Sashe 4
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Ya fada ba tare da ya kalleta ba, tsif tai kamar babu ita a gurin, ta san halin Aliyu sarai dan haka bata sake yunkurin sake yin wata maganar ba har suka isa bakin gate din gidasu. Bata jiran ya ce ta fita ta shiga gida, tasan halinsa farin sani ba tana da wahala ya iya bude baki yai magana musamman a inda zai iya isarda sakonsa da ido. Bude motar tai ta fita shi kuma ya hau titi ya dauki hanyar gidansa.
Horn daya yai aka bude mai gadin ya bude masa gate da sauri sanin cewar baya son jira, yayi minti biyar a cikin motar sannan ya fito yana rike da wayarsa ya nufi wata katuwar kofar mai ruwan zaiba. Door bell ya danna, Rahama ta bude masa kofa duk ta wani hade rai, kallonta yai from head to toe wani farin yadi ne a jikinta mai tsarin ja yadi ya fito da kyaunta da kuma dark skin dinta. Murmushi ya sakar mata kadan a maimakon ya fada mata cewar tayi kyau, sai ya ratsa gefenta ya shiga cikin falon kai tsaye sama ya haye ya shiga dakinsa dake cike da kamshin turare.
“Ni fa ba zan iya ba, na fada maka na gaji gaji”
Rahama ta fada bayan ta turo kofar dakinsa ta shigo, zuwa tai kusa da shi ta tana da yi masa mitar data saba.
“Aliyu na fada maka ni gaji, ga zafi sokoto ga wannan uban aikin fisabilillahi baka min adalci, baka tausayi na, tun farko sai da na fada maka ni ba zan iya zuwa na zauna ni kadai ba kace za a samu mafita gashi nan ka barni kullum sai sai wahala na ke ta yi”
Be dago ya kalleta ba, har ya gama cire agogon hannunsa ya bude maballan rigarsa sannan ya juyo ya rika kanta ya sumbanci goshinta ya saketa ya nufi bathroom. Ta saba inda fada ne zata yi ta gama be ce mata uffan ba wani lokacin ma har tambayar yake shikenan ko akwai wani? Magana tana masa wahala ainun kamar wanda aka idan yai maganar zata ragu .Haka rayuwarsa take tun yana karami indai ka girmeshi yai maka laifi sai dai kai ta nasa fada ka gaji ka bari ba zai ce uffan ba, idan kuma shi ne a sama da kai to baka isa ka daga kai ka kalleshi ba ma balle har kace zaka masa fada.
Baya son yanayi, magana tana masa wahala ko da zo ki karba ne, baya jira sai dai a jira shi, yawan kallo yana bata masa rai ko da kuwa shi zai shafe sa a daya yana kallonka ne, baya son hayaniya and when ever he say no that's means no for sure. Duk wanda yake masa da shi a cikin familynsu tun daga dangin uwa har na uba babu wanda ya isa ya tsare Aliyu da kallo balle kuma har ya cilasta shi yin wani abu. Mommy ce kawai ta isa da shi sai Daddy bayan su babu mai kallon idonsa kai tsaye yai masa umarni da yi ko hani.
Wanka yai ya fito daure ya tawul fuskarsa kamar ko yaushe ma'ana babu far'a balle murmushi. Kamar be san da zaman Rahama a dakin ba haka yabi ta gabanta ya wuce zuwa gaban maduba yana shafe jikinsa da karamin tawul. Tsadadden man shafi mai kamshin gaske ya shafawa kansa sannan ya juyo ya nufi wani bangare na daki da aka ware aka zuba masa tufafinsa a ciki. Rahama ta biyoshi tana magana cikin bacin rai.
“Ni fa na fada maka na gaji”
Be ce uffan ba, kuma be bar mata wata alama da ke nuna cewar yaji abunda take fada ba, ba kuma dan be ji ba sai dan haka dabi'arsa. A gabanta ya kwance tawul din jikinsa ya shirya cikin wasu kananan kaya wadanda suka kara fitar da kyaunsa da kuma aibarsa fuskarsa sai annuri take kamar sabon ango. Wata yar karamar dorowa ya janyo ya dauko pen da memo aurensu yai rubutu a kai ya mika mata sannan ya fice daga gurin zuwa bedroom.
“Na yi Magana da Mommy tace za a samo aikin, amman tace ki daina wahala da yawa saboda ciwonki kuma Jawahir zata rika zuwa tana rika miki aikin gida”
Tana gama karantawa ta saki paper a nan, ta saba karanta abunda baya iya fada mata idan an maganar basa kusa, wani lokacin kuma sai ya zauna ha fada mata kamar ba shi ba. Yana gaban madubi yana fesa turare ya hangota ta fito sai ta jingina da kofar closet din tsa dayan hannunta ta rike kanta, da sauri ya aje turaren ya nufi inda take hankalinsa a tashe ya rikata ya dawo da ita jikinsa daga jikin kofar closet din.
“Kin cika yawan magana Dear, kuma kinsan matsalarki”
Ya fada yana kissing front head dinta.
