← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 143

Sashe 46

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Ba za ki bari ta gani ba ai, boyewa za mu yi ki rika sakawa cikin kayanki, idan mun tara da yawa idan za ki je ganin gida sai a kaita asibitin ko?”

“Mama...”

“Ya isa, komai dai Mama Fulani zan mata magana ta daina takura miki”

“Aa dan Allah ka rufa min asiri wallahi zata iya dukana ma”

“To karba ki aje, karki bari ta gani sai ki boye abun ki ai”

Babu yadda na iya bayan karba domin ni ma kaina na san ina da bukatar kudin, dan haka na saka hannu biyu na karba cikin tsoro da firgice har na manta ban masa godiya ba, shi ya fara fita cikin motar ya zagaya ya bude min ya fito sannan ya rufe motar, wani abun da ban sani ba ashe Aliyu yana tsaye bakin gate din yana kallonmu amman ni ban lura da shi ba har sai da na ga Kamal yai murmushi ya daga masa hannu.

“Sannu dai Aliyu”

Sannan na koma cikin motar yaja abarsa zuwa gaban gate din gidansu ya danna horn aka bude masa ya shige ciki. Ina tsaye a inda ya aje ni ina kallon Aliyu da ke tsaye daf da gate din yana watso min wani kallo mai ban tsoro fuskarsa a hade kamar bakin hadari, tsakanin jiya da yau Allah ya saka min tsoronsa duk wani fitsara da nake jin zan iya masa sai na ji yai min kwarjini har na gagara karasa gurin gate din na shiga shi kuma yai tsaye a gurin yana ta kallona kamar daman can dan kallo kawai aka halliccesa. Ganin ba zan zo ba yasa ya juya ya koma cikin gidan, yana wani irin taku na masu karfi da kuzari. Sai na tabbatar ya shige ciki sannan na nufi gate din na tura kofar na shiga, sai na ganshi tsaye da alama ni yake jiran na shigo ni kuma nai tsaye a gurin dayan hannuna da kudin dayan kuma da ledodin.

ALIYU POV.

Tun ya bar gidan Mama Fulani ya saka samun sukuni da walwala a yadda yake, zuciyarsa na ta raya masa Muhseen zai iya cutar da Ataa, ya san Muhseen ba dan iska ba ne, amman ai ba a shaidun mutum a yanzu, kuma yadda Ataa take da kyau zai iya rudarsa ya jefata cikin wani halin, wanda yake da tabbacin shine silar komai tun da shi ne silar cire kodar mahaifiyarta har ta zo aiki a gidan, idan kuma wani abun ya same ta ai duk shine sila, dan haka ba zai bari rayuwarta ta lalace ba, ba zai taba yarda ta rika kebewa daga ita sai Muhseen ba, daman can tsakanin shi da Muhseen basu taba shan inuwa daya ba, saboda Muhseen yana jin haushin yadda yake da jin da nuna isa da dakama, shi kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake da sakewa da mutane. Daga gidan Mama Fulani ya nufo gidansa cikin bacin rai, duk yadda yai kokarin ya kawar kar Rahma ta fahimci yana cikin damuwa sai ya kasa, in every minute sai ya ji kamar wani abun ne zai samu Ataa duk kuwa da yasan be barta mugun guri ba amman ya kasa natsuwa da zamanta a gidan tsakanin jiya zuwa yau.
Rahma kallonsa take har ya shigo cikin falon ya karaso kusa da ita ya zauna yana matsa kansa alamar yana masa ciwo.

“Lafiya dai, na dauka sai nine zaka dawo gida idan mun ga Doc Perry?”

Kissing dinta yai sannan na kwantar da kansa jikin kujerar ya lumshe ido na wani lokacin sai kuma ya ciro wayarsa yai danne danne ya tura mata. A take sakon ya shigo wayarta da sauri ta dauki wayar dake gefenta ta duba.

“Za mu iya bari zancen Doc Perry for now? Bana son zuwa gurinsa”

Kallonsa tai bayan ta gama karanta sakon.

“But why? Wata kila ma mafita ce ta zo mana, waya sani ko waraka ce”

Dagowa yai ya zauna daidai yana kallonta.

“Rahma akwai abunda ban taba fada miki ba, ban so wannan maganar ta fito daga bakina ba, amman ban san iya lokacin da zan yi ta aje ta ba”

Kara matsawa tai kusa da shi da maida hankalinta gurinsa tana kallonsa kunnuwanta cike da kwadayin jin ko mienene daman yau ta fahimci yana cikin damuwa.

“Minene Aliyu akwai wata matsala ne? Fada min”

Wani dogon numfashi yaja ya sauke ya shafa fuskarsa cikin yanayin da ke nuna yana cikin damuwa, daman kuma a cikinta yake.

“Rahma ban sani ba ko zaki fahimta, ban san yadda za ki kalli abun ba, kuma ban san yadda za ki kalleni ba”

Saurin kama hannunsa tai.

“Fada min kawai Aliyu minene matsalar?”

“Rahma duka tsawon lokacin da muka dauka matsalar daga ni ne..”

Da sauri ta rufe bakinta sai kuma ta girgiza masa kai hawaye na cika idonta.

“Ba daga kai bane Aliyu sun ce ba mu da matsalar komai ba daga kowa ba ne, suna cewa za mu iya haihuwa a duk lokacin da Allah ya kaddara”

“Na boye miki ne saboda bana son ki damu, amman maganar gaskiya matsalar daga ni ne, a duk inda muka je ina sakawa likitocin su ce mu duka ne bama da matsala amman serious matsalar daga ni ne”

“Aliyu ba haka ba ne... ”

Ya rika fuskarta.

