← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 67 OF 143

Sashe 67

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Gaskiya kin yi kuskuren barin mahaifiyarki tana cikin wannan ciwon na tsawo lokaci haka, da an dauki mataki da yanzu duk hakan ba zai faru ba”

Har yanzu hawaye kawai nake har bana iya ganin fuskar Nana da nake kallo. Ko da na yarda cewar Aliyu ba da saninsa aka min haka ba, ba zan taba iya ganin kimarsa ba har abada, domin saboda matarsa akai wa Nana haka. Ji nai an dago fuskata sai hawayen suka kwanto min na ga fuskarkar Muhseen da ke kallo na ido cikin ido.

“Mahaifiyarki zata tashi ta ji sauki na tabbatar miki wannan, amman ba zata iya gane wacece ke ba ba kuma zata iya tuna komai ba, sai dai karki nuna mata cewar akwai wata rayuwa ta baya da tai a yanzu, sai nan da wani lokaci idan ta fara shan magani”

Sai a lokacin na iya bude bakina na amsa masa da to ina kawar da fuskata daga rikon da yai min.

“Kar abunda Aliyu yai ya dame ki, ke dai ki maida hankalinki gurin neman lafiyar mahaifiyarki kawai kina mata addu'a”

“To”

Na fada murya can ciki, sai na zauna a kujerar da ke nan na rumtse idona ina hawaye. Ina jin lokacin da ya fice daga dakin ya bar nan a nan na samu damar yin kukana na tausayawa kaina kuma na tausayawa Nana na halin rayuwar da muke cikin, ban taba tunanin za mu jidadi ba amman a kullum ina fatar zata samu sauki mu cigaba da rayuwar mu kamar yadda muka saba. Misalin biyar da rabi Momy ta zo ita da wata bakuwar fuska ta riko mana lemu da ayaba da kankana. Na gaishe ta da muryata mai sautin kuka sai ta amsa min tana kallon yanayi na.

“Ataa ki kwantar da hankalinki Mahaifiyarki zata samu lafiya ta tashi In-Sha-Allah”

“Muhseen ya ce idan ta farka zata manta da komai, ba zata iya tuna komai ba kuma ba lallai ne tunaninta ya iya dawowa ba”

“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u, kuma dai? Kai Subhanallahi wannan abun babu dadi ji”

Ta fada cike da tausayawa sannan dakin yai tsif kamar babu kowa a ciki. Ni ina hawaye ita kuma tana ta kallona ta kasa yin komai.Shiru nai ina nazari maganarsa, wata kila da gaske be sani wata kila kuma shi ma wannan likita hadin baki yai da shi kamar wacan dan ya wake kansa.

“Idan na akan kuskure yai ko kuma da ganganci na bar shi da Allah shi da duk wanda ya cuce ni Allah zai saka min”

“Allah zai kwatar miki hakki ki a nan duniya ko kuma gobe kiyama, na jidadin da kika san da hakan kuma kika yarda, Aliyu kuma be biya ni ko ya roki na fahimtar da ke haka ba, hasalima bansan cewa da zalinci aka cire miki kodar ba sai yanzu, sai dai na san da zalintar yai da ba ki isa ki tsaya a gabansa ki fada masa magana mai daci haka ba, idan har shi azzalumi ne a take zai batar da ke ua shafe labarinki a doron kasa, dan haka ki kwantar da hankali ki daina damun kanki da wata damuwar a shekarunki”

Hannu nasa na share hawayena na kawar da fuskata.

“Na sani uwa tana da muhimmanci dole ne za ki ga abunda akai miki da fadi, amman ki rika tsayawa kina tunani a ko wane lokaci kamin ki aikata abu”

Mikewa yai tsaye ya fice ba tare da ya sake ce min komai ba. Ni kuma na kwanta a saman gadon ina jin zuciyata tana min wani mugun zafi, idan har Nana ta manta da komai ciki har da ni ban san yadda zan yi rayuwa ba, addu'a kawai nake ina rokon Allah kada ya kaddara hakan ta faru.

Sai kusan la'asar aka fito da Nana daga dakin tiyata, ko da aka dawo da ita dakin tana bachi suka saka mata jini tare da lullube ta da zanen da Momy ta aiko mana. Ni kuma na tsaya a kanta ina ta kallonta hawaye na ta min zuba kamar ba gobe, tsoro nake kar abunda Muhseen ya fada ya zama gaskiya.

“Ke wai ba ki gajiya da kuka ne?”

Muhseen ya fada bayan ya shigo dakin yana nufo inda nake tsaye ina kallon Nana.

“Anyi tiyata cikin nasara sai dai fatar samun sauki, dan haka ki daina kuka”

Dagowa nai na kalleshi.

“Yanzu da ta farka mantawa za tai da ni ko?”Daga tsayen da take ta zo kusa da ni ta tsaya ta kai hannu ta dafa kafadata.

