Sashe 129
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wani Dattijo ya fada yana nuna min inda zan zauna din a kusa da shi. Ni da Aliyu muka zauna a kasa sai ya fara nuna waenda zan gaida sune iyayena da kuma abokiyar zaman kakata, da kuma sauran da suke yan'uwana wasu dai ban ga fuskokinsu a jiya ba, sai yau ina kyautata zaton zuwa su kai a yau, sai haba haba suke da ni da kuma Mama. Duka zuri'ar Sarkin farare tas wasu ma har sun fini fari da jar fata, ga kyau kamar larabawa daga mayan har yara da matashi farare ne, sai dai wani ya fi wani farin, a cikin hakimansa kuma akwai fafaren da bakeke, matanyen na sanye da shadda ga wani uban ginari a hannu da wuya ko wacce ta saka gwanin sha'awa.
A lokacin da sarkin ya shigo sai da kowa ya mike tsaye masu kirari ta bude rigunansu suna tare masa gaba da baya suka fara wasu kuma na fita da katon mafecinsu. Yadda ake ma sarkin sai da abun ya burgeni kuma ya kara min jindadi. Sai daya zauna sannan kowa ya zauna, da dai daya masu rawanin suka fara zuwa suna mika masa gaisuwa baya amsawa sai dai badawansa su amsa a madadinsa har suka gama gaisuwar.
Sai da yao gyaran murya sannan yai dan jawabi akan dawowa Mama da kuma zancen yafiyar da yai mata, sannan ya sallami wadanda ba familynsa ba ya bar iyalan gidansa kawai ya sake gabatar musu da jawabi tare da nasiha da kuma jan kunne akan al'amurran rayuwa, fada musu abubuwan da ya samu Mama na bijire musu da tai a ciki har da zancen cire mata koda wanda kowa be san da maganar sai a yau. Babu wanda be girgiza ba da jin lamarin kuma aka tausayawa Mama, duk na san ba za a rasa wadanda a zuciyarsu za su ce Allah ya kara ba domin ita ta jawa kanta. Hankalin kakarmu ya tashi sosai jin cewar an cirewa Mama koda sai dai Mai Martaba ya shaida mata ya jaddada mata kuma ya tabbatar mata da cewar za a kwato mata hakkinta domin tuni elya mika abun ga kungiyar likitocin kasar, ko zuwan nan da zai yi sai da ya roke su akan su daga mana kafa ta samu zuwa ganin danginta kamin su gama tattara bayanai.
Yayi takaici kuma ya nuna bakincikin akan abunda ya faru da kuma gina mana rayuwa da tai ba tare da yan'uwanta ba. Sai dai abun jindadi kuma mai muhimmanci dawowarta a yanzu wanda hakan zai ba ni damar sanin yan'uwanta da kuma yan'uwan mahaifina kamar yadda sarkin ya fada.
Bayan ya gama jawabinsa ne aka sallami kowa, ni kuma sai na raba kusa da Mama na fada mata cewar Aliyu yana son na koma yau saboda Rahma bata da lafiya, ita kuma ta fadawa yayanta yayanta kuma ya samu Mai Martaba ya fada masa a take, Mai Martaba ya sa a bincika masa idan za'a samu jirgi da a yau, aka tabbatar masa da babu sai dai gobe, saboda haka dole Aliyu ya aje tafiyar har gobe.
A ranar aka kai ni gurin kakannina na bangaren uba, ganin cewar Aliyu zai tafi ba masanar ko ya dawo yanzu ko kuma sai nan da kwana biyu ko wani lokacin, su kansu ba za su jidadi ace ya tafi ba tare da sun ganshi ba, kuma za su iya daukar cewar saboda su suna takalawa ne, tare da Mama muka tafi da kuma wasu daga cikin yan gida, akwai tafiya mai nisa sosai tsakanin unguwar da Sarkin yake da kuma inda su suke. Ko da muka isa rana ta bude sosai a unguwar su har sun sauke sallah azahar. A hanyar mu ta zuwa ne na ke labartawa Aliyu jawabin da sarkin yai abubuwan daya fada, domin duka maganganun da yai da yaren buzanci yai shi wanda kuma Aliyu ba ji yake ba.
Sai da aka fadawan ta Mai Martaba ya hado mu da su suka shiga aka sanar sannan mu ka bi baya. Gidan kasa ne gaba daya gidan, sai dai irin ginin nan ne na mutanen da wanda ake na iyali da yawa, wanda zaka samu wani lokacin har da jikoki ma a gidan. A gidan muka wuni ni da Aliyu suna ta kiran mutane a zo a ganmu wai yar Ummaruje ce kamar yadda take fada, tsohuwar ko gani bata yi sosai Nene na ke jin suna kiranta, ta yi farinciki sosai da ganin mu kuma ta yi kuka ita da duka yan gidan jin cewar Baba ya rasu, ba su kadai ba ni kaina sai da nai kukan tunawa mutuwar tasa, yau ga ji a gaban iyayensa amman babu shi. Sai da dare muka baro gidan a can muka ci abincin rana da dare da za mu dawo aka tasa min nonon rakuma saboda an bani na sha na jidadi har na roka. Kallo daya za ka ma fuskokinsu ka fahimcin cewar suna cikin farinciki da jindadi ganinmu, ban yi zaton Aliyu zai sake jiki kamar yadda yai a yau ba, fuskarsa na nan a yadda take babu wani walwala sosai Murmushin ma ba komai yake ba, amman ya sake jiki ta hanyar cin abincin da aka kawo mana da har ma da Nonon ragumin wanda ya fada ai yana shansa a gidan Mama Fulani wani lokacin tana siye ta aje. Duk kuwa da kasancewar an aiko mana abincin daga masarautar suna ganin kamar ba za mu iya cin wannan ba, wani abincin ma na san saboda Aliyu aka girka shi irin tuwon shimkafa miyar Allayahu da akai da man shanu ga naman kaji da garo a ciki.
