Sashe 61
Adade Anayi Sai Gaskiya Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gado tare da fashewa da kuka, wannan wani irin bala'i ne, ya Allah ka kawo mana k'arshen wannan Musiba, Allah ba mu ds wani wayau sai wanda ka bamu, Allah ka sa muci Jarabawarmu" sai da yayi kuka san ranshi, kafin ya zube kan Gado. **** "M y Forever, kinsan ya nayi kwanakin nan ba tare da na ganki ba? Eyi? A daddafe nayi su, i couldnt even focus on the work, kawai naji ba zan iya k'ara kwana daya ba tare da na ganki ba, na bar aikin nazo Kano" Wani Murmushin jin dadi Ziyada keyi, Allah ya san son da take ma BawanAllahn nan, duk wani magana da yayi yana ratsa kwanyarta da duk wani sasan jikinta, bakon yanayin da bata saba ji ba takeji, tana jin in bata auri Zaid ba, ba zata iya rayuwa ba. Kallon da take binshi da shi ta kasa cewa komai. Zaid a zuciyanshi ranshi s baci, sai ya kai zuciyarsa nesa yake iya furta mata kalaman da yake gaya mata, balle yau part din da Armstrong ya bashi ya mai nauyi, shifa be sonta, be taba jin sonta ba, yana amfani da ita ne don ya idasa ruguje Mairo, in komai ya kare be ma san me zaiyi da ita ba, yasar da ita zaiyi kamar abu wanda bayaso, ko kuma a mata fyade, Yes Zuciyarshi ta raya mai, Fyade kawai zai kashe Mairo da ranta, duk wani dan Gidan zai mutu da bakincikin Fyaden da aka ma Ziyada, shi yafi karfinta, be iya hada jiki da ita, duk dai ta k'are, Armstrong zai ba ita ya mata lagalaga, wannan shu'umin murmushin yayi yana cigaba da tunaninka ya kusa mancewa da ita. " Ka aureni" abunda kunnuwanshi suka jiye mai kenan, ranshi yayi tsananin baci, ya zaayi, wannan banzar yarinya ta ta6a tunanin zai aureta, shes dumber than he thinks, har ta kusa gane chanzawar yanayinshi, tace "ranka ya 6aci ne don nace ka aureni?" da sauri ya k'ak'alo murmushin da iyakarsa la66a yace "Farinciki ne ya lullubeni, Aurenki zai fiye min komai dadi, Nagode". Ziyada Dadi kamar ya shideta jin kalaman Zaid, tace "yaushe zaka turo?" sai da gaban Zaid ya fadi, amma ya dake yace "yaushe kike so na turo?" Dadi ya kusa sakata daka tsalle, tace "zan gaya ma Yayana, sai suyi maganar, sai ka turo ko?" kafada ya dan daga, yace "Your wish Milady". * ** "Zaku ban hanya na wuce ko sai na faffala muku mari?" Cewar Mairo a fusace, daya daga cikin Securityn yace "ke kinsan inda kike maganar nan kuwa? Ki kula fa kar bakinki ya ja miki. A fusace tace "Ya ja min? Ka san ya nake da Oganniyar taku? Aminiyarta ce tun kafin tayi tunanin zata auri His Excellency, tun wuri ku ban hanya in wuce" dayan yace "da da yanzu ba daya bane, masu appointments kadai ke shiga, ba zaki shiga ba sai an bamu izini, so in kina da Number dinta, ki kirata, mu kawai masu bin dokana" nan Hajia Mairo ta fara rattafo Masifa "Dokar Banza, dokar Wofi, aiko karshen aikinku yazo". Horn sukaji daga cikin Gidan, da sauri suka bude, Amjad ne cikin wata Bak'ar Mota Mai Tint, duk da bata san waye cikin Motar ba saboda bak'in Gilashin sai ta hau sa mai Hannu, har ya sa kai zai fita daga Gidan, ya ga ana Daga mai hannu, ya kallo Matar dake kusa da wata