← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 137 OF 143

Sashe 137

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Haka ya janyo ni har gurin motarsa ya bude min na shiga ya rufe sannan ya zagayo ya shiga mazaunin direba ya tashi motar muka dauki hanyar gidan Momy.
Ina shiga dakin Momy yai kan Mama da gudu na rumgumeta ina murna. Matan da ke tare da ita sai suka saka dariya suna ta kiran wai na cika kurciya, Momy ma dariya take tana fadin haka muke ni da Husna da Siyama kusan halin mu daya Amina ce kawai mai hankali, sai da muka dade a dakin muna fira ni har na manta da Hamma sai gashi ya shigo dakin da kunya ya gaishe su tare da musu fatar an zo lafiya sannan ya fita. Wani abun haushi abun mamaki Mama ta yi ma kowa tsaraba, a gidan sun daga kan Daddy har Momy da Amina Husna da Siyama kai har Hamma sai da ta siyo masa wata dakakkiyar shadda yar Agades amman ban da ni, nikan Nonon Ragumi ne kawai tai min tsaraba da shi. Misalin biyu saura na rana muka fito zuwa inda ake bukatar ganinmu, ni da Hamma a mota daya Mama kusa ta shiga wata mota da yan'uwanta maza suka zo da ita daga can inda suka sauka.
Ko da muka isa gurin biyu daidai, wani katon gurine mai kamar ma'aikata, yan'uwan Mama maza da Hamma suka shiga gurin da aka tana da domin sallah, ni kuma da Mama da wata yar'uwarta da ake kira da Mama Lattu muka shiga wani dan fili mai kamar dakin karatu mukai na mu sallah.
Ba mu zauna a dakin ba sai uku daidai domin bayan gama sallah sai da aka jira isowar wasu daga cikin wadanda za a zauna da su. Maza da mata ne da yawa a dakin za su kai su goma a dakin, sai wasu kujeru da aka jera can dabam wadanda aka nuna mata aka ce mu zauna, duk irin kusancina da Hamma na kasancewar mijina hana shi shiga akai a gurin, da kuma yan'uwan Mama sai aka hana su shiga, wai da mu kawai suke son su fara magana.
Inda Doc Asim yake zaune da dabam da inda muke zaune, sai kallona yake kamar be tana ganina ba, na kalleni ya kalli Mama wata kila mamakin rayuwarta ya kashe shi ko kuma mamakin kawo kararsa yake oho, sai dai a yanayin da ya ganmu daga ni da har Mama ya sam yanzu ba kamar da ba ce domin ta canja zane. Da turanci suka fara magana kamin dayan ya fara yi da hausa yadda ni da Mama za mu fahimta.

“Doc Asim ka san wannan?”

Sai ya kalleni ya gyada kai.

“Eh na santa”

“A ina ka santa?”

“Ta yi zaman jinya asibiti tare da mahaifiyarta a lokacin da ta siyar min da kodar mahaifiyarta”

“Ke kin sanshi?”

“Eh shine likitan da ya cire kodar mahaifiyata ba tare da sanina ba ko saninta”

Daga haka suka fara karanto masa abunda ake kara akansa da kuma zarginsa da ake.

“Wannan yarinyar fa karya take ita ta siyar da kodar mahaifiyarta, kuma ta kai karata a gurin police ba ta ci nasara ba suka koreta shine yanzu take kokarin ganin ta bata min suna, wasu ne suke sakata saboda aci min zarafi”

Sai da suka tambayeni sannan na bayyana komai yadda ya faru ciki har da kulleni da akai gurin police, da suka tambayi ko ina da shaidu akan hakan sai na ce shukura ce ta san komai yadda ya faru.

“Fine na yarda a nemo shukura za ta fadi gaskiya ai, and zan kawo takardar da ta saka hannu akai za ku ga komai”

Yana fadar hakan na raya a zuciyata cewar akwai abunda yake kokarin shiryawa, wata kila ita ma zai siyeta kamar yadda yai ma polisawan da suka kama ni.

“Za mu cigaba da bincike, za mu gone gaskiyar lamarin idan har ba shi da laifi za mu hukuntashi, kuma zamu mika shi kotu domin ta hanke masa hukunci daidai da abunda ya aikata, ba zamu yarda wani likita ya bata mana aiki ko suna ba, ko kuma ya taka daya daga cikin dokikinmu, idan kuma ke muka samu da laifi yin masa kazafi za mu hukunta ki babu ruwanmu da kasancewar jikan Sarkin Agadaz babu ruwanmu da kudin kakanki ko babanki za mu hukunta kuma mi mika ki kotu domin a yanke miki hukuncin daidai da abunda kika aikata”

“Na yarda”

Ina fadar hakan Doc Asim ya maida hankalina a gurina, wata kila yana mamakin yadda nake da karfin hali ne wata kila kuma yana mamakin jin alakata da wani babban mutum nw kamar sarkin Agadaz da kuma zancen kudi da sukai ko da be san waye shi ba yana ji ya san ba karamin mutum, a take yanayinsa ya canja ya koma kamar ba shi ba rama yai ko lalacewa ba, yana nan yadda yake amman hankalinsa ne a tashe, domin ya san waennan likitocin ba kamar police ba ne da zai iya siye su ba. Ninkaina a yadda na gansu na san za su adalci ko da yake abun ba a fuska ba ne, da a fuska ne da Doc Asim ba zai min haka ba.
Dukanmu da farinciki muka dawo a mota na ke labartawa Hamma yadda akai yana ta kara kin kwarin guiwar cewar za su yi adalci domin gurin ba gurina na wasa ba, kuma ya san wasu daga cikin ko dab ganin abun ya fito ta bangaren Mai Martaba dole su kwatanta adalci domin ya nuna musu hakkin yarsa yake son a bi masa, abu na biyu kuma ba za su so wani likitan mai zaman kansa ya bata musu suna ba.