Ba tare muka dawo da Mama ba domin ita tana gama gaisawa da su ta dawo gida, wai bata son kowa da kowa ya zo ganta ta san ba zasu taba cire tabon abunda ta jawa musu na ja dansu su gudu ba, ballantana yanzu da ta kawo musu labarin mutuwarsa har a bada ba za su manta da ita ba, ba kuma za su yafe mata ba, duk wani so ko nuna mata kauna da za su yi ta ciki na ciki tana ganin kamar komai lafinta, saboda ita taje ta same shi da zancen guduwar kuma ya amince.
Na dawo ima jin kamar kar na baro na dawo nan ba, ba dan komai ba sai dan yadda tsarin gidan da kuma yadda suke haba haba da ni ya burgeni, har ta ginar gidan ana ta lekowa ana kallona, ba ma kamar lokacin da za mu tafi har da masu fitowa suna kallon motocin Mai Martaba.
A cikin unguwar na yi ta ganin zangon maza masu shan shayi da yar butarsu wasu sun yi gugun guri daya sun kuna kidan buzaye wasu kuma suna ta fira abunsu.
A lokacin da muka dawo gidan ma sai aka sake kawo mana wani abincin aka ni dai sai da na ci Aliyu ne kawai be ci ba saboda ya koshi, muna shirin kwanciya aka aiko kirana, har zan fita haka sai ya rike ni ya dauko min Hijab.
“Gidan nan har ya fi gidan mu yawan maza, bana son fitar ki haka Baby, kuma ya zama dole ki min alkawarin kula da kanki da jikinki da kuma babyna da yake cikin ki kamin na tafi pls”
“Taya mutum zai kula da kan shi? Da ma dai kula da wani ne ai zan iya”
Ya kama kunkuruna ya rike.
“Karki bar kanki da yunwa, ko kuma wani abun ya same ki, idan kin ji ciwo ko rashin lafiya ki yi saurin fada, kar ki bar jikinki haka nan sake har wani ya ga kyauki ko ya yaba, ki rika rufe jikinki kina tunawa cewar ke ajiyar wani ce”
Na gyada masa, sai ya sumbance ni sannan ya sake ni na fita. Bangaren da Mama take na nufo sai dai ban same ta a dakin dana same ta jiya ba sai wani dakin dabam,tana tare da mahaifiyarta da kuma wata mai kula da gidan da kuma wasu matan da aka nuna min dazun da safe aka ce matan yayyen mahaifiyata ne.
“Saboda tafiyar safe zai yi ya kamata ki fada mana abunda yake bukata sai saffara masa da wuri kamin ya tashi”
“Wa? Wai Aliyu? Okay bari na tambaye shi”
Duk kallona sukai har Mama dakanta kamar na yi wani sabo ko fadin maganar da ba daidai ba.
Sai Mama da sauran matan sukai murmushi.
“Ina ruwan Ataa”
Mama ta fada.
“Mu a nan ai ba a fadar sunan miji, miji yana da girma sosai, kuma akwai kunya ka fadi sunan miji kai tsaye, ina ma laifin ki ce masa Hamma”
Cewar Mama Hajjo. Sai a lokacin na gane dalilin kallon nawa da suke, ashe dan na fadi sunan Aliyu ne kai tsaye.
“Ga ki da sunan Maman su Mai Martaba amman ba ki iya girmama manya ba?”
Na yi kasa da kaina alamar kunya sannan na fice. Lokacin da na dawo dakin ya same shi rike da waya a hannu, ina shigowa ya dago kai yana kallona.
“Hamma wai ance mi kake so a maka da safe kamin ka tafi?”
Na yi maganar da sigar zolaya ina dariya tare da lake kafada kamar karamar yarinya. Murmushi yai ya miko min hannunsa.
“Zo nan matar Hamma”
Sai na saka dariya na zo gunsa kamar yadda ya bukata. Sai ya dora ni kafafuwansa.
“Wace ki ce min Hamma”
“Cewa akai wai ba a fadar sunan miji, shine aka ce ina laifin na kiraka Hamma”
Na fada ina dariya, sai shi ma yai dariya.
“Ke kuma na rika ce miki indo”
“Eh na yarda, fada min abunda kake so aka dafa maka da safe”
“No bana bukatar komai zan karya idan ya sauka can, akwai kayan tea a nan zan iya hadawa na sha ai”
Haka na koma na fada musu baya bukatar komai, sannan na dawo bangaren mu muka kwanta.
Washe gari.....