Sashe 107
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Haba Rahma, ai Wallahi Aliyu yayi hakurin zama da ke na lokaci be yi aure ba, duk kuwa da irin ciwon da kike fama da shi, yanzu kuma ai ke kika jawa kanki haka kawai daga dan abu kadan kin kwaso kin dawo gida kuma mahaifiyarsa ta zo bikonki Mommy ta ci mata mutunci har da mata gorin danta baya haihuwa bayan kuma ita ga yarta nan ba lafiya amman ya zauna ke a haka, ai wallahi indai ba wawa ba ne dole yai aure ya shareki, kin ga ko wannan tafiyar da kikai zuwa dubai ba da izininsa kika yi ba, kuma kin san hakan be dace ba, kin barshi can shi kadai kamar marar galihu kuma yanzu yayi aure har ki yi korafi ai Wallahi ki gode Allah da be aiko miki da takadar sakinki ba”
Rahma ta kalleta da sauri.
“Ya kira ni yanzu bam dauka ba, ko sakina zai yi? Na shiga uku Wallahi ina son mijina Ikram”
Ta kara fashewa da kuka.
“Indai kina son mijinki ki shirya tsakaninki da shi, kuma ki tattara ki koma dakinki ki zauna lafiya da abokiyar zamanki”
“Ba zan taba zaman lafiya da wace ta aure min miji ba, kuma yar aiki gidana yar talaka marar daraja, ba zan taba bari ta haki iska mai kyau a gidan nan ba”
Ta fada tana jin cewar zata iya hana Ataa sukuni da walwala idan har ta koma gidan, domin ta san Aliyu yana sonta ba zai hana ta yin komai ba ciki kuwa har da musgunawa Ataa, wata kila ma baya son Ataa ya aureta ne kawai saboda Momy da Mama Fulani, ce mata da yai wacce zata kula da shi ya aura ta ina Ataa zata iya kula da shi yarinya karama kuma wacce bata waye ba yar talakawa wacce bata leka ko'ina ba balle har ta san yadda duniyar take ta san soyayya. Share hawayenta tai tana jin cewar ta samu mafita domin idan har ta koma gidan sai ta kori Ataa.
“Dan Allah ta so muje kowa yana can ana murna, bikin da za ayi Daddy yace mai gidansa ma zai zo”
“Wanda yake kasar Agadez?”
“Shi fa ya ce ya fada masa da wuri kuma yana ganin zai zo saboda yace zai zo ganinki be samu zuwa ba ga kuma gobarar da aka masa be aiko ba kuma be zo ya masa jaje ba, sannan yanzu kuma ga bikin Amra yana ganin zai zo domin akwai ma wani kamfani da aka siya masa a Abuja da jigawa idan ya zo duk zai kai ziyara ya can”
Rahma ta kara share hawayenta ta mike ta bi yar'uwarta suka fita tare zuwa falon gida na inda kowa ke zaune ana wasa da dariya da kuma duba lefen da aka kawo.
*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
*Khadeeja Candy*
Mama Fulani na zaune falo waya a kunnenta tana magana a hankali ita da kawarta Hajiya Zainab Arzika, Muhseen ya shigo falon fuskarsa dauke da murmushi wayarsa kuma a hannunsa yana kallon wayar har ua zauna, gaba daya hankalinsa yana gurin wayar.
Sai da Mama Fulani ta gama wayar sannan ta kalleshi.
“Ya akai Muhseen”
“Lfy kalau, Mama duba min yarinyar nan tana da kyau kuwa?”
Ya mikawa Mama Fulani wayar da ke rike a hannunsa mai dauke da hoton wata kyakkyawar yarinya.
“Kai mashallah amman tana da kyau Wallahi wacece?”
“Surukarki ce”
Ya fada da murmushi a fuskarsa.
“To ai ba girin girin ba tai mai ba na saurin murna saboda ban san ko yar wacece ba kar a min na Ataa?”
Ambatar Ataa da Mama Fulani tai yasa ran Muhseen ya dan bace domin baya son tuna a yanzu balle kuma jin suna ta.
“Wannan fa yar bachi ce kuma mahaifine shine Shugaban ma'aikata”
“Shugaban ma'aikata na nan Abuja ko na can bauchi?”
“Nan Abuja”
“Wow amman ka kyauta haba ni kan yanzu na ji magana, ina kuka hadu?”
“A twitter muka hadu, har na je gidansu mun gaisa sau biyu ma”
“Mashallah tana dai son ka ko?”
“A yadda ta karbe ni kan ya nuna haka, Mama ai yana da wahala in shiga wani gurin ace ba a so na gaskiya”
Mama Fulani ta yi murmushi.
“Yanzu na ji batu za ka yi auren cire raini kuma auren da kai aure yanzu ka dawo cikin hayyacinka, Maryam Rukaiya ku fito ku ga kyakkyawa”
Mama Fulani ta karasa tana kwala musu kira. Rukaiyah ce ta fito yayinda Maryam ta ke can cikin daki abun duniya ya isheta saboda baikon da akai ma Humaira, gashi ita ce babba, wadanda suke warin Rukaiya ma Barula da Zee ta san na gaba kadan tsayar da mijin za su yi a barsu su kadai ita da Rukaiya a gida sai kuma kanensu kanana Baby da Inteesar.
Da far'a Rukaiya ta sauka domin daga jin yanayin kiran Mama Fulani ta san wani abun ne ya samu, kusa da Muhseen da ke murmushi ta zauna tun kan tai magana Mama Fulani ta mika mata wayar tana dariya.