Corolla yagane Hajia Mairo ce Kawar Mom dinsa, jiki ba kwari ya fito, da doki tace " Yauwa Son In-law, wadannan yan iskan Masu Gadin ne suka hanani shiga, nafi 20mins tsaye, ka koresu, ka sallamesu". Amjad ya dan Murmusa yace"Aikin su kawai sukeyi, inda sun barki kin shiga suna iya rasa aikin nasu". Ba haka taso ba, sai dai ta chanza Zancen da tambayar Her Excellency, a tak'aice yace"tana ciki, ku barta ta shiga" juyawa yayi da niyyar komawa cikin Motarshi ta tsaidashi da "Fita Zakayi?" a takaice yace "Eh" ta dan kwantar da Murya tace "ko zaka dan hakura mu shiga ciki, maganan da nazo da ita ta shafeka" shigewa Motar yayi tare da kunna mata wuta, daidai ita ya tsaya yayi wining glass yace "Ki shiga Mom na nan, duk me ta yanke daidai ne" daga nan ya ja Motarshi ya wuce, Mairo bata da lokacin tunanin Changing Amjad ta galla ma Securities din harara tace "Sai ku barni na wuce ko?" ta fada Motar ta, suka bude mata gate din ta shige ciki. Sai da tayi kusan Minti 35 tana jiran Her Excellency kafin ta shigo Parlorn da aka sauke Mairo, Ba kamar zuwansu na farko ba, da sune har Bedroom dinta, yau wani parlo aka sauketa kuma Hwr Excellency ta shigo tana yaushi tana yamutse fuska, Mairo ta hau kwasar Gaisuwa, kamar ba zata amsata ba ta amsata, karo na farko da Mairo taji Shakku, ta fuskanci wulakanci kawai Maman Amjad ke mata, amma da yake itace mabuk'aciya, bata ji haushi ba tace "Your Excellency, dama Maganar Yaran nan ne, Amjad da Ziyada, naga sun fahimci Juna, kuma suna son Juna, me zai hana azo ayi auren nan tun wuri?" wani kallo ta mata da ya sa hanjin cikin Mairo kadawa, hanjin cikinta sun fara sabawa da tashin hankali, ba wuya sun kada, kamar ba zatayi magana ba tace "ta ina suka fahimci Juna? Tunda yaje so daya ya kuma zuwa?" Mairo na in ima tace "suna waya" tace "Haka Makaryaciyar diyar taki tace miki?" Mairo baki ya hau rawa, tace "tsaya kiji Hajia Mairo, Amjad ba zai auri Karuwar diyarki ba, duk abubuwan da takeyi a Baze University a tafin hannun mu suke, ni da kaina na sa aka min bincike balle ace sharri aka mata, balle ba abun mamaki bane don diyarki ce, meye baki ba Mairo? Menene bakiyi ba lokacin yarintar ki, ban manta ba fa, i was even stupid to think zan hada zuria dake, so please tun da sauran Mutuncinki a idanu na, ki bar maganar nan kawai". Add Wani irin tashin hankali Mairo taji, Ziyadarta aka ma sharri? Like duk cikin yaranta mata, itace daban, tafi su natsuwa, Zaineema rashin hakuri, Zinatu rashin kunya, amma Ziyada magana ma bata dameta ba, ba kuma ta da saurin sabo, amma itace ake ma sharri? Wani Zuciya na tunzurata ta watse ma Her Excellency karama, wani zuciyar kuma na tausarta, "kari kiyi saurin daukan hukunci, Her Excellency kadai ne best choice dinta na samun kudi, so ba zata wargaza lamarin ba, hakuri ta ba Zuciyarta kafin ta fara magana cike da ladabi da biyyaya. " Your Excellency, kinsan shaanin yara ba a shiga tsakanin su, i'm sure dan karamin problem ne, kuma na san zasuyi sorting out da kansu" Her Excellency ta murtuke fuska tace "Wai ke dak'ik'iya ce? Ko fahimta