← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 135 OF 143

Sashe 135

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da akai aka gama karbar gaisuwa sannan Mama Fulani da Ammy suka koma Abuja tare da Abbah daman shi Muhseen kwana biyu kawai yai ya koma saboda yanayin aikinsa. Nasir ma da matarsa sai da suka kara kwana daya saboda Aliyu sannan suka wuce. Aliyu da kansa ya raka su har airport lokacin da za su tafi, Nasir yayi ta bashi hakuri da kuma kalaman da za su karfafa masa guiwa su akan rashin Rahma.
  After ya raka su ya dawo gidan Momy duk ya zama wani silent kamar ba shi ba, lokaci lokaci Rahma take fado masa a rai, idan ya tuna cewar be cutar da ita a zamantakewar su da aure ba sai ransa yai fari tas domin babban abunda yake gudu a rayuwarsa zalintar wani ko danne masa hakki da ikonsa, and wani abun godiya ga Allah da Allah ya saka ba Ataa ce ya rasa a yanzu ba, domin da ita ta tafi a yanzu maimakon Rahma wata kila da zai fi shiga damuwa sosai fiye da Mutuwar Rahma, duk wani abu da yake game da Rahma sabo ne kawai da kuma tuna irin rayuwar da akai ko makinyin ka ne ya rasu sai ka ji babu dadi balle kuma matarka, yana yawan ayyanawa kansa wata rana zai mutu Rahma ma zata mutu saboda matsalarta tun daga kan cire mata koda da akai na farko da ta biyun ta lalace aka canjin mata wata da ta mahaifiyar Ataa ta zo ta kone abun ya soma ba shi tsoro. Wata kila ta kone ne saboda Allah ya nuna musu ikonsa akan abunda suka aikata sai dai hakan be zame ma Rahma da iyayenta ishara sai ma kokarin aikata wani suke, yanzu kuma da mahaifiyarta zata bata nata sai Allah ya gwada musu ikonsa ya karbe abarsa a lokacin da suke tsananin bukatarta kuma babu yadda suka iya da ikon Allah. Yar da suke kishi da fada akanta mai abu ya karbi abarsa kuma ya maida wacce suke kishin da ita asaman su sai kuma ya?

ATAA POV.

kamar yadda Momy ta fada min ina kokarin ganin Hamma ya ci abinci ko da ba da yawa ba, kamar yadda ni ma yake tsare ni na tisani a gaba dole sai na ci na koshi a cikin satin sai ya zama ni da shi muna bawa junanmu kuwawa ta musamman da kuma ganin tausayin junanmu, yana ganin tausayin cikin da na ke dauke da shi da kuma tausayi Rahma sai ya dawo kaina ni kadai daman can kuma ga kaunata a ransa, yadda yake tallalina kana ganin abunda yake min kamar mai tsoron ya rasa ni ne, ni kuma tausayinsa ya cika raina sosai na rashin Rahma da yai da kuma yadda baya iya bawa kansa kulawa ta musamman amman yana kokarin kula da ni. Wanda ya rasu shi ya tafi babu abunda za a canja daga rayuwar wani ko kuma duniya gaba daya, daga lokacin da rayuwarka ta yanke shikenan kai na manta da ka taba wanzuwa a wata duniyar ma, kana ciki kabarinka kana fuskarta abunda ka aikata idan alheri ka fara gani idan kuma akasin hakan ne shi ma zaka gani. Na karu da abubuwa da dama a mutuwar Rahma a ciki akwai na tunatar da ni cewar saboda na samu jindadi da kwanaciyar hankali a yanzu ba shi yake nufin mutuwa ta manta da ni ko kuma ni na manta da ita. Abu na biyu kuma na yarda wanda ya mutu shi ya mutu duk kuwa irin son da ake masa, domin Hamma ya dan fara sakewa ba kamar da ba, daman kuma ai ba zai dawwama a cikin bakincikin mutuwarta ba kamar yadda take tsammani saboda Allah ya musanya masa da ni, wata kila da ace ta tafi a lokacin da be aure ni da zai fi shiga damuwa sosai, a kokarinsa na faranta da saka ni nishadi ni da abunda yake cikima kamar yadda yake fada, sai shi ma ya saka kansa ba tare da ya sani ba, ban ayyanawa a raina cewar wata rana Hamma zai so ni kamar haka ba, kuma zan rayu a gidansa daga ni sai shi sa abunda zan haifa inda da rai da rabo.
  Kusan kullum ina waya da Nana wacce na ke kira da Mama a yanzu saboda canjin da Hamma yai min tama tambayar lafiyata da ta Hamma na fada mata muna nan lafiya, har take fada min akwai yan'uwa da yawa da ban gani ba sai idan komai ya laba na dawo, ni dai sai dai na amsa da to amman na san yadda Hamma yake daukin cikin nan da ni ba zai iya barin nai nisa da shi ba, idan muna gida a jikinsa na ke wuni idan kuma mum taho gurin Momy idonsa na kaina da na yi wani abun da ba daidai ba sai yi kin alama da ido. Momy ma tana kula da ni har zaman da ke kusa da kofa sai ta fada min wai mai ciko bata zama a bakin kofar dakin ko kusa da kofa aaboda aljanu, ni dai abun har dariya ya ba ni sai dai ban yi a gabanta ba, ni dai ban taba jin haka ba wata kila saboda ban zauna da tsofi ba ko kuma ban yawance akan irin waennan abubuwa, wata kila kuma saboda suna son cikin ne suke ganin komai be dace nai yi ba. Shi kanshi Hamma da safe sai ya min addu'a har a cikin haka ma da dare idan zan kwanta. A ranar da muka wuni idan Momy take masa maganar karatuna sai ya nuna mata baya so.

