← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 121 OF 143

Sashe 121

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fada yana jam kumatuna ba tare da ya mim murmushi ba, a dole na koma ciki nai wanka na shirya kamar yadda ya bukata, a tare muka fito da shi yana kallon yadda yake kallon tafiyata wata kila so yake yai sauri ko na taka ba daidai ba yace da gangan na ke yi saboda ina da ciki. Shi ya bude min motar na shiga sannan shi ma ya shiga ya zauna, sai ya kai hannunsa a bakinsa yana karanta abunda ban san ko minene ba sannan ya saka dayan hannunsa ya daga Hijab dina ya bude rigar zanen da ke jikina ya shafa min addu'ar a ciki. Sannan yai ma motar key daman tuni mai gadin ya bude mana gate, a hankali ya fara tukin har muka fito daga cikin gidan.
Na yi zaton gidan za mu fara zuwa sannan mu wuce asibitin sai ya fara zuwa asibitin sai dai ba wacan ba ce domin wannan katuwa ce sosai ga ma'aikata ta ko'ina gwanin ban sha'awa. File aka fara bude min sannan ya sake tambaya ko ina jin sani abun bayan abunda na fada mishi jiya.

“Bana jin komai”

A nan ya sake rubuta wani abun a farar takadar ya mikawa Aliyu.

“Ka kara mata da wannan, wannan kuma results dinku ne na jiya congratulations”

Aliyu yayi murmushi yana kallona, kunya ce ta rufe ni nai kasa da kaina ina watsa da yan yatsuna cikin Hijab.

“Doc ka fada mata abunda ya kamata tai da wanda be kamata ba da abubuwan da zata ci”

Aliyu ne ya bukata da kansa, a take likita ya fara lissafa min irin abubuwan da zan rika ci da kuma aikin da zan yi wanda ba mai wahalarwa ba.

“Aa no doctor ni fa ko bokitin ruwa ba zata dauka ba, balle wani shara da wanke wanke”

“No ai aikin yana da kyau amman kar ayi na kashe kai”

“Ko na raya kai ba za ayi ba, balle na kashe kai, ina ciki fa aka ce Alhaji”

Aliyu ya fada yana nanatawa, shi kuwa likitan sai dariya yake, ni dai gaba daya kunya ta gama kamani har bana iya daga kaina.

“Ta so muje”

Tashi nai ina tafiyar cike da kunya shi kan tuni ya kai kofa har ya bude min kofa yana jira na fito, sai na fita sannan ya fito, ba ko kunya ya kama hannuna zuwa gurin motarsa da kansa ya bude min sai da na shiga na zauna sannan ya rufe ya zagoyo gefensa ya zauna, tukin mota yake amman gaba daya hankalinsa da tunaninsa na kaina, minti biyu uku sai ya kalli inda na ke.

“Kina son wani abu? Kina jin wani abu?”

Yayi min irin wannan tambayar ta kai sau takwas kamin mu isa family house na su, a harabar gidan ya faka motarsa har na kai hannu zan bude sai ya danna dan wani abu dake gefen motarsa motar ta rufe, kallonsa nai sai ya fara min magana a natse.

“Kin dai ga cikin mutane ne, bana son ki je ki ci wani abun da zai lalata miki ciki ko ki ci da yawa, kuma ki ci yaji ko ki zauna da yunwa, da ama ace Mama ce kadai ko Ammy zan iya yi miki magana a ganbansu amman Mama (Nana) ba zan iya miki magana a gabanta ba, pls ki kula da kanki”

“Tau”

“I love you”

Ya fada sannan ya cire abun ni kuma na bude motar na fita ta nufi bangaren Ammy, sai na ji ya kira ni.

“Babyna, za mu fara zuwa mu gaishe da Mama”

Juyowa nai na karaso inda yake tsaye ba tare da na ce masa komai ba, a tare muka jera muna tafiya zuwa part din Mama Fulani, yana ta kallon yanayin tafiya kamar mai kirga yadda na ke takawan. A falo muka samu Mama Fulani zaune kanta sanye da hular wanka hannunta kuma rike da brush an zuba masa mai daurin kirji ne a jikinta sai kuma wani karamin tawul da ta rufa a saman jikinta, Rukaiyah ya mata kafafuwanta. Zaunawa yai kusa da ita, ni kuma na zauna a dayar kujerar sai kallona take kamar bata taba ganina ba, gaba daya ta wani yi sakuku kamar ba ita ba, ni ban taba ganinta a cikin yanayin tausayi ba sai a yau.

“Mama yanzu kika tashi?”

“Eh Aliyu”

Ta amsa tana aje numfashi.

“Na'am, amman Mama ba ki jindadi ko?”

Ya tambaya cikin yanayin da ke nuna tsantsar kulawarsa a gareta.

“Muhseen ya duba ni ai, kuma yanzu idan nai wanka na karya zan sha maganai”

“Mama ina kwana”

Na fada ina dan risino kaina alamar girmamawa, sai ta kalleni kawai ta kasa amsawa kamar mai jin nauyi ko kunya, mikewa tai tsaye ba tare da ta amsa min ba ta nufi hanyar dakinta sai da tai rabin stairs sannan ta juyo ta kalleni sai kuma ta dauke kai ta shige dakin.

“Ku baku iya gaisuwa ba ne?”

Maganar Aliyu ta saka na maida duba a gurin Maryam da ke gyaran cucumber da kuma Rukaiyah wacce ta gama matsawa Mama Fulani kafafuwanta.

