← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 28 OF 143

Sashe 28

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba yanzu ba”

Da mamaki ta daga kai ta kalleshi.

“Saboda me?”

Shiru yai for like five minutes before ya bude baki ya ce.

“We need to help her”

“Who?”

“Yarinyar da aka cirewa mahaifiyarta koda, zata iya shiga wani hadarin saboda mu, be kamata mahaifiyar yarinyar nan a jikinki ba, tana kallon mu a matsayin azzalumai, kuma ta rayu a cikin kallon zalintar za mu sake yi wani zai iya fakewa da mu ya zalince a again”

Wani irin zaranannen kallo tai masa kamar ya ce mata za a cire kodar jikinta ne a mayarwa mahaifiyar Ataa....

______________________________

Assalamu Alaikum.
Kamar yadda na fada yau na kai karshen free pages wato page 15, nace 12 zan kare free pages wasu suka roki n kara na kara to 15.

Masu niyar siya za su iya sending 300 to 0314795884 Abubakar Hadiza Gt Bank, sai ku turo shaidar biyan ta number nan 08036126660. Yan nijar kuma za ku turo 500fc ta number nan +22790165991 sai ku min magana ta number nan 08036126660 zan saka ku group.

And for our yan kasuwa da suke son a tallata musu hajarsu it's 4k via 08036126660.

Masu niyar siya da marasa niya duka Allah ya wadata mu da arzikin na halal. Thanks 🙏😍🌹
1️⃣6️⃣

A wani babban gida muka kwana da alama ta san mutanen gidan domin na ji sai tambayarta wasu suke tana cewa suna lafiya. Shayi da biredi aka kawo mana da safe muka karya sannan muka shiga bandakin mukai wanka da shower abun ban taba ba kuma na dade ina mafarkin yi. Bayan mun shirya aka sai ta waremu mu uku muka shiga motar da muka zo da ita, ni da wata Murja da Humaira.
   Tafiya ake ta yi ni dai ban gane inda muka dosa ba, ban kuma zan iya cewa ga inda aka bi ba, domin akwai tazara sosai tsakanin unguwar da muka saka da kuma wance za mu je, har ya zamana da za ace na dawo da kaina ba zan iya ba. Sai dai abunda na kura da shi unguwar ta manyan mutane ce, domin manyan benaye ne a unguwar sai kuma wadanda ba benaye ba amman masu kyau sosai da daukar hankali, a bakin ko wane kofar gida an kawata shi da furanni, kuma babu kowa a unguwar sai manyan motocin alfarma da ke wuce shi ma jifa jifa. Ba dan na san halin Maman Salma ba da na zargi ko wani abun za a min a unguwar domin a rayuwata ban taba zuwa irin wannan unguwar ba, hasalima ban taba sanin cewar akwai irin wadannan manyan gidaje da benaye masu kama da ma'aikatu a Nigerian ba.
  A bakin wani kato gate direban mu ya tsaya, yai horn, wani matashi mai siffar karfi da kuzari ya leko ya zo har gurin motar suka gaisa da Maman Salma sannan na koma ya bude mana gate din. Da muka shiga gate din farko sai na hango wani gate din a tsakanin tafiyar wacan gate din da na farko yai taku sittin bayan shi kuma akwai wani dan karami da aka kawata da furanni, banbancin gate na biyu da na uku na ukun irin wannan ne da aka saka kawai dan kwalliya wanda zaka iya hango na ciki na ciki kuma ya hango mai shirin tahowa, na biyu kuma be kai na farkon girma ba, na farko shine kato gashi dogo kamar yadda ginar gidan take.
  A wani kato fili direban ya aje motarsa, yamma da filin an kafa wata katuwar rumfa mai kala wance ta lullube wasu manyan motoci da ban taba ganin irinsu a sokoto ba, da alama gidan kashi uku ne, bayan bangaren da ke fuskarta mai shigowa ga wani can yamma da motoci, kuma akwai wani arewa da motocin, gaba daya gidan da duk wani abu na kwalliyar gidan na glass ne, ya wasu furanni kananan da suka kara haska gidan, bayan wadancan na nesa da mu da na ke hangowa masu tsayi da hudu an musu yar karamar kofa, da alama Garden ne kamar yadda na ji ana fadar cewar gidajen masu kudi suna yin Garden, muna rufe motar sai ga barewa ta fito da gudu daga Garden din da kahoninta tana kallonmu kamin ta juya da gudu ta koma ciki.
Tsuntsun maka ne Peacock har guda hudu ke ta yawo a harabar gidan yana bude fukafukansa abun sha'awa, wani irin shauki ne ya kamani da kuma tsoro a lokaci daya, domin irin manyan masu kudin nan ba su cika ganin kimar talaka ba, balle kuma ace za ka yi aiki a karkashinsu ne.
  Daya daga cikin part uku da suke gidan muka nufa, Maman Salma na gaba muna biye har muka isa, gaban kofar ma duk furanni ne irin na kaskon nan an kawata katuwar kofar da su. Wani dan maballi ta danna taja baya ta tsaya jiran bude mata amman ba a bude ba, sai ta sake danna bayan wasu mintuna, nan ma sai da aka kara bata lokaci sannan aka bude kofar falon. Ba mu ga wanda ya bude mana kofar ba, da alama wanda ya bude komawa yai ya zauna a daya daga cikin manyan sofa din da suke katon falon mai kama da falo uku.
Wani kamshin masu arziki da turaren mai tsada ne ya fara yi mana marhabun kamin ac da ke falon ya karaso garemu. Wasu manyan yan matane su hudu hakince saman kujera suna kallon wani kato tv wanda ban taba ganin irinsa ba tun da Nana na haifo ni duniya. Babu wacce ta juyo ta kallemu daga cikin yan matan balle ta amsa mana sallamar da muke, duk kuwa da irin daga mana hannu da Maman Salma take na alamar mu sassauta muryarmu.