A gidan Momy na wuni ni da Mama domin bayan Hamma ya aje ni sai ya shiga gari, muka wuni muna ta maganar likitan har ake dauko zancen wasu likitocin masu taimakon da gaske da kuma wasu masu halin Asim sai dai su ba su kai shi ba ba domin na shi ya yi yawa ba kowane mai imani ne zai aikata haka ba. Daga bisani Mama ta dauko min labarin yayan Ammy da wasu yayan yayyunta ke so, wai magana har ta yi nisa ta kai gurin Mai Martaba ana zancen yin baiko. Na jidadin sosai jin cewar yaran Ammy ne duk dai Mama bata rike sunansu ba, amman ina ayyana cewar Humaira ce da Anty Zee, sosai na so ganin fuskar Mama Fulani da Maryam dan na san ba zata jidadi ba, saboda ba son shiri da Ammy take ba, kuma babu wanda zai so y'ar kishiyarsa ta samu jiki ta sa bata samu ba, balle Mama Fulani dake ta falako a cikin gida da nuna isa. Lallai Allah mai yadda ya so, kuma sai ya bawa Ammy surukai a cikin jikokin Mai Martaba yayan masu arziki wanda nasan Mama Fulani ce zata fi kaunar hakan.

Sai da dare muka koma gida, bayan Mai Martaba ya sake Kiran mama ya fada mata cewar an saka wani ranar Assabar mai zuwa wato nan da kwana biyu kenan. Kamar yadda ya saba yau ma sai da siya mana dan abun tabawa a baki sannan ya muka isa gida yana rike da hannuna kamar ba zai sake ki ba.

*** *** ***

Gaba daya al'amarin duniya ya koma mata sabo kuma ya zo mata ta inda bata zata ba, bayan daukakar da Allah yai ma Ataa akansu ya daukakata fiye da su sai kuma Allah ya kawo ma yaya Ammy miji daga cikin zuri'ar da tai kwadayin yayanta su samu, har magana ta fara karfi ga nata yayan babu wanda ya taya ban da Kamal shi ma Kamal din ma tun da akai fada da shi akan Ataa be sake kula Maryam ba. Balle Rukaiya ita ko zancen ba a ayi yadda kasan ta kasa kashi haka take, ga shi ba kyau ne babu ba amman babu mai gani ya taya kamar wanin abun amai. A yadda take so ita bata ki an hade su da auren Muhseen da za ayi ba, ita ta wanke su gaba daya ta huta ya zamana baby ce kawai ta rage mata.

Fitowa tai daga kitchen ta nufo inda Maryam take zaune tana lasar waya ta fara mata masifa kamar mai jin haushinta.

“Ai dole ku rasa mijin aure, ina can ina aiki kina nan kina lasa waya, idan safiya ta waye dakinku kawai kuka iya gyara kamar ku? Ace ba za ku iya aikin komai ba? Idan ma kun yi auren ai ba duka namiji ne zai dauki haka ba, dan ba ko wane namiji na kamar Aliyu ba da zai yarda da hali irin na Rahma wanda yai kama da halinku, su yayan Ammy haka suke? Indai auna nan ai su suke mata komai ku gyara ko'ina girki ne kawai nata shi ma wata rana su suke yi, gashi nan ai Allah ya basu maza a cikin waenda nai muku burin samu saboda ku ba ku san ku yi tausayina ko idan ina abu ku rika min ba, duki ki ga yarinyar Ataa haka ta zo tana aiki a gidan tai nan ta yi a can gurin Ammy duk akan mahaifiyarta kuma da Allah ya tashi bata gashi nan har Muhseen da Aliyu sai da sukai fada akanta, kuma yanzu gashi nan Aliyu take aure, mai taimakon uwa ai baya faduwa amman ku kullum kuna kan waya sa kan gado sai ka rantse kujera sai idan na gama ku taso zuwa dinning room dan ba ku da kunya”

Maryam ta kalleta cikin jin haushin fadan na ta ta ce.

“Oh Mama yau kuma duk wannan fadan a kan mu? Kamar dai kin gaji da ganinmu”

“To wace uwa ce zata so yayanta kamar ku su zauna a gida suna jera tsawo da ita? Yanzu idan an wanke Zainab da Humaira ai kubkadai kuka rage domin na ji Abbah ku na zancen har da Batula zai aurar tunda tana da mijinta amman ku ko mai sallama babu, balle mai zancen aure ko a wayar nan da ake haduwa da maza ku ban ku, ace kuma tausayina da yanzu kuma Allah ya tauyasa muku ya baku inda za ku huta ku jidadi”
Chapter 137 · 0% Book details