Sashe 99
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Masha-Allah haka na ke so, sai anjima da dare za ku dawo gida kinji? Amman yanzu ba ri a akaiwa Nana waya ku gaisa”
Na amsa da to, haka na rike wayar har aka kaiwa Nana ina jin muryarta sai na ji wani farinciki ya cika ni cikin far'a muka gaisa da ita sannan na mikawa Amina wayar.
Kamar yadda Momy ta fada ban mu koma gida ba sai da dare na yi zaton direba zata aiko ya dauke mu ashe Hajiyar ce da kanta zata kai mu, bayan ko wace awa biyu sai Aliyu ya kira wayar Amina ya ce ta ba ni tun tana dauka tai magana har ta kai idan ya kira sai dai kawai ta dauka ta miko min, tambaya yake wai ko ina bukatar wani abun sai na ce aa sai ya tambaya na ci abinci na ce masa ce daga haka kuma sai yai shiru yana sauraren numfashi har an wani lokaci sannan ya kashe. Ko da muka shiga gidan babu kowa sai wata budurwa da kuma su Siyama da Husna da gudu suka zo suka tarbe ni Momy kuma na zaune saman kujera tana kallona fuskarta da murmushi. Zaunar da ni sukai suna ta rumguna suna ja min kumatu Husna na ce min Amarya.
“To a kyale ta haka nan taje ta ga Mamanta haba”
Momy ta fada. Siyama ta rika hannuna.
“Muje na rakanki”
Sai muka fito tare da ita tana rike da hannuna ni dai har Siyamar kunyarta na ke ji balle kuma Momy, Nana ma da zanje gurinta sai ma soma jin kunya kamar ba zan iya zuwa ba.
MOMY POV.
ataa na ficewa daga falon ita da Siyama Momy ta mike tsaye tare da Hajiya Ramatu suka nufi dakinta, Hajiya Ramatu na mata ya gajiyar biki.
“Alhamdulillah”
Momy ta fada tana zaunawa saman gado Hajiya Ramatu kuma ta zauna a kujera. Sai da suka fara firar daurin aure da taron da akai wanda Momy bata sa ran za'ayi ba sannan Hajiya Ramatu ta ce.
“Ai kowa yayi mamakin jin auren daga sama, amman dai sati na sama za a kai masa matarsa ko?”
“Aa ba yanzu ba ai, yarinyar ma da yanzu ake son ta fara makaranta? An dai yi auren ne kawai saboda hankalin kowa ya kwanta kuma a san mijinta kin ga ba wani zancen wane na so wane na so”
“A a Wallahi karku tauye masa hakki, yaushe rabon ma da a daurawa mutum aure kuma Amarya bata tare a ranar ba? Ai bar wannan yayi ko a kauye, balle wani diban shekaru a gida? Wane namijin zai daukar miki haka?”
“Ai ya san da maganar karatun na ta tun ba yau ba”
“to karatuna yana hana aure ne? Ai aure baya hana karatu kuma karatu be hana aure, tai karatu tana karkashin kularwarsa ai zai fi dadi saman da tana gidanku abun ai be ma burge ba, karki biyewa kowa ki bar mata ta tare dakin miji kar ma a ja abu da sauri”
“Haba Hajiya komai fa ba a shirya ba”
“Shiri yanzu wani wahala ne da shi? Lefe ne ko tana dakinsa zai iya mata, kayan daki kuma rana daya za a iya siyowa indai a kasar nan ne, sai dai dan gyara gida da fenti ko kuma ya koma sabon gidan Alhaji da ya gina a wurno road ba dole sai an tsaya gina wani ba”
“Ai ni bana son ya raba musu gida da Rahma, kara dai ya hade su ya zauna da su guri daya”
“Har kin tuna min da ita, wai ta ji an yi auren nan ne?”
“Wallahi ban sani ba amman ba zata rasa ji ba tun da yan'uwanta ko matan abokan Aliyu su fada mata kin san tana dubai fa har yanzu”
“Haba dan Allah ko dan wannan be isa ya saka ki bar ya tare da matarsa? Ai ko dan wannan haushin ya isa ya saka ki barta ta tare, zaman gida na me kuma? Yanzu zamanta a nan tashin hankalinsa ne fiye da ba a daura auren ba ma”
“Hajiya yarinyar nan bata iya komai ba bata san komai ba ko girki bana jin ta iya, ga kuma karatun da take son yi”
“Karatu ai ana yi a gidan miji ni ba da aurena nai HND ba? Yar wajena Sumayyah ma da aurenta har da yara hudu tai karatu, abinci kuma gobe idan za ki shirya abun karyawa sa a kira miki ita ki shirya komai a gabata ko kuma ki bata kina fada mata tana yi kamin satin nan da zata tare ta iya wani abun sauran ta koya a can, amman Wallahi karki yarda ta dade a gidan nan ina tabbatar miki ko sati biyu tai a gidan nan sai Aliyu ya fara nuna miki damuwarsa, kan Rahma ta dawo ma ai sai a barshi da matarsa ya tare tana zuwa ta tararda wata ba saboda haka akai auren ba?”
Momy ta yi shiru tana nazarin maganganunta, ta san gaskiya Hajiya Ramatu ta fada ita kanta ta yi wannan tunanin amman bata son Ataa da Nana su ga kamar ta matsa musu ne.