“Ina kwana ya Aliyu?”

Har sauri suke gurin gaishe shi suna hada baki.

“Ba ni ba ita, matata ce yadda kuka respecting dina haka ita ma za ku mata”

Ya fada babu alamar wasa a tare da shi, a tsakanin Rukaya da Maryam ban san wa yafi wani nauyin baki gurin gaishe ni ba, ni kan wani irin kunya da girma ne ya rufe ni a lokacin ba dan na san sai ya cilasta ni amsawa ba da ba zan amsa ba, sosai na ji daraja ta ta dagu, ba kuma dan sun san wacece ni a yanzu ba, sai dan auren dan'uwansu da ke wanda ya zama dole su girmamani ko da kuwa sun haife ni.

“Ta so muje bangaren Ammy mu gaishe su”

Ba musu na mike tsaye, ina gaba yana bayana har muka fito daga part din Mama Fulani muka nufi bangaren Ammy.

“Ba dan Mama tana jin kunyarki da nauyinki ba da yanzu ta rumgume ki tana nuna miki jindadinta da farincikinta aka my samun cikinki”

Ban ce masa komai ba, muka cigaba da tafiya, fuskarsa ba yabo ba fallasa muka nufo bangaren Ammy sai dai muna shiga falon ganin Muhseen zaune yasa ya dan canja fuska kamar be ji dadiba, ni kan har na yi farat zan fara masa magana sai na tuna cewar ina da aure a yanzu kuma ina tare da Aliyu. A saman kujera yake zaune Kamar yadda Ammy da Nana ma suke zaune a saman kujera, tun da nai sallama ya dago kansa ya kalleni sai ya maida idonsa gurin wayar be sake dagowa ba, har na zauna ina gaisawa da Ammy da Nana, Aliyu ma ya gaisa da ita, sai Muhseen ya mike tsaye ya face daga falon idonsa akan wayarsa ni kuma na bi shi da ido ina juyowa Aliyu ya watsa min harara a cikin sigar da babu wanda zai gani ya fahimta sai ni da akai wa.
Mikewa yai ya fice daga bangaren Ammy ya bar a nan, ni kuwa na tashi na koma kusa da Nana na zauna a kasa na dora kaina saman kafafuwanta, sai ta fara shafa kaina tana murmushi.

ALIYU POV.

Sam be jidadin ganin Muhseen ba ba kuma dan komai ba sai dan yana tare da Ataa, idan ya tuna cewar Muhseen ya taba son Ataa abun tana taba shi kuma yana jin babu dadi, duk kuwa da kasancewar ya aureta amman wannan kishin yana nan cikin ransa. Ko da ya shigo bangaren Mama Fulani yayi zaton zai samu Muhseen a falo ko dakin Mama Fulani amman sai ya samu akasin haka, domin kuwa Mama Fulani ce kadai a dakin zaune rike da brush din dazun tana kallon wani gurin kamar mai tunanin domin shigowarsa kadai har da zabura tai.

“Mama har yanzu laifina kike gani?”

Bata ce masa komai ba sai lasa lips dinta da tai cikin yanayin damuwa.

“Wallahi Mama Nasir ne ya kawo min wannan shawarar amman ba wai dan wata manufar nai ba”

“Ina maka murna Aliyu wannan babban abun farinciki ne da jindadi, ba zan iya fada maka ko misalta maka yadda na ke ji a yanzu ba, sai dai abun bakinciki na zan iya nuna ba”

“Saboda mi Mama”

“Kai ma ai ka sani Aliyu duk wani abun da zan musu a yanzu ko na nuna farincikina ba yarda za su yi da ni ba, kuma har abada Ataa ba xata daina ganin cewar bana sonta balle kuma abunda yake cikinta. Aliyu kunyar kaina na ke ji, kunyar kaina na ke ji sosai”

Ta fada idonta cike ta kwalla har ya fara sauko mata, murmushi Aliyu yai yana kokarin nuna mata shi be ga wani abun damuwa ba.

“A rashin sani kika aikata Mama, kuma ni danki ne, Ayusher ta sani dole ki so abunda yake cikina tunda har kina so na, na fada mata bani da kamar ke da Momy a duniyar nan, ni yanzu abunda na ke so ma idan kin yi wamka kin shirya kije ki roka min Mamanta ta bar min matata ni ba sai ta je d ita can nijar ba”

“Nijar za su tafi?”

Ta tambaya tana share hawayenta.

“Eh ta fada min tun shekaranjiya cewar Mamanta tace za su tafi ta ga dangi tare da Sarkin Agadaz za su tafi idan zai wuce, da na yi nijar bin ta muje tare, yanzu kuma na canja sha'awara gaskiya idan tai tafiya mai nisa da wani ganin dangi jagalgala cikin za ayi, kara dai tai hakuri sai idan ya girma sai mu tafi tare ko kuma idan ta haihu”

“Gaskiya ni ma ban bada goyon bayan ta tafi yanzu ba, taya zata fara yawo da karamin ciki ma?”

“That's why I love you Mama, kina da mugun fahimta, yanzu dai ki yi wanka sai ki je ki yi magana da Mamanta ki roka min ita”

“Aa ba zan iya ba”

“Zaki iya”

“No-no Aliyu i can't ai da kunya nai maganar a yanzu ma, duk abunda zan yi kar suke kallona, jiya mahaifiyarta ta kasa sakewa da ni, itam Ataa ba so zata tai b Wallahi balle har tai tunanin abun kwarai zan mata”
Chapter 121 · 0% Book details