Sashe 9
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
A ranar da Mairo taji cewa Yesmin zata tafi k'asar waje, Ihu ta saka don ji take kamar tayi hauka, kasa boye bakincikinta yayi har Abba na mata dariar mugunta yace "ba yanda zakiyi uwar Hassada, haka zaki ta kallo har zuciyar ki ta fashe".
聽聽 Haka sukaje K'asar Italy sukayi sati biyu kafin sukayi sarin abubuwan da suka kaisu aka turo ta Ship, tsaraba sosai tayi ma Zaid da Abdul komai iri daya, daga Italy suka wuce Makka sukayi Umra kafin suka dawo Nigeria kai tsaye Sabon Gida suka tare.
Washegari zaa yi Waliman bude Sabon Shago da Sabon Gida.
聽 聽 聽 Hankalin Mairo a tashe da taga Babban Gida kamar wannan, Hassadar ta ya motsa ta shiga kushe gidan wai gida kamar gidan yan yankan kai,yan walima suka bita da ido, kallon ko wani lungu da sak'on gidan takeyi zuciyar ta ba dadi, wani zazzabi mai zafi take ji, zuciyarta聽 bata farfado daga tashin hankalin da ta shiga ba aka dunguma a kaje Sabon Shago. Daga nesa ta hango Wani katafaren Gini wanda ya k'awatu da hasken Fitila, idonta ya kai ga SADA ABU AND SONS FURNITURES, a tare aka shiga, Alhaji Sada baki har kunne, Alhaji Abba da Yesmin na gefenshi yana nuna ma mutane wurare a cikin shagon, wurin sai kanshin Italian furnitures yake tayi, wurin ya k'ayatu, ga maaikata, baki wangale Mairo ke tunanin yaushe Sada yayi Acheiving聽 haka,聽 bata damu da yawan mutanen da ke kallonta ba ta daura hannu a ka tana zubda hawaye, harsada ba zai barta ta sake mintuna ko daya a gun ba, da sauri ta juya ta fita daga shagon, ta tsaida taxi tace a kaita Dorayi.
*
聽 聽 "Hmm kin ban mamaki, wai yanzu akwai abunda zai gagareki Mairo Sani?, duk kaifin basirarki? Har yanzu baki gama da Yesmin ba?" wlh da nice ke da tuni na yarda k'wallon Mangoro na huta da k'uda"Mairo tace"uhmm Wallahi Aliya abun sai a hankali, duk na rasa yanda zanyi,Sada na controlling Mijina, Mijina na k'arkashin shi, sai abunda Sada yace yakeyi, rannan harda marina yayi saboda Sada" Laiya ta rik'e baki, Mari? Mari fa kikace, Dank'ari Mak'ari, nan gaba mugun bugu zai miki ya barki kwance" "ya zanyi Aliya?" Aliya tace "tsaya kiji in baki labari,Mijina ke da Arziki duk cikin familynsu, kowa ya kwaso shara kan Mijina yake zubarwa, yayi Hidiman Gidanshi, yayi na yanuwanshi,daidai da ruwansha shi ke siyan musu, komai yake musu, ni ko inda akwai abinda na tsana be wuce yanda yake musu bauta ba, don a guna bauta ne yake musu, aiko na yi shige da fice na, na rusa lamarin, yanzu da nike miki magana, Ba uwar da yake musu, ya tara daga ni sai 'yayana, In gaskia tazo a fadeta, kin ga da Mijinki ne k'anin Mijina da ba zan dinga barinshi yana muku Hidima ba, kowa yaci gashin kanshi, Lallai Yesmin na k'ok'ari da har ta ke bari ya muku Hidima" da sauri Mairo ta katseta, ta san halin Aliya, yanzu zata gaya mata magana tace "Hegia, nima ina mamakin kauda kai irin na Yesmin, yanzu dai gaya min, ta ya kikayi shige da fice har Mijinki ya zama me jin maganarki?" ko shakka Aliya tace "gyara zama ki sha labari, bani kunnenki" nan ta mata bayani a kunne, suka kwashe da daria suka chafe hannu."Shegia Aliya Bashir, ba Allah a ranki" tace "tsaya nan,kallon ruwa kwado ya miki k'afa" Mairo ta nisa tace "yanzu kina tunanin akwai halin Abba ya mallaki dukiyar Sada gabaki daya?" Aliya tayi wuf tace "tsaflillahi" ke dai kawai ki shirya gobe Asabar na rakaki Marmara.