“Hajiya Rukaiya da Hajiya Maryam ina kwananku?”

Maman salma ta fada da dukan far'arta sai a lokacin ne yan mata suka dago suka kallemu, wacce na ke zaton ita ce Maryam din ta amsa a kaikaice tana mana kallo ba uku saura kwata, yayinda Rukaiya ta sakarwa Maman Salma Murmushi kadan, sannan wacce ta fi su kurciya ta dago ta kallemu sai ta maida kanta gurin zeeworld din da suke kallo.

“Na ce ko Hajiya tana nan?”

Maman Salma ta tambaya kamar da tsoro, sai wacce aka kira da Rukaiya dazu ta kalli karamar ta ce.

“Baby je ki kira mata Mama”

Da kamar ba zata je ba, sai kuma ta mike tsaye tana sanye da wasu guntayen kaya irin na turawa wato dogon wando da be kai kasa ba, da kuma t-shirt ta mata mai guntun hannu kanta ba dankwali an yi mata kitson attach tsorayen sun sauko har bayanta. Wata katuwar mattakala ta nufa irinta ta indiyawa mai fadin ta fara takawa a hankali har ta haye sama gaba daya, daya daga cikin dakunan da muke hange ta tura ta shiga. Shiru shiru bata fito ba har kusan awa daya sannan muka hango an bude kofar wata kasaitacciyar mace mai isa da ji da kai ta fito daga dakin tana sanye da wata dakankiyar shadda mai kamar kamfala sai shining take kamar an shafa mata mai. Da ďai-ďaya matar take takawa tana saukowa stairs din wani saurayi mai kama da ita na gafenta fuskarsa dauke da murmushi ya zuba duka hannayensa aljihu.

“Mama ba ki yarda da ni ba”

Saurayi ya fada bayan sun sauko tare yana kallonta. Uffan ba ta ce masa ba bayan hararar da ta watsa masa ta nufi wata one seater da ke fuskantar mu ta zauna, shi kuma saurayin ya zauna hannun sofar yana cigaba da gitse dariyarsa. Maman Salma ce ta fara mika mata gaisuwa ciki da girmamawa daga kasan tile din da muke zaune mu da ita. Sai Hajiyar ta amsa da far'arta kadan tana shigar da idonta can ciki a yayinda take kallonmu irin kallon nan na rashin ganin kimae talaka.

“Lafiya Kalau Ramatu an shigo”

“Eh Wallahi, dama na fada miki zan shigo ai”

“Haka ne, suna wadannan yaran?”

“Eh sune sai ki zabi wacce kike so, idan ma duka za ki dauka ga su nan dai”

Maman Salma ta fada tana dariya.

“Aa daya ta isashe mu,wanke wanke ne kawai sai shara da mopping da dan aikin da zai taso, kin san ni bana yarda yar aiki tai min girki, haka ma Ammy bata son girki”

Ta fada tana daga hannu kamar bata son motsa jikinta. Ina dauke idona daga gareta na kalli d'anta sai na ga ni yake kallo kamar mai mamaki, maida kaina nai kasa na sake dagowa muka hada still ni yake kallo.

“Mama kin ga kyau? Subhanallahi ahsanar halikin amman wannan yarinyar Allah ya miki kyau, you're so pretty”

Ya fada yana kallona daga can inda yake zaune.

“Mama wannan yar Fulanin za mu dauka tashin hankali”

Ya sake fada yana kara kallo da kyau, wanda hakan yasa sauran yan uwanshi mata suka dago suka kalleni, a cikinsu babu wance ta ce ina da kyau suka maida dubansu gurin tv da suke kallo.

“40k za mu biya idan ya miki”

“Eh yayi Hajiya Allah amfana mana su, ke kuma kina da 30k a wata ni ina da 10k ya miki?”

Maman Salma ta fada tana kallona da sauri na gyada mata kai da sauri zuciyarta cike da jindadi har dubu 30k. 

“Bude baki ki yi mana na ji muryarki mana kyakkyawa”

Saurayin ya fada yana kallona, sai Hajiya ta daka matsa tsawa tana kallonsa.

“Muhseen what this?”

Mikewa yai tsaye yana dariya ya nufi gurin da sisters dinsa suke zaune ya zauna. Sannan Hajiyar ta kalli Maman Salma ta ce

“Ki fada mata yadda komai ya ke, sannan ki kai ta bangaren Ammy ta ganta kuma ta nuna mata aikin da zatai”

Maman Salma ta juyo kaina ta nuna min Hajiya.
Chapter 28 · 0% Book details