“To yanzu dai sai na ji ta bakin Mahaifiyar yarinyar idan ta yarda”
“Ai yarda ma za tai wake son a daurawa dansa aure kuma ya zauna masa a guri? Wannan ai sai rashin kunya ta shiga ciki ma, kin ga yadda yake kiranta a waya dazun? Abun har Mamaki ya ba ni, karki takura masa Wallahi ki bar matarsa ta tare komai sai ta koya a can idan ma school din koyon abincin zai saka ta duk daya”
Momy ta yi murmushin jindadi.
“Zan duba Hajiya Ramatu, ko dan saboda Rahma ai ta tafi ta bar shi sai ta dawo ta tararda wata”
“Shine Ai Allah dai ya basu zama lafiya ya hada kansu”
“Amin”
Cewar Momy tana mikewa tsaye ganin Hajiya Ramatu ma ta tashi.
Sorry 🙏😑
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Wani irin bakinciki ne ya cika mata zuciya, sai hararar wayar take kamar Aliyu a gabanta.
“Wai ni Aliyu zai yi ma kishiya? Kiji fa”
Muneera ta tabe baki.
“Ai daman nasan za a rina, daman can ba ya fara gajiya da ke, gashi nan tun yanzu kin fara gani ai, kuma ya rasa da wacce zai hada ki kishi sai wannan yarinyar, ai Wallahi ki ma gode Allah daya saka ba ki ma garin ke ma ki kasar gaba daya zancen hakan ya fi ma”
“Ai Wallahi daga nan ma gaba zan kara sai ya raina kansa da wannan kazamar sannan idan ya ga dama ya dawo ya bada hakuri na ko?”
“Au komawa ma za ki yi?”
“Muneera to ya na iya ina son mijina, kuma dan wata banza ta aureshi ai be kamata na kyaleta da shi ba”
“Yanzu ha hada ki kishi da wata banza marar asali kuma yar aikin gidanki, ya hada ki kishi da talaka karamar yarinya kamar wannan be fada miki zai yi auren ba, sai da aka daura aure shi ma kuma ta hanyar kawayenki kika ji haba Rahma ki daina abu kamar so ya haukatar da ke mana, dan za ki kara aure sai ya wulakanta uwargidansa, daman ma zaman nan haka suke kin dai san iyakar wulakanci Bawan Allah nan na miki shi”
Idon hawaye ya cika da kwalla, sai a yanzu take jin ba dadi domin dazun haushi kawai take ji amman a yanzu ta soma ganin rashin kyautarwa da Aliyu yai mata.
“Ke daina damuwa ki manta da komai ki yi kiba ki mulmule yau ko rabuwa Aliyu yai da ke shi yai hasara, Daddynmu na can yana nema miki kodar da Aliyu ya kasa nema miki saboda ya gaji da ke, ashe aure zai yi, yanzu ko rabuwa yai da ke idan kika samu lafiya sai ki auri mai haihuwa shi kuma yaje can ya karata da amaryar”
“Ko a mafarki ban taba zaton Aliyu zai min haka ba, ban tana taba tsammanin haka ba ko a mafarki”
“Ai namiji ba shi da tabbas namiji dan kunama, hmmm ai karki tana yarda zai so ki ke kadai ke kadai ranki”
“Na shiga uku Muneera, zuciyarta kamar zata narke na ke ji, i can't believe tun ina raye Aliyu zai hada ni da wata, Wallahi ko bayan raina ya auri wata be kyauta min irin soyayyar da mukai balle kuma yanzu da na ke raye, bayan kuma ya san lalurata, baya tsoron abunda zai same ni? A yanzu kenan baya gudun bacin raina? Ashe Aliyu zai iya min haka?”
Wasu zafafan hawaye ne ke sauko mata kamar ba gobe.
“Ni kishiya? Ni...?”
“Ai namiji kenan, kadan daga halinsa kika gani”
“Komai raba mu za mu yi kenan? Yanzu Aliyu ba nawa ba ne ni kadai kenan? Wayyo Allah ”
Ta fada da hargagin kuka tana saukowa daga saman gadon ta fado kasa tana wani irin kuka. Muneera ta taso da sauri ta dawo kusa da ita
“Yanzu akan wannan abun za ki saka kanki kuka?”
“Ina son mijina Muneera ba zan iya ganinsa da wata ba, taya zan rayu da Aliyu shi kuma ya rayu da wata? Taya Aliyu zai min haka? Muneera haukacewa ce zan yi wayyo zuciyata na kasa yarda cewar Aliyu ya auri yarinyar nan”
“Haba Rahma a hotel muke fa, hotel din ma ta dubai idan kina irin wannan ihun kina kuka ai sai su dauka wani abun su shigo”
“Gida na ke so Muneera, gida zan koma Nigeria na ke so ki fadawa Yaya ya kai ni ya shirya mu koma gida, Muneera zan iya mutuwa”
Ta fada tana kara narkewa tana wani irin kuka mai ban tausayi. Ita kadai ta san abunda take ji a yanzu ita kadai tasan yadda taje son Aliyu kuma yanzu ace ya hada son ta da na wata?
“Mi na masa? Mi na masa Muneera? Mi yake damunsa? Anya kina ganin na cancanci irin wannan sakarya?”