← Book details Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 43 OF 128

Sashe 43

Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read

Soyayyar da take mishi na nan dank'are a ranta, saboda shi ta k'i zaman Aure, Aurenta 3 tun lokacin tana fitowa saboda shi, amma kwatakwata bata gabanshi, ta san Sharrin Hajia Mairo ne, amma ta san wani wuri a zuciyarshi na sonta. "Hajia Aina'u kece a gidan mu, sannu da zuwa" muryar Daddy ke amo a kunnuwanta, ta lumshe idanu tace "Alhaji Abba, nazo muku Jaje ne, ashe abunda ya faru kenan?" da jimami yace "Wallahi kuwa, abu da haka yazo, kawai muka wayi gari muka ga wuri a rushe, kuma wai an saida filin" Hajia Ainau da tausayi tace " Allah Sarki, Allah ya saka muku, ya bi muku hakkinku, haka "Rayuwarmu* take yanzu, masu k'arfi sai su danne hakkin marasa k'arfi kuma gwamnati na kallo, Allah ya saka muku Alhaji" Sosai ta burgeshi ya amsa da "Ameen" cike da kissa tace "ina mutanen Gidan?" Daddy yace duk suna cikin Daki, ya ciro waya ya kira Majeed yace "kai fito ga Auntynka Aynarh tazo" Hajia Ainau ta maimaita 'Auntynka Aynarh' a ranta, dadi ya ziyarce ta, akwai Hope kenan, Jim Kadan Majeed ya fito daga Daki, da murmushi ya k'araso Parlor. "Aunty Ina kwana" "lafiya lao, Majeed Ashe abun da ya faru kenan?" Majeed yace "Wallahi kuwa Aunty" tace "Allah shi kyauta, ya tsare gaba" ya amsa da "Ameen" tace "Na ma Daddynka maganan Lecturing, bansan ko kunyi maganan ba" Majeed ya dan shafa k'eya yace "Eh munyi" tace "yanzu ka dauko min CV dinka, in tafi dashi" Majeed yace "Ok, barin dauko" ya tashi ya shiga ciki, bedside drawer ya jawo don dauko Folder dinshi, wayam, ba komai, da mamaki ya san da hannunshi ya ajiye a nan, nan ya shiga dubawa drawer drawer, be gani ba, ya dauko Jakkan Laptop ya duba be gani ba, Nana ya tada don tambayarta ko ta chanja mishi wuri, Nana ta hau inda inda, kwana 3 da suka wuce tana ta jiran wayan Wannan bawanAllah be kira ba, har ya fara ganin wautan ta na bashi ba tare da sanin ko da number dinshi ba, tsoro ya cikata sai tayi k'arya tace "bata gani ba" Majeed yayi shiru ya fita, yace "Aunty, zan kawo miki har gida, banyi photocopy ba" tace "Ok Yarona ba matsala, sai kazo" . Kamar daga sama suka ga Mummy gaban Hajia Ainau tana huci, Hajia Ainau ta murmusa tace "Hajia Mairo Ya gida ya yara? Ashe abun da ya faru kenan?" Mairo cike da masifa tace"tsohuwar Minahika, uban me ya kawoki? Jaje kikazo ko munfunci" Majeed yayi saurin shan gabanta ya ja ta baya"Mummy Please" ta bangaje Majeed tace "Tashi ki bar min Gida, kar ki sake zuwa mana Gida, tsohuwar kilaki" Hajia Aina'u ta mik'e da murmushi daidai yanda Mairo kadai zata jita tace "Zaki ga kilakanci duk randa na auri Abba, kashin ki zai bushe Hajia Mairo, ba kamar ki ba, ba Boka ba mallam zanyi taking over gidan gabaki daya, duk wanda ya biya allonshi ya wankeshi" ta dauki jakkarta ta bude murya tace "toh Hajia Mairo da Alheri, Allah shi kyauta gaba" Majeed ya bi bayanta, Daddy yace "Hajiya Aynarh, mungode Allah bar zumunci" abun mamaki ya kalli Mairo ya galla mata harara ya shige ciki. Baki bude Mummy ta bi Daddy da ido, wannan matar tana shiga