Sashe 52
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Aliyu ya kalleta kamar ya tambayi abunda akai mata har Momy take fadar hakan sai kuma wata zuciyar ta hana shi. Rukaiya ce tai kwafa
“Wallahi kwata kwata Kamal ba shi da mutunci kuma ba shi da tarbiya”
A take zuciyar Aliyu ta kwadaitu da son jin abunda ya faru amman ya kasa tambaya har sai da Zee da ke son ta ji labarin ta tambayi Rukaiya.
“Mi Kamal yai hala?”
Rukaiya da Maryam ne suka labarta abunda ya faru a nan Aliyu ya ji komai, wayarsa ya ciro kamar be damu ba ya nufi kofa rike da hannun Inteesar ya fice. Sai da ya fito daga ward din sannan ya turo Inteesar ta kira masa Zee, ita da Inteesar har a rigengen zuwa suke domin sun san Aliyu baya son jira, kuma abu kadan ya saka ransa ya bace.
“Zainab So na ke ki kira min Kamal ki tambaye shi wace asibiti ya kai Ataa”
“Ya Aliyu bana da number Kamal”
Ya mika mata wayarsa ba tare da ya ce mata komai ba, tana karba sai taga number Kamal a sama sakawa tai a wayarta ta kira bugu biyu ya daga.
“Hello Kamal ina wuni”
“Lafiya kalau wake magana”
“Zainab ce, wai Ammy tace a tambaya wace asibitin ka kai Ataa”
“Ammy? Ko Mama Fulani dai”
“Ammy dai”
“Perry Hospital female ward room 104”
“Thank you”
Tana fadar hakan ta sauke wayar ta yi karya da Ammy ne domin ta lura da Aliyu baya son asan shi ya saka ta kira, da acce yana so da shi da kansa zai kirashi tun da abokinsa ba sai ya saka ta ba.
“Ya ce Perry Hospital female ward room 104”
Ta fada tana mika masa wayarsa, karba yai ya saki hannun Inteesar ya fice daga gurin. Ita da Inteesar suka dawo dakin da Rahma take.
“Ku wuce kawai gida, ni zan tsaya a nan sai an jima Dan wajen Fulani zai maida ni gida”
Sai da suka mata Allah ya sauwake sannan suka fita. Bayan sun fice ne Momy ta kalli Rahma da ke cikin damuwa ta ce.
“Ciwo fa ba mutuwa ba ne, dan ba ki da lafiya ba shi yake nufi zaki mutu ba, ko babu kodar a jikinki idan Allah ya so sai ki ga ya raya ki”
“Ba neman lafiyar ne abunda ya dame ni yanzu ba Momy, haihuwa ce abunda ta dame ni a yanzu, ina son na haihu kamin na mutu”
“Duka dai na Allah ne, kuma idan yace yanzu abu ya kasance za ki ga ya kasance”
“Wata kila da matsalar daga ni ne da zan iya samun sauki ko kuma wata mafitar, amman matsalar daga Aliyu ne na san ba zan taba samun waraka ba”
Momy ta kalleta irin kallon nan na ban fahimci zancen ki ba.
“Matsalar daga Aliyu ne? Kamar ya?”
Rahma ta yi shiru bata ce komai ba, domin ta fahimci be fadawa Momy ba. A take hankalin Momy ya tashi fiye da da, domin a da tana daukar daga shi har Rahma ba su da matsala kamar yadda yake fada mata likitoci sunce yanzu kuma Rahma ta ce matsalar daga shi ne, amman miyasa be taba fada mata ba? Daman Rahma ta san da wannan ta rufa masa asiri take zaune da shi a haka ko kuwa daga baya ne abun ya bullo? Anya Mama Fulani ta sani ma kuwa? Har Momy ta bude baki zata sake tambayar Rahma sai ga wani Doc ya shigo tare da nurses kusan biyar suka hau duba Rahma suka bata magani sannan suka bawa Momy takardar sallamarta domin su a gurinsu ta ji sauki tun da ta farfado kuka bata jin ciwon komai sannan kuma an riga an san matsalar koda ne, sun kuma dorata akan magani. Daman haka suke yi sai dai idan mutum yana son ya cigaba da karbar magani a asibitin sai ya bukaci su barshi yai ta biyan kudi yana karbar magani har ya kare. Momy ta yi kokarin nuna farincikinta duk da irin tashin hankalin daya same ta na jin gaskiyar maganar cewa matsalar haihuwar daga Aliyu ne, har ga Allah ta jidadin samun lafiyarta domin ko bata san inda Rahma ta fito ba za tai farincikin samun lafiyarta a matsayinta na musulma balle kuma matar danta ce dan ta take aure. After like thirty minutes da fitar likitan Mommyn Rahma ta shigo da kanenta ai ko suka hau murna kamar su cinye Rahma sun jidadin ganin an sallame a take hakan na nuna jikin nata da sauki keman kuwa da kasancewar kodar na ta a kone yake.
“Mahaifinki ya ce ya saka cigiya a gurin likitocin daya sani a nemo duk inda koda take kuma ko nawa take za a siya miki, kin kwantar da hankali lafiya zata samu In-Sha-Allah”
Mommyn Rahma ta fada tana dariya sai dai ita Rahma bata wani farinciki sosai, domin tana cikin damuwa a yanzu. Momy ce ta kira Aliyu ta fada masa an sallami Rahma kuma ya zo ya maida ita gida, da murna ya amsa mata sannan tai hanging call din ita da farinciki tana kallon Rahma, sannan gaisuwa ta biyo bayan tsakaninta da Mommyn Rahma har suka dora da labari.ATAA POV.