na ne baki ba? Amjad ba zai auri ragowar Garada ba, akai kasuwa, ko mata sun k'are, Amjad ba zai auri diyarki ba" Hankalin Mairo ya sake tashi, ta dai sake nutsuwa tace "Ok naji, abar maganar Aure, but donAllah your Excellency, ki dan ban wani abu, like Million 2, ina so na daukaka k'ara ne zuwa babban kotun duniya" Her Excellency tayi daria tace "Iska na wahalar da mai kayan kara, wato baki daddara bane kenan? Kina nan kin zama abun daria a gari, ai sjariar ku Live aka nuno shi, shiyasa ma na sake tsorata dake, bayan abubuwan Alheri da Alhaji Nakowa ya muku, ki rasa abinda zaki saka mishi sai Sharri? Kika lak'a ma diyar shi Sharri? Ko an gaya miki kowa kamar diyarki ce? Haka kuke saka Alheri da Sharri? Wato haka misali in anyi aure da Amjad din haka zaku laka mai sharri? To ba zai yiwu ba, mu ba tsaran yinki bane, kikace zakiyi mana abunda kika ma Nakowa, sai kin karashe miserable life dinki kina nadama, sai na karar da Family line dinku, so tun muna shaida juna get lost". Ran Mairo ya baci amma ganin fushi ba nata bane yasa ta zube kan guiwowinta biyu, tana rok'on ta da ta bata ko da bashi ne, amma haka Her Excellency ta shafewa idonta toka ta karta mata rashin mutunci karshe tace " ko ta tashi ta fitar mata daga Gida, ko ta sa Security suyi mata wulakanci, su tozarta ta" ganin ba kirki ne dasu ba, kuma in ta tsaya mata rashin mutunci, to abun zai sake kwaye mata, saboda wa ya isa ya ma matar SSG wulakanci? Jakkarta ta fizga da karfi kana ta juyo ta wurga ma Her Excellency kallon zamu sake haduwa, kafin ta fita fuuuuu. Kwantar mai da hankali take tayi tunda ta kirashi a waya, be san meyasa ba, a duk lokacin da yake magana da Hajia Aynarh, yana samun kanshi cikin nishadi, a yanzu da yake cikin tashin hankali, sai ya tsinci kanshi cikin saukin zuciya, yanda take jawo mai hadisan daukan k'addara ya k'ara burgeshi, abunda yafi burgeshi shine, da yaji tace zata taimaka mishi da ko da Miliyan biyu ne, ta burgeshi matuk'a, amma sai yace da ita "Hajia Aynarh, nagode kwarai da irin guddumuwan da kike bani da Iyalina a duk lokacin da bukatar hakan ya taso, amma gaskia ba zan amince da wannan ba, mungode Allah ya saka da Alheri, Allah ya baki ladan niyya". Shagwabewa tayi kamar tana gabanshi, tace "Haba Alhaji Abba, kar ka min haka, wallahi nayi niyya, nasan ba zan iya biya muku bashin nan ba, amma a dan rage, DonAllah kar ka juya hannun kyauta baya". Murmushi ne ciro yayi yace " dagaske ba zamu amsa ba, mun sa Gidan nan a Kasuwa, za a siyeshi fiye da Miliyan 20, InshaAllah zai kai 30 din, karki damu mungode". Ba yanda batayi ba, amma Fir Alhaji Abba ya k'i, chan tace "to shikenan, zan dai zo in tafi da Muhsin da Zinatu Gidana, sai su cigaba da zuwa Makaranta daga Gidana, don kar tashinku yayi affecting dinsu, ka tuna barinku Abuja, da k'yar aka samu Zinatu ta sake". Alhaji Abba ya jinjina kai yace " to kinga wannan ba zan hana ba, dama basu san da zancen ba, Yaronki kadai ya sani, ya hana a gaya musu" Hajiya Aynarh tace "Allah Sarki AbdulMajeed, sosai yake bani tausayi, Allah ya kara mai hakuri