“Kin ga wacce yayanki ya dauko yar mutanen arziki”
Rukaiya ta karba tana wara ido.
“Wow amman wannan yarinyar akwai kyau ni kama na santa ma”
“Ba za ki rasa saninta ba tana da mabiya da yawa a twitter”
“Amman tana da kyau sosai gaskiya wane gari take?”
“Bauchi amman a nan suke zama Abuja tare da Babanta”
“Gaskiya Ya Muhseen ka dauko mai kyau”
Murmushin jindadi yai shi dai yana son ace ya auri mace mai kyau kuma yana son ya auri mace da idan abokansa da kowa na shi ya ganta sai sun sara mishi akan kyauta inda za a rika maganarta a duk inda ta wuce.
“Ita da Ataa wace ta fi kyau?”
“Haba dai ka sawo wannan kazamar yarinyar, wannan ai ta fita cika da komai wannan fa babban budurwa ce Ataa kuma yarinya karama da ita kuma ita Ataa yar ba yar kowa ba ce wannan ko yar masu abun ce, wannan ma ai har ta fi Ataa kyau sai dai kawai ace ita hancinta ya fi na Ataa kauri shi ma dan Ataa tana yarinya ne”
Wani irin dadi ne ya lullube Muhseen yana jin cewar yanzu kan yayi zabe kuma ba zai yarda ta subuce masa ba tunda har Mama Fulani tana sonta.
“Daman can fa akwai mata masu kyau saboda ba ku dubawa ne shiyasa ba ku san da su ba, yanzu ba gashi ba, shi ma Aliyu da be yi sauri ba da ya hadu da mai kyau ai wacce ta fi Ataa”
Mama Fulani ta fada.
“Amman ina magana Amina? Ba Momy ta ce ta baka Amina ba?”
Cewar Rukaiya tana kallonsa sai ya amsa mata kai tsaye.
“Bana son ta ana zancen mata masu mahaukacin kyau kya sako min Amina?”
“Aiko Amina na kyau Muhseen”
Ya kalli Mama Fulani cikin wacce tai maganar.
“Tana da kyau ai na sani, amman na irin wanda na ke so ba, ni na fi son mace mai kyau bala'i wacce kowa zai san na aura, wannan ma ba barinta zan yi ta dade ba kar wani yai min kwantar 6auna dan haka ku fara shiri tun yanzu, Mama kuma ki fadawa Abbah idan kun tattauna za mu yi can tsakaninmu”
“Karka samu damuwa Muhseen In-Sha-Allah sai ta aureka, ko nawa ake kashewa za mu kashe mu aurota”
Muhseen ya mike tsaye yana jindadin furucin Mama Fulani daman ya san zatai supporting dinsa tun da yar masu kudi ce, shi kuma ya samu kalar da yake so saboda tana da kyau shi daman kyau ne kawai abunda yake iya saka shi ya so mace. Ba ya jin zai dauki lokaci be yi auren ba kamar yadda ya fadawa Mama Fulani saboda ya cire haushi Aliyu ya nuna masa ya samu wacce yake so cikin kankanen lokaci kuma mai kyau kamar Ataa auren kece raini zai yi auren da zai amsa sunansa a garin Abuja.
Rukaiya ta tabe baki tana kallon Mama Fulani.
“Ai idan akwai irin wadannan kyawawan ba yadda za ayi maza su zo su ce suna son mu”
“Kin ji ki da wata magana, ita Humaira kyau ta fi ku ne? Kuma ai kyawawa ne kuma ko ba a son dan kyau ba a so ku dan kudin ubanku”
“Amman Mama irin yayan manyan amsu kudin nan ina ruwansu da kudin ubanmu? Ai suma cewa za su yi suna da kudinsu ko ubansu na su to miye abun so kenan?”
“Ai wani dan ace yar wani ya aura mace ko bata da kyau zai aureta, balle ki da kyau na ku, ku kwantar da hankalinki kuma na ku yana nan zuwa In-Sha-Allah, dan Humaira ta samu au sauran suna nan su ba a musu baikon ba kuma Humaira ce kanwarsu”
“Amman Mama kin ga Batula da Zainab fa yayan mutumen nan sun ce suna son su kin san ko ba abunda zai hana auren sai idan mazan ne suka fasa, azo a yi musu aure mu muna nan zaune”
Rakaiya ta karasa tana buga kafa kasa tare da bata fuska kamar za tai kuka.
“To laifin waye? Kullum kuna nan cikin gida ba fita ko yar kwarkwasar nan mai janyo hankali maza ba ku iya ba ai dole bakin jini yai muku yawa, ita wannan ba ta Twitter Muhseen ya fadu da ita ba? Ku da wani be hadu da ku ba? Amman kwaliya ma sai dai kawai ku shafa mai ba wani kwaliya”
“Su ma ai ba kwaliyar suke ba Wallahi har mun fi su kwaliyar arziki, amman gashi nan duk sun samu kuma ko kamin wacan na nijar din su zo ai kowacce sun tana da samarinta amman mu babu ko daya”
“To kwantar da hankalinki ai Abbah ku yace sarkin Agadaz zai zo ya duba kamfanin da kansa da wasu dabam da suke wani gurin kika sani idan suka zo ko wani ya ganku ya ce yana son ku, ku dai ku yi fata kawai Allah kawo shi lafiya kuma Allah ya saka su ce suna son ku kamar wannan family idan na samu ke ko maryam kuka shige ai shikenan na huta nikan tawa samu na hada surukanta da Sarkin Agadaz”