka iya tuna ko da sunan garinsu ne, Yayanta kuma, da Yardan Allah, indai yana cikin K'asa Nigeria, in har da ransa, da Izzar Allah zai baiyana kanshi a duk inda yake, kar ku sama zuciyoyinku komai, Ikon Allah ya wuce tunaninku, da Ikon Allah zai baiyana Yayanta, a Mace ko a Raye". Ya k'ara da fadin suma su dage da Addua, k'arfin Addua zai bayanasu duka, Majeed ya hau Godia, ya ciro 5000 ya ba Mallam, Mallam ya girgiza kai yace "aa Abdul, dauki kudinka, taimako ne, aka ma wasu bare kai?" Majeed ya girgiza kai yace "Aa kar muyi haka da kai Mallam, Sadaka ne, a sai ma masu Sauka ruwan Sanyi" Mallam yayi Murmushi yace "Allah ya saka da Alheri Allah ya sa a dace, Najwanatu Allah ya Baiyana miki Yayanki, Allah ya sa Mahaifinki suci galaba kan masu son ganin bayansu" duk a tare suka amsa da "Ameen". A lokutta da dama, Allah na daura ma bayinsa Soyayyahn junansu, balle ma in suka maka abunda ba zaka taba mancewa ba, zakaji duniya ba wanda kake so sosai matuk'a kamarsu, hakan takasance da Najwa, tana jin AbdulMajeed Abba har cikin ranta, tun kafin ya furta mata So, bayan ya furta mata kuma sai soyayyarsa ta ninku a Zuciyarta, a yanzu kuwa da ya bada himma wurin taimakawa don haduwanta da Yayanta da kuma Mahaifanta, sai taji a ranta kamar dama don ta hadu da Majeed ne tazo Nigeria, ya mata abunda ba zata taba mancewa ba, duk da bata ga an samu Nasara ba, amma ina laifin wanda ya so taimaka maka da k'uddirinka?, wanda ya dauka matsalarka ya maida nashi? Wanda ya maka hallaci tun daga farkon haduwarku? Zuciya bata da k'ashi, kuma Zuciya na son mai kyautata mata, ta ya ba zata so AbdulMajeed Abba ba? Taya ba zata so ta rayu dashi ba?. Duk cikin Keke Napep take ta wannan zanttutukan a zuciyarta, muryanshi taji yana waya. Hello Zuzu, erhm, kiyi hakuri kiyi taking A daidaita Sahu, Mummy ta fita da Motana, but idan ta dawo zanzo in dauke ki" bataji me Ziyadan tace ba, sai jin Majeed tayi yace "are you sure you'll be OK alone?" OK be safe, i'll see you when you get home, I love you Kinji?" da Murmushi ya kashe wayan. Soyayyan da ke tsakanin Yanuwan na burgeta, ina ma zata ga Yayanta, zai kula da ita kamar yanda Majeed ke kula da k'annenshi, Allah ya baiyana mata Yayanta Zaid. "PureHeart" taji yace, ta dago kai ta kalleshi ido cikin ido, yace "Ina so in k'arashe k'arshen rayuwana da ke, Ina matuk'ar k'aunarki, Kina sona?" kanta ta chusa cikin cinyoyinta tana Murmushi mai sauti, yace "PureHeart, meyasa kike min daria a duk lokacin da na gaya miki abunda ke Heart dina? Am i some laughing Stock?" da sauri ta girgiza kai, yace "then ki gaya min, kina sona? Zan fahimceki in kikace Aa, but right now i need an answer" shiru tayi, har ya cire ran zata tanka, ya maida kallonshi kan Titi, har sun iso kwanar Gida ya ji tace; "tum meree khushee ho, aap hamesha ke lie mere hain, Mein tumseh bahut pyar kharta hoon (Kaine Farincikina, You are my Forever, Ina matuk'ar Sonka)". " Ehen, Ina jinki, Fassara min" shiru tayi, ta juyar da kanta tana kallon hanya, ya dan daga kafada yace "Kawai dan anga banjin Indianci sai a dinga zagina ko?" ta rausayar da kai tace"bafa zaginka nayi ba" yace "to fassara min, sai in Yarda" da ta lura tsokananta yake, sai ta kulle ido tana girgiza kai, Kallon k'auna ya bita dashi, duk da be san ma'anar abunda ta fada ba, ya tsinci kanshi da jin dadi, da Murmushi baki kamar Gonar Auduga, har Mai Adaidaita ya iso Gidan, da sauri ta sauka ta shige ciki da saurisauri, gudu gudu". ******** Fitowarta lecture kenan, kasancewar sabuwa ce a Makarantar kuma dai bata da saurin sabo, take tafiyarta ita kadai cikin yanayinta na sanyi, straightahead Gate ta nufa, don YaMaji ya sanar da ita ba zai samu zuwa yau ba, har ta fita bakin gate taga Mutane na ta kai kawo, hayaniya, ko ta tsaya nan ba zata samu Keke Napep ba, kawai sai ta fara tafiya, tafiya takeyi kanta
Chapter 54 · 0% Book details