hancinta ta k'udundune ita take ikirarin auren Abba, ji yanda Majeed ke binta kamar wani me neman gafata, aiko zata shayar dasu madaran mamaki. * Majeed yace "Aunty donAllah kiyi hakuri, bansan meyasa Mummy ke haka ba" H.Aynar ta murmusa tace "haba Majeed, bakomai Wallahi, inda sabo ma saba, so kar abun ya dameka please" murmushi yayi yace "Mungode Aunty" ta bude motarta ta ciro wani Envelop tace "gashi ko" Majeed ya mak'e hannu, tace "haba Majeed, kar ka min haka donAllah ka karba, nasan you are in need" Majeed ya sa hannu biyu ya amsa yana Godia, har ga Allah tana son Jinin Abba, sosai takeson Majeed, ta ja Motar ta ta wuce, sai da ya ga tafiyarta kafin ya shiga Gida. Cikin Dakin Daddy yayi Sallama, yana jin yanda Mummy ke balbale shi da Masifa, Daddy yayi banza da ita ya k'yale, Majeed ya girgiza kai, ya shiga da Sallama, Daddy ya amsa yace "har ta tafi?" Majeed yace "eh gashi ta bamu ma, dubu Dari ne" Daddy yace "Allah sarki Aynarh, harda dawainiya" haushi kamar ya kashe Mummy, wai yau Abba ke yaban wata, lallai tayi Sanyi, tana jinsu inda yake cema Majeed "Toh Allah ya saka da Alheri, sai kaje ka yi siyayyan Abincin Gida" yace "To Daddy" ya fita. Daddy be bi ta kan Mairo ba ya fice shima. * Add Vote Sahad ya fara zuwa ya kwaso Provisions kala kala, sai da ya cika booth da abinci, Duk yanda rayuwa ta zo musu ko ba komai ba zasuyi rashin Abinci ba na 'yan wattanin nan masu zuwa, yana tuk'i Najwa ta fado mai a rai, Salati yayi a zuciyarsa, cikin kwanakin nan tashin hankali ya hanashi tunano komai, reverse yayi ya dauki hanyar Rijiyar Zaki, jim kadan ya baiyana a k'ofar Gidan Hajjo. Sallama yayi tare da tura k'ofan, kutsa kai yayi, kamar ance ya daga kanshi daga gefe ya daga kai, gabanshi ya yanke ya fadi, idonshi kamar ya fado, tsoro ya mamaye zuciyarsa, abu kamar almara, da sauri ya k'arasa gindin Bishiyar Zogalen da ya ga Hajjo a kai inda take katso Zogale tana yaddawa a k'asa, murya na rawa yace "Hajjo, sauko donAllah, sauko" Najwa na jin Muryanshi ta fito da Murna, Hajjo bata so ganin Majeed ba a yanzu, saukowa tayi a hankali. Da farinciki Najwa tace "Ya Majeed" murmushi kadai yayi ya maida dubanshi ga Hajjo yace "Haba Hajjo, ya akayi kika iya hawa Bishiyan nan? Ba kya tsoron ki fadi? In Zogale kikeson ci da ba siyowa ya kamata kiyi ba? Kin kama kin hau bishiya, inta Allah ta kasance fa, tsautsayi da be wuce rana kika fado fa? DonAllah kar ki sake hawa Bishiyan, in Zogale ne kuka barin je Kasuwa in siyo miki daffafa ba sai kin sha wahalan dafawa ba" be jira amsarta ba ya juya. Hawaye suka gangaro ma Hajjo, Najwa tace "oh ashe besan ita ke saidawa ba" baki ta cire ta kira Majeed. "Ya Majeed" ba tare da ya juyo ba yace "Najwa ki tsaya yanzu zan dawo, barin siyo ma Hajjo Zogale da k'ulli" tace "to ina zakaje siya bayan ga Mai Zogalen nan ka bari a gida?" chak ya tsaya, ba wai don ya fahimci abunda take cewa ba, ya juyo a hankali yace "bangane ba" Hajjo ta mata alama da ido, Najwa ta tako har gabanshi tace "i mean, zakaje siyi Zogalen bayan me Zogalen gata ko dafawa batayi ba balle taje kasuwa ta saida" ganin be fahimtar abunda take cewa ya sa ta cewa "Hajjo mai Zogale sunan da Yan Kasuwa suka fi saninta dashi kenan, tunda nazo kusan 8days kenan, ban taba ganin taci wani abu ba sai Zogale kaga har ta koya min ci, wannan Tree din kullum sai ta hau ta tsinko Sai ta dafa, sai inga ta daka wani abu kamar dutse a turmi, what do they call it? Kuli? Yes kuli, sai na rakata Kasuwa ta saida, kullum fa sai mun fita, like every blessed Day". "Inalilahi wa ina ilaihir rajiun, Allahumma aajirni fi musibati wa akhlifni khairin minha" zuu ya zame k'asa ya dafe kanshi da hannunshi, Kuka yakeyi kamar ranshi zai fita, Hajjon ma Kuka takeyi, wai Kakarshi ke Tallan Zogale? Kullum sai tayi gangancin hawa Bishiya? Kakanshi? Maman Alhaji Abba Abu? "Ya Illahi" sai da ya ci kukanshi ya gaji, kafin ya rarrafa gabanta yana rokonta gafara kamar shi ya mata laifi, yana tausayin Babanshi, ya san yau Daddy ya mutu wuta zaije saboda yanda ya banzatar da rayuwar Mahaifiyarshi, rok'onta gafara yakeyi na ta yafe ma Babanshi, kuka takeyi sosai, Najwa na tayasu, da k'yar Hajjo ta tsagaita kukanta ta dago Majeed tace "Abdallah, kayi shiru, Babanka be min komai ba, tsakanina da Abba Addua ce kawai". "Wani d'an k'warai zai bar Mahaifiyarshi cikin wannan hali? Wani dan kwarai zai sharw Shekaru sama da biyar be ga Mahaifiyarshi ba kuma dukansu suna raye? Wani dan k'warai zai wofintar da Mahaifiyarshi?" Hajjo ta katseshi tace "kul Abdallah, ba yin Abba bane, ni na sani, wallahi ba yinshi bane, yanda na nuna ma Abba So fiye da danuwanshi, Wallahi ba yinshi bane kar ma ka zarge shi, na yafe ma Abba duniya da lahira Allah ya fiddashi daga halin da yake ciki". Majeed ya so ya gane me take nufi, amma zuciyarshi bata si ta aminta da zargin, yayi saurin kawar da tunanin a ranshi yace "Hajjo, kina da D'a kamar Abba Abu, kina da Jika kamar Abdulmajid, duk da muma Rayuwarmu na da dan targarda, amma kinfi k'arfin Tallar Zogale, kinfi karfin hawa bishiya, wannan Mutane suka san Asalin ki, Wallahi sai sun dinga la'anar Daddy, kuma wallahi Bakin mutane sai ya bishi, Hajjo ta faru ta k'are, kin gama Zaman Gidan nan, zaki koma gaban Danki, da Jikokin ki, Najwa Help me get her things". "Aa Abdallah kar ka min haka, ni da in taka k'afana gidan Abba, ka dai bari, barni a nan" Majeed yace "dagaske Hajjo ba zan barki nan ba, Wallahi Gida zamu tafi" Hajjo ta fashe da kuka tace "Mamarka da bakinta tace kar in sake zuwan mata gida, in dana ne, zai dinga zuwa yana gaishe ni, gaban Abba, Abba bece komai ba, Kar ka ja min Wulakanci donAllah" Majeed ranshi ya baci kwatakwata Mummy bata kyautawa yace "da da Yanzun ba daya bane, ba wanda ya isa ya wulakantaki, ko Mummy ce, ba zan bari ba, ki yarda dani" sai da sukayi mahawara kafin Hajjo ta amince zata bi Majeed da sharadin idan taga zaa mata Wulakanci zata dawo ya amince. Jikin Najwa yayi sanyi ganin zata koma Gidan Jiya, Majeed ya lura da ita yace "Dont worry, i got you both" Murmushi suka ma juna, Hajjo ta dauki kaya kala biyu ta sa a Jakka, don a cewarta ba zata kwashi kaya da yawa ba, in zama beyi dadi ba dawowa zatayi. * Har shi ma gabanshi faduwa yake don be son yanda Mummy zata karbesu
Chapter 43 · 0% Book details