*
聽聽 WASHEGARI
K'arfe Biyu da Rabi ya ma Alhaji Sada, Yesmin da Hajjo gidan Alhaji Abba, sun zo daukarsu zasu tafi Visiting dinsu Zaid,dama Alhaji Abba ya shirya,ya fito da Zaineema,Yesmin tace "Zainee ina Mamarki?" Abba yace "Mairo bata jin dadi tun safe, tace a gaida yaran". "Allah sarki in mun dawo ma dubota" cewar Alhaji Sada, ya ja Mota suka nufa makarantar HIG.
Tana jin tashin Motarsu ta sa6i gyalenta, ta kwashi kudi mai yawa ta kulle gidan ta fice, taxi ta hau ta nufa Dorayi gidan Aliya Bashir.
*
K'aton Carpet aka shimfida a k'asa k'ark'ashin Bishiya, duk suka Zube a k'asa, Sosai Zaid ya rame, dama tunda AbdulMajid ya dan fishi kumari, Zaid kwance jikin Mamanshi, Baba Abba yace "yadai yarona?" AbdulMajid yace "Baba tun jiya Zaid yake ta kuka,kuma yace baisan meke damunshi ba" Hajjo tace "nidai ince bai jin dadi don tun da yazo be yi wani magana sosai ba kuma be dauki Zaineema ba" Sada yace "abunda zai hana Zaid daukan zaineema ba k'aramin abu bane" Yesmin ta kalli danta tana karantar shi, shirushiru ba halinshi bane, a hankali ta lumshe idanunta ta bude tace "Zaid baka da lafiya ne?" Kai ya girgiza, tace to me ya sameka? Yace"Mama ni gida nake so, i want to be with you" tace "haba Zaid, ko term daya ba kuyi ba, kayi hakuri, baga danuwanka ba kuna tare? Kanaso babanka yayi asaran kudin Makaranta?" ya girgiza kai, yace "nidai ku tafi dani yau ku dawo dani gobe"ina so inje gida ne" Baba Abba yace "Zo, ya tashi ya je gunshi yace "Bakason boarding?" ya gyada kai yace "na ma Alk'awari ba zaka dawo 2nd term na, zan chanza ma makaranta a dawo da kai kuda da mamanka" nan ya danji dama a ranshi, abinci Yesmin ta zuba musu duka sukayi lunch, har yanzu Zaid bai warware ba, har Lokacin tafiarsu, ya shiga kuka sosai, Visting dinsu na farko beyi kuka ba, sai wannan, Yesmin hankalinta tashe amma daurewa takeyi balle da ta ga ya mak'alk'aleta yana kuka sosai kamar bazai sake ganinta ba, itama hakan takeji kamar ba zasu sake haduwa ba a hankali ta rada mai a kunne "I love you Zaid, dont you ever forget that, take care of yourself" kai ya daga mata ya sake fashewa da kuka, ya karya musu zuciya duka, Sai da Alhaji Sada ya tsawatar mai kafin ya saketa, sannan ya rungume Babanshi shima, haba Sojan Baba Abba, ka bar kuka mana, bakaji yace zai cireka ba? Ya gyada kai, "maza share hawayenka" ya kalli AbdulMajid yace ku kula da junanku" suka juya suke wuce, Yesmin na waigen danta, sabon kuka yazo ma Zaid ya ruga da gudu cikin makaranta, waiyo ji take kamar ta bi bayanshi.