“Wata jarrabawar da sauri take zuwa wata da dadewa wata kuma sai daga karshe, wadanda take zuwama daga karshe sun fi shan wahalar rayuwa, amman daga ta zowa a lokacin kurciyarsu sun fi kowa jindadin rayuwa a gaba, ina jin tausayinki sosai ba ba dan saboda jinina ne silar hakan ba, sai dan halin da kika tsinci kanki tun kamin rayuwar ta kawo ki nan, labarinki abun a tausaya miki ne a tallafa miki, tun daga lokacin da ya fada min abunda ya faru ban taba ganinki ba amman sai na samu kaina da tausayinki, daga lokacin da na saka ki a idona kuma sai na fara miki kallon yata, ba fata na ke ba amman ko mahaifiyarki bata raye ni nan mai rikonki ce kuma na kula da ke, ki kwantar da hankalinki Ataa In-Sha-Allah za ki samu duk wani jindadi da wata rayuwar da kika rasa a baya”

Fashewa nai da kuka kalaman da take min sai nake jin kamar Nana mutuwa zatai ta barni, idan ko ta mutu na shiga uku bana da kowa sai Allah. Sai shida har da yan mintuna sannan Momy ta tashi zata wuce gidan.

“Wannan matar sunanta Laraba zata rika kula da Mahaifiyarki ke kuma kina dan samu kina hutawa, kamar yanzu za mu iya barinta sai ki bini muje gida idan kina so, kin ga sai ki samu ki yi wanka ki huta kamin ta farka”

“Aa ni dai ki barni a nan, na fi son ko zata farka ta farka a gabana, ji nake kamar idan nai nisa za ta mutu ta barni”

“Ba zan takura ki ba, amman ita ma zata zauna a nan tana da waya a hannunta kinji kina bukatar wani abu ki yi mata magana zata kira ta fada min”

“Tau”

Na fada ina kallonta da idona da suka gama kumbura. Kudi ta ciro mai dan dama ta mikawa matar wacce ta kira da laraba.

“Ki rike wannan idan tana bukatar wani abun sai a siya, kuma kin san halin yarinya sai dan lallaba duk da nasan ba halinki bane fada amman dai a kara, bama son abunda ya taba yarinyar nan yanzu”

“To Hajiya In-Sha-Allah za a kiyaye”

Daga haka tai min Allah ya kawo sauki ta fice ta bar ni da matar mai sa'ar Nana.Bayan na gama sallah magariba na dawo saman kujerar na zauna ina ta kallon Nana zuciyata na min wani irin zafi, babu abunda ya dame ni a yanzu kamar sanin dangina, lallau rashin yan'uwa a kusa da mu ya saka mu cikin rayuwa mai wahala da tsanani. A yanzu kuma da nake da bukatar sani sai a ace min zata manta da komai? Kife kaina nai a gurin nai ta kukana har aka kira sallah isha'i, sannan na shiga bandakin nai alwala na fito na shimfida carpet na gabatar da sallah isha'i ita kuma tana zaune a saman tabarma tana waya. Bayan na gama sallah na kwanta a gurin ina da hawayen da a yanzu suka zame min kamar farilla. Har ta gama wayar ta tashi tai nata Sallah ta bude abincin dazun ta zuba min a plate ta aje a gabana.

“Ki ci abinci”

Sai da tai maganar na tuna cewar ban ci wani abinci na bayan na safe.

“Bana jin yunwa”

Na fada ina kawar da kai daga barin kallon abincin da warinsa ma baya min dadi. Jan plate din tai a gabanta ta soma ci, ni dai ina a gurin har dare ya soma yi. Jin nai zaman dakin ya ishe ni ina marmarin wani gurin dabam ba nan ba, fita nai daga dakin ba tare da na fada mata ga inda za ni ba ita ma bata tambaye ni ina zanje ba. Fitowa nai harabar asibitin ina ta kallon yadda fitilun asibiti da sukai haske har suna kashe min ido domin idon nawa sun yi laushi sun kuma rage haske saboda kuka da nake. Mikewa nai ya fito daga cikin asibitin ba dan nasan inda zanje ba. Wani bangare nake tunawa na rayuwarmu daga zaman da muka saba yi a bukka da kuma baran da muke har zuwa rasuwar Lukman.
A da mu biyu ne yanzu kuma na zama ni kadai, ina tuna lokacin da Baba yake da fada cewar wata rana zan maza a yarta wata kila yana da rai ko kuma bayan ransa, har ya kama hannun Lukman yana wasa ya ce.

“Ban so rayuwar mu a haka ba, ban so komai ya zama yadda yake yanzu ba, amman wata rana komai zai zama tahiri, Lukman sai zama babban mutum Ataa kuma ki zamu gata mai kyau, sai dai ban sani ba ko kusa ne ko kuma nesa, idan ina da rai zan jidadi idan kuma bana da rai sai ku min addu'a kun ji”

A lokacin da yai wanann maganar yana rike da hannuna da na Lukman.
Yawun bakina na hade ina magana da kaina.

“Baba ka rasu, Lukman ma ya tafi, tsakanin ni da Nana ban san wanda zai riga wani ba, amman ina fatar na rigata, sai dai wannan jindadi da ka ce mana ba zai zo ba har a bada”Hawaye ne ya sauko min a haka na kamo hanyar Clapperto ina hawayen har na iso, cikin dakin kwanon na shiga na kwanta daga bakin kofa ina kallon taurarin dake sama hawaye na ta min zuba na kasa tsayar da su.

ALIYU POV.
Chapter 67 · 0% Book details