Ban san adadin wannin dana dauka a sume ba, shin sumar ma nai ko kuwa dai wata duniyar na tafi na dawo domin Nana nai ta gani da kuma wata rayuwa da muka kai da ita a can baya, da kuma ganin da cikin wani daki mai kamar na kasa ba kuma kasar ba, shin haka suman yake ko kuwa fitar hankali ne kawai daga jikin duk ba zan iya tantancewa ba. Da wani irin karfi marar misaltuwa na ji na dawo duniyar motane da dabbobi har ma da sauran hallitu, duniyar da ke cike da kazanta da gurbatacciyar rayuwa da ba kowa ke tsira cikinta, wasu abu nake gani su ba mutane ba kuma su ba aljannuna ba, ganina nai kasa bana iya tantance ko mienene sai dai ina ganin kan abun yana yawa kuma suna sanye da fararen kaya. Daga bakina har hanci da ido numfashi suke fiddawa da karfi wani kuma na shiga da karfi, wani abu ne a kirjina kamar dutsin guga da zarar numfashin nawa yai kasa sai su goga shi da dan'uwansa su manna min shi a jiki sai na ji makamancin abunda na ji dazun, haka sukai ta min har numfashin nawa ya daidaita, sai sannan na soma ganin likitoci su uku ashe mutane ne ba aljannuna ba kayan likitocin na su ne nake gani farinsu kamin idon nawa ya waye.
“La'ilaha illallahu Muhammadu Rasulullah Sallalahu Alaihi Wassalam”
Shine abunda ya fito daga bakina sai na lumshe ido ina fitar da numfashi a hankali. Dayan daga cikin su ne naji yai hamdala ga Ubangiji da alama shi din musulmi ne. Sai na ji dayan ya kira sunana da hausar da da bata fito sosai.
“Aasha”
“Na'am”
Na amsa ina kallonsa sai dai muryar tasa har yanzu kasa kasa nake jinta. Dauke ni sukai daga saman wannan gadon suka dora ni akan wani suka turani zuwa wani dakin na musamman a akan gadon dakin suka dorani sannan sannan suka saka min drip dayan kuma ya saka min bandeji a bayan kaina, sannan suka juya suka fita. Lumshe ido nai ina kokarin tuna abunda ya faru sai na ji an turo kofar an shigo hakan yasa na bude idona sai na ga Kamal cikin shiga ta manyan kaya ya doso inda nake cikin yanayin damuwa.
“Ataa”
Na kalleshi ina kokarin amsawa sai ya kai hannunsa ya taba jiki.
“Kina jin wani abu yanzu?”
“Bana jin komai”
Murmushi yai ya gyara min kaina da gashina.
“Sannu”
Na gyada masa kai.
“Likito ci sun ce abarki ki yi bachi, zan je gida na dawo ke kuma ki samu bachi kinji”
Nan ma kan na gyada sannan na ce
“Na gode”
“Ba komai Allah baki lafiya”
“Amin”
Na amsa cike da nauyin baki sannan ya juya ya fita, ni kuma na lumshe idona bachi wahala yai gaba da ni. Wata kila na kai wa biyu ina bachi kamin na farka, idona na fara budewa ina ta kallon farin silin dakin warin asibiti na soma ji kamin na kamshin turaren Aliyu ya biyo baya, dagowa nai kadan sai na ganshi zaune saman kujera yana ta kallona da cat eyes dinsa ko kyaftawa ba yayi. Nima idon ma sakar masa ina ta kallon fuskarta, sai a yau ake kara tantance kyauwunsa hanci ya sauko sosai ga manyan ido masu daukar hankali.
“Ba na ce ki daina kallona ba?”
Yayi maganar kamar shi ba kallona yake ba, yana takura idan ana kallonsa sai dai shi ya iya kallon wasu har sai ka soma tsarguwa. Rumtse ido nai ina turo baki, sai na ji an buge min bakin da sauri na bude idon na kalleshi yanayim yadda yake sai yai min kamar ba shi ya bugar min bakin ba sai dai hakan be hana na zaburo masa.
“Mi na maka zaka dake ni?”
Kallona kawai yai be ce komai ba ya mike tsaye yana saka hannunsa na dama aljihu sai kuma ya kai dayan hannun sai taba kaina.
“Me zaka mata? Bayan marin da Mama Fulani tai mata wani zaka mata kuma?”
Kamal ne ya shigo hannunsa rike da leda yana fadin yana tare da doso inda nake kwance, Maganarsa bata hana Aliyu tana kan nawa ba, kamar ma be san da shigowar Kamal a dakin ba haka yai domin ko inda yake be kalla ba ni kawai yake kallo yana taba jikina da alama so yake yaji idan jikin nawa da zafi ko sanyi.
“Ashe dai ba Kamal kadai yake iya kula yar aiki ba, idai ko haka ne ya kama ka sauke girman kan nan naka Aliyu”
Dagowa Aliyu yai ya kalli Kamal.
“Ba a fada min abunda zan yi sai dai ni na fadawa wasu abunda za su yi, a kasa da ni kake Kamal kasan ma kasan takarmin kafata, ya zama dole ka min biyayya kuma ka kalleni da daraja ba zan sake musayar yawu da irinka ba”