聽 Marmara
Mallam danlami yace "Naji bayananki, me kikeso ayi?" ta kalli Aliya, Aliya ta mata alamun kiyi magana tace "Ina so Mijina ya daina min gardama, ina so yayi duk abunda na sashi, ina so yayi duk abunda nikeso, ba ma shi kadai ba, dukkan su, duk wanda nace kar yayi abu, kar yayi, inaso ,su zama mai jin maganata a ko yaushe" Mallam yayi dariya yace "angama sai me kuma?" tace "aa Mallam a fara da wannan, in an ci nasara sai in dawo" Mallam ya daka mata tsawa yace "kina da tantama ne? Kina tunanin aikina baya ci?" da sauri ta girgiza kai, Aliya ta mata nuni da ta badhi hakuri, nan ta sake bashi hakuri, ya hakura ya buk'aceta da ta sake tambayan wani abu, tace "So nake duk dukiyoyin Sada ya dawo k'asan Abba, komai da ya Mallaka ya mallaka ma Abba" yayi dariya yace "ke da kikace bakya son kowa ya maki gardama, ai wannan aikin kine, ke zaki sa shi duk abunda kike so, kuma dole duk suyi abunda kikeso, tashi kije komai zai tafi kamar yanda kikeso, ni aikina ban bada magani, ban bada komai, ni zan miki aikin da kaina ku tashi ku tafi zan fara aiki". Suka mai Sallama bayan ta Zube mai duk kudin da tazo dasu tace zata dawo bayan aiki.
聽 **聽 聽 **聽聽 **
聽聽 Ghen! Ghen! And this is just the begining.
Hello Bibilicious Freaking Fans, show me love Please Vote and comment.
#1love
#ADAY
#Bibiliciousfreakingfans
#anatare
#nagode
Biebee Isa
聽
[11:32, 25/09/2017] 鈥�+234 803 414 9368鈥�: 锟斤拷A DADE ANA YI....sai gaskia锟斤拷
NA
BIEBEE ISA
庐NAGARTA WRITERS ASSOCIATION (NWA)
Pg7鈨�
Komai ya Chanza a ranar nan, Rayuwar su ta chanza a ranar nan.
Mairo na daga daki ta lura da chanjin Abba, da ba ta isa ta sa shi yin komai ba, duk magiyarta in beyi niyya ba bayayi,da ta lura da alamun da Mallam danlami yace mata zata gani, sai tace bari muga in aiki ya fara ci ta bude baki tace "nagaji wallahi, barin huta In miki wanka Zainee" da sauri Alhaji Abba yace "barin mata" tace "to ba dai ruwan zafi, barin tashi in daura" da sauri ya tashi yace "bari na dafa, huta". Yana fita ta daka tsalle tana murna, ah bari ta ga yanda komai zai tafi cikin kwana biyu kafin ta fara aiwatar da aikinta.
*
Duk yanda take zaton aikin Mallam ya kai to ya wuce nan, sai ga Baba Abba da wanke wanke da shara daki, a cikin kwanaki biyun nan, yanda ka san rak'umi da Akala haka yake binta da duk abunda takeso,sannan taje gidan Hajjo, tace da hajjo " tanaso ta ci danwake" rannan Hajjo bata dan jin dadi amma haka ta tashi ta jefa ma Mairo danwake tana zaune tana karkada k'afa. A nan ne dai ta tabbatar da aikin Mallam yayi sosai, don haka zata aiwatar da Ayyukanta, Burinta ya kusa cika.
Kamar ko yaushe,in Alhaji Sada na gari sai yazo gidan Alhaji Abba bayan Sallahn Asuba, haka yau ma ta kasance, suna k'ofar gida suna fira Mairo ta fito, Abba ta kalla tace "koma ciki" ba musu ya tashi ya shige ciki, Sada da mamakin abun da ya faru, ya dai wayance da cewa "Barka da Safiyya Maman Zaineema" fuskarta daure ta kalleshi ido cikin ido tace "ina important documents dinka? Ina ownership documents dinka na Sada's furnitures, ina Makullan Shagunan ka da ka ta6a mallaka? Ina duk wani takaddu masu amfanin da ke gareka? Ina suke Sada?" samun kanshi yayi da cewa "wasu na gida, wasu na office, wasu na company" murmushi tayi tace na baka lokaci nan bayan Azahar, ka tattaro min duk wani abu da kasan ka mallaka, duk wani abunda zaka iya dauka, ka dauko ka kawo min,sauran kuma kar ka damu yanzu dai kayi yanda nace".