“Haka ne, kin san ba zan boye miki komai ba, ba zan miki karya ba, be kamata na kyale ki ki yi ta wahala akan abunda daga ni ne ba, na san idan muka je gurin Doc Perry dole zai fadi gaskiya domin shi baya karya”

“Duka shekarun nan da muka dauka da gaske matsalar daga kai ne? Ko kuma daga ni ne kake boye min?”

“Daga ni ne”

Hawaye ne ya sauko mata sai ta kwantar da kanta jikinsa.

“Miye amfanin fada min a yanzu Aliyu? Miyasa ba ka cigaba da boyen sirrin ba?”

“Saboda bana son ki yi ta wahalar da kanki akan abunda na san ni ne silarsa”

Rumgume shi tai ta fashe da kuka.

“Ba amfanin bayyanawa Aliyu, kai na ke so ba abunda ban gani ba, jin wannan kuma ba zai hana mu cigaba da neman haihuwar ba, wata kila gaba mu dace ba mu san inda rabo yake ba, da matsalar daga kai ne wata kila zan mu iya dacewa ka samu waraka”

Shafa kanta yai yana kara janta a kirjinsa ita kuma ta fashe da kuka mai tsanani har ya rasa ta ita zai fara rarrashinta. A haka suka kwana tana ta kuka, wanda yake tunanin wata kila da yace matsalar daga ita ne wata kila ma ba zata damu kamar yadda ta damu haka ba.“Kamal dai soja abokinka?”

Nasir ya fada cikin tsananin mamaki, Aliyu be ce masa komai ba, daman kuma ya san ba zai amsa basa ba, sai dai tunda yaji yai shiru ya san cewar Kamal din ne.

“Ina ya hadu da ita?”

Nasir ya sake tambaya, sai Aliyu ya fito daga gurin ya nufi kofa rai a bace, cikin sauri Nasir ya ce

“Aliyu ina za aka je?”

“Na zuba musu ido su lalata mata rayuwa?”

“Kana da tabbacin bata nata rayuwa za su yi? Daga Kamal har Muhseen ba irin samarin nan ba ne”

“Bana iya shaidar kowa sai kaina, idan ban taka musu burkiba lalata mata rayuwa za su yi, akan mi zai dauke ta ya fita da ita? Waya bashi izinin ma?”

“Ai ba yau aka saba ba, dan mace ta kebe da wanda ba muharraminta ba ba wani abun ba ne, naga gidanka ma namiji ne yake muku girki ya gyara gidan”

“Nasir baka da hankali kai ma, Rahma ai babba ce ta san ciwon kanta, ba zata bari wani ya yaudareta ba, wannan kuma karamar yarinya ce tunaninta be kai can ba”

Yana fadar hakan ya saka katinsa kofar ta bude masa ta fice. Nasir ya bishi da kallo yana murmushi.

“Aliyu kenan, at least dai yarinyar nan ta sa ka fara motsi kamar na miji, sai yanzu kasan da muharramin?”

Ya fada yana cigaba da murmushin tare da zaunawa saman kujera ya cigaba da aikinsa.
Kai tsaye gida ya nufa gudu yake amman yana jin tafiyar ta masa nisa yau, a kada horn daya yake danna amman daya bisa bakin gate din sai da ya danna horn ya fi hudu a lokaci daya, har mai gadi sai da ya ji tsoro yai tunanin ko wani abun ne ya faru. Daf da kofar falon ya faka motarsa ya fito cikin zafin ran da be san ta ina yake fito masa ba ya shiga cikin falon ba ko sallama, Rukaiya ya samu kwance a kujerar tana lasar waya tana dariya da alama chat din ya mata dadi.

“Ke ina Ataa”

A firgice ta tashi zaune domin hankalinta yana kan wayar bata ma san da shigowarsa ba.

“Na'am tana, tare muka fita shopping shine sai Kamal ya ce na bashi aron ta ta taya shi shopping idan suka gama zai kawo ta gida”

“You're very stupid”

Ya fada yana kara matsawa kusa da ita cikin wani irin yanayin bacin rai marar misaltuwa, tana ganin hakan ta tashi da gudu ta nufi upstairs tana kiran sunan Mama Fulani, ta san baya dukansu ko ba su ba abu ne mai wahala ya saka hannunsa ya daki mace amman a yadda ta ga bacin rai a fuskarsa a yau ta san komai zai iya faruwa. Da sauri Mama Fulani ta fito daga dakinta dankwalinta a hannu yana tambayar ba'asi. Cikin kuka Rukaiya ke fada mata abunda ya faru sai ta nufi downstairs tana kallon Aliyu tare da fadin.

“Ta fada min ai, Kamal ne ya ce a ara masa ita”

“Ya za ara masa ita kamar wata sutura, idan wani abun ya same ta fa? And you.... ”

Ya fada yana nuna Rukaiya sai kuma ya juya ya fice sai huci yake kamar wanda yai gudun ceton rai. Mama Fulani ta saki baki tana kallon ikon Allah.

“Wannan yarinyar ta zama fitini ta zo ta koma garinsu ba zata zauna a gidan nan ba, gaba daya Aliyu ya canja ganin yarinyar nan, shi da babu ruwansa da kula da mace? Ji abunda yake?”

“Ba sai an koreta ba Mama, Wallahi kamaninta za mu canja, kyau ne yake rudarsu”
Chapter 46 · 0% Book details