“Na yi magana da Doc Asim yace za a samo very soon, idan an samu sai muje waje a dasa miki, i can't wait to see you alive healthy”
Ya rumgume tsantsan a kirjinsa yana shafa bayanta kamar ba shi ba.
ATAA POV.
Sai da na kalleshi da kyau sai na gano ba shi yake min maganar ba, wata ce mace ce mai kama da shi take maganar tare da ziro min hannunta mai kunshin lallen hausa wanda yai baki sosai a farin hannunta. Ba tsaya karbar kudin wankin motar ba domin gaba daya hankalina ya gama tashi sai na juya da sauri na koma can gefen titi na tsaya ina kallonsu, jira nake naga ko zai fito ya biyo ni amman sai naga be ko kalli inda nake ba, yarinyar ce kawai ki aiko min da sakon zagin da hannunta. Wutar traffic ta saki suka kama hanya shi da sauran mutanen da ke tsaye da motocinsu, sannan na soma tambayar kaina, wai wayar waya na sata? Yaushe nai satar? A ina nai satar? Na san muna da talauci da yunwa amman hakan be tana saka mu maida abun wani namu ba, yo ni ina ma naga wayar balle na dauka. Wata kila wata mai kama da ni ce tai satar to amman wayar waye aka sace a cikinsu? Ita ko shi? Idan tashi ce ai da shi zai yi magana ba ita ba, ita kuma ai ban tana ganinta ba balle har tace na mata sata ko dai shine yai min kazafi yace na masa satar?
Koma dai mienene zan yi iya kokarin da zan yi na ga ban sake ganin wannan hadaddiyar fuskar tasa ba, wacce bata ko kallon mutane da kima balle har ta martabasu, yau kwana uku kenan kullum idan na hadu dashi sai wani abu marar kyau ya faru da ni, da farko fitsari nai kuma ya watsa min ruwan kazanta, na biyu kuma kuka nai har da wani jefar da rigar dana taba shi sai ka ce ni din ba mutum ba ce, wannan karon kuma an laka min satar wayar da ban san kalar ba.
Har nai na gama na nufo hanyar gida babu abunda nake sai miti da surutun rashin alherin da yake tare da wacan mutumen iyakar alkawarin da na daukarwa kaina ba zan sake hadu da shi ba, da alama nan gaba cewa zai yi wani na kashe ko kuma ya takani da mota ya wuce.
Yau kam ban dawo da wuri ba, domin a hanya magariba tai min, hango manyan motoci guda biyu a gidan da zan iya kiransa da hamu yasa ni hanzarin cira kafa na karasa ciki da sauri, Nana na samu risine a kasa tana rokon wani mutum kamar zata fasa kuka.
“Dan Allah ke yi hakuri Wallahi babu inda zai je, shiyasa ya laba nan shi da yaranshi”
Babban mutumen mai rigar arkin dake nuna isarsa da tarin dukiyarsa ta dakawa Nana tsawar da har sai da naji ciki raina.
“Babu ruwana da wannan, akan mi za ku zo ku bata min gida, ku san nawa na zuba na siye filin nan, an fara min gini sai kawai ku zo ki shige kuna lalata min guri”
A nan nima na zubar da kayana na shiga rokonsa kamar yadda Nana ta hade hannayenta tana rokonsa.
“Baba dan Allah kai hakuri Wallahi idan ka koreni daga nan ban san inda zamu je ba ba mu da kowa”
“Ba ku da kowa daga sama kuka fado? Daga ina kuka taso kuka dawo nan? Ku koma can ni bana son ganinku anan, ku bar min gida na fada muku idan na sake zuwa na tarar da ku a nan sai na wulakanta ku”
Yana fadar hakan ya bude motarsa ya shiga, sauran mutane da suke tare da shi suka shiga dayar motar suka bi bayansa. Kallon mahaifiya dake kuka nai ina kwalla sai kuma na daga kai na kalli yar bukkarmu, miye laifin mu dan mun raba a wannan gidan tunda ba a ciki muka zauna ba, miye laifin bukkarmu mu dan kawai mun zauna a ciki.
“Yau ko mun shiga uku an koro mu can nan kuma an kore mu, yau ina za mu?”
Shine abunda mahaifiyata take fada ya yaren buzanci tana kuka. Zuciyata ta sosu sosai tana da gaskiya domin idan har kuma bar nan ban san wani guri da zamu iya rabawa ba, domin ba mu san wani gurin da zamu iya zuwa mu nemi taimakon gurin zama ba. Daga ni har Nana haka muka wuni cikin damuwa da rashin walwala har garin Allah ya waye, da safe Nana ta aika Lukman ya siyo mana waina ni da shi ita kuma ta gagara cin komai. Sai dai hakan be hanata fita bara ba, ni ce dai ban je ba, daman yau bana jin fitar saboda abunda ya faru jiya na laka min sata da kuma zancen barin gurin da muka raba, sai duk haka yasa ni jin kamar ma bani da lafiya, sai dai yau na samu yin sallah biyu a cikin lokaci tun a gida na wuni kuma bana aikin komai, wato azahar da la'asar ban da Asuba da da nai bayan rana ta gama bayyana.