“Momy ga ciki kuma ace tai karatu? Haba abun ai sai yai dawo, da karatunta zan ji ko cikin?”

“Wai dan wajen Fulani kanka farau ciki ne? Karatu ko na islamiya sai ta fara da shi a yanzu, saboda kula da kanta da addu'oi, ai ilmin mace yana da muhimmanci ba wai ko dan aiki ba, saboda kula da yayanka ma ta koya mu su, kuma idan babu ilmi tarbiyar ma ya kake tunanin za ayi ta? Miyasa ake son auren mace mai ilmi ba dan wannan ba”

“Momy ki ma kinsan dan wajen Fulani da Mama Fulani komai na su dabam ne, gaskiya ni ba zan iya daukar wannan ba, ke ma fa Momy kin san yadda ake bukatar abun nan yanzu kuma ki kawo wasu maganganu haba dai Momy”

“Haba dai? Yanzu kana ganin idan a gurin Kakanta take kuma ya samu labarin bata iya komai ba batai karatu ba zai zuba mata ido haka? Yanzu ka fi son tai ta zaman banza a wata bakwai ko takwas da ke tafi wanda za tai nan gaba? Ai ya kamata ka saka ta ilslamiya ko kuma na nemo malamin da zai rika karantar da ita a gida, in so shi bokon idan ta haihu sai ta yi, baka sani ba ma ko tana da burin yin wani abu da karatunta”

Momy na fadin hakan ni kuma nai karaf na ce.

“Eh ina son nai likita ko nurse abun na burge ni sosai Wallahi”

Harara ya watso min.

“Eh ba ri ki sake magana na buge miki ba ki a nan, haka nan za ki je ki yi karatun likita shekara nawa tare da maza?”

“Ai ansan ina da aure kuma zan rika saka hijab har da niqab ma”

“Ba za ki yi shirun ba? Ba ki san kyaunki hadari ne ba, kuma ba ki da wayo da za ki iya tattalin abunki balle har ki kare martabarki, ni ko ko tafin kafarki aka kalla aka yaba Wallahi zafi zan ji”

“Allah ya sauwake maka wannan bakin kishin daya cika maka zuciya, amman karatu kan dole ne tai yarinya ba za tai zama haka ba, kai ma da yarka ce ai ba zaka barta haka ba”

“Momy za tai karatu, karatuna yana cikin burin da na ke da shi akan Ayusher amman sai ta haihu ta yaye abunda ta haifa ya yi kwari sannan a fara maganar karatun shi ma idan bata samu wani cikin ba”

“Yanzu a maimakon zaman da za tai ai sai ka sakata ta fara daga matakin farko kamin ta haihu dan yai kwari ta san wani abu ka ga ci gaba kawai za tai”

“Momy mun ma kusa barin garin nan Abuja za mu koma”

“Ai a Abujar na ke nufin ka saka ta ba a nan ba, daman can sun fi makarantu masu kyau ai”

Na jidadi sosai da Momy ta tunatar da shi burina da kuma abunda na ke ta mafarkin samu shekaru da yawa, domin na ga kamar shi ya manta idan ma be manta ba to yana son shashantar da abun saboda kar dansa ko yarsa su wahala. Ni ko ban ga abun wahala a ciki ba domin bana jin komai ko aman da nake na dade ban yi ba sai dai yawan cin abinci da na ke sosai kuma akai akai.

“Shikenan Momy daman can na san ai ba ke ce Mama na ba, shiyasa ba ki goyon baya na, da Mama tana nan da yanzu ta saka baki ta tsaya min”

“Daman can ai kai ba dan ba ne, balle kuma yanzu da na samu yata ta, ga su Husna da Amina da Siyama sun ishe ni ga kuma Muhseen a gafe”

“Na kusa komawa gurin Mahaifiyarta na barki da su”

“Ai da ma kabar ta nan ta yi karatu ta koyi abubuwa da yawa kamin nan”

Dariya yai dan yana jin kamar ba da gaske Momy take ba, ni dai na yi yar dariya dan san Momy ta fada masa abunda ba zai iya ba ne.

“Tashi mu je gida”

Ya fada har lokacin be daina dariya ba, ita kanta Momy dariyar take dan ta san abunda ta fada ba mai yiyuwa ba ne a gurin Hamma. Muna shirin barin gidan kiran Wayar Mama ya shigo wayata da zumudi na daga na kara a kunne, ba ma kamar da ta fada min cewar gobe zata zo sai da n daka tsalle na dire saboda murna da yaren buzanci na ce.

“Haka nan kawai za ki zo Mama?”
Chapter 135 · 0% Book details