← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 69 OF 143

Sashe 69

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya kai minti biyar zuwa bakwai kamin ya amsa ni har na dauka ba zai amsa ni ba.

“Idan na barki kika kwana a nan wani abun ya same ni kuma ni za ki dorawa laifin ai, kin fita ba ki fadawa kowa inda za ki ba”

Ya fada still be kalleni ba.

“Sa gaske kwana kai kana gadina? Da gaske gadina kai?”

Sai a lokacin ya kalleni be ce min komai ba ya faka motarsa gaban wani masallaci sai da ba kusa da shi sosai ba ya fita daga cikin motar ya bar wayarsa a nan. Ajiyar zuciya na sauke har yanzu na kasa daina mamaki ina ganin kamar ba gaske ba, maganganun Doc Bukar nata dawo min akai. Ni dai ina zaune a gurin har yai sallah ya fito ya dawo cikin motar, ashe ma daga masallacin zuwa gidan Momy babu nisa sosai domin tafiya kadan yai muka iso bakin gate din gidan.Sau daya ya danna horn sai kuma ya kalli inda na ke har lokacin kallonsa nake kallon mamaki da tunani.

“Bana son kallo na sha fada miki”

Dauke kaina nai daga barin kallonsa na maida idona gurin yatsun hannuna da nake juyawa cikim dayan hannun, har aka bude gate din jikina be daina ba ni cewar idonsa na kaina ba, mistakenly na dago kaina sai muka ido kallona yake sosai kamar mai son ganin wani abu a fuskata saurin maida kaina nai kasa sai aka bude mana gate din sai a lokacin ya dauke kansa daga gareni ya tuka motar ya shiga ciki, daf da kofar falon ya faka motarsa ban jira ya bani umarni ba na bude na fito kamar yadda na ga ya fito, yana gaba ina binsa a baya a hankali har muka isa gurin kofarz jikina nata kamshin turarensa daya cika motar. Knocked yai sau daya be sake yi ba har na wani lokaci sannan na ga ya dora wayarsa a kunne.

“Zo ki bude mana kofar falo”

Ko minti biyu be yi da sauke wayar ba Amina ta bude mana kofar falon, a maimaikon ya fara shiga sai ya tsaya kallona da ido ba zai iya cewa na wuce ba sai dai so yake na fara shiga kamin shi. Ina ganin hakan na wuce ciki sannan shi ma ya shigo daya saka wayarsa aljihu.

“Shiga da ita ciki tai sallah”

Wani kallo Amina tai min kamin ta sake kallon Aliyu tai saurin dauke kai.

“Zo muje”

Ta fada tana nufar upstairs. Kallonsa nai na ga ni yake kallo sannan na dauke kaina na bi bayan Amina. Dakinta ta kai ni ta nuna min bandaki na shiga na yi alwala ko da na fito har ta shimfida da min carpet da Hijab dina nai sallah sannan na mike tsaye da zimmar fita daga dakin zuwa kasa sai na ji ta ce.

“Ya ce wai ki kwanta ki huta”Saman gadon ta na hau kamar yadda ta nuna min na lulluba da bargo mai laushi ya lumshe idona ba dan bachi ba, sai dan tunanin kwanan da Aliyu yai yana gadina wai har yana tsoron kar wani abun ya same ni, abunda wani mutum be taba min ba, babu ruwan kowa da inda zan kwanta ko da ko gurin mai cutarwa ne balle har ayi gadina idan ba mahaifiyarta ba, amman a karon farko wani ya yi gadina kuma yana tsoron wani abun ya same ni, wanin ma Aliyu mutum mai girman kai da ji da kai mai kyamar talaka, idan har na boye na ce ban jidadin abunda yai min hakika na yaudari kaina. Unkurawa nai na sauka daga kan gadon na nufi kofa na fita daga dakin daman Amina ta fita daga dakin tun bayan data fada min sakonsa. Tun da na fara takawa zan sauko downstairs ya dago daga zaune da yake samanb kujera yana kallona har ya sauko.

“Ina son naje gurin Nana”

“Koma ki kwanta sai idan za a kai abinci za a wuce da ke”

Ya fada fuskarsa babu alamar wasa, juyawa nai na dawo dakin na sake haye gadon na kwanta, amman bachi ya ki daukata har rana ta bullo, ba dan komai ba sai dan tunanin abunda Aliyu yai a yau da kuma son ganin Nana da zuciyata ta kwadaitu da shi. Ji nai an turo kofar dakin an shigo hakan yasa na bude kaina daga cikin bargon ina kallon Amina data shigo rike da brush ta mika min.

“Ki shiga bathroom din nan akwai man goge baki ki zuba a kai ki wanke bakinki kuma ki yi wanka”

Har ta fadi hakan sai kuma ta nufi bathroom din tana fadin.

“Bari dai na hada miki ruwan wanka”

Bayan wani lokaci ta fito tana rike da brush din a profile zuba mai akai ta mika min.

“Idan kin yi wanka ki dauro tawul ki fito karki maida kayan za a kawo miki wasu tufafin”

“To na gode”Na fada ina nufar bandakin, wanke bakin na fara yi sannan nai wanka da ruwan data hada min da kuma sabulu mao tsada na dauki tawul din da na gani rataye na daura sai ya tsaya min iya jinyoyina. Haka na fito daga bandakin na samu gafen gado na zauna, bana son na taba wani abu ta zo ta ga na mata ba daidai ba, na fin son sai idan ta zo ta fada min man da zan shafa. Ina zaune ina kallon yatsun kafata masu tsawo kuma sirara na ji an bude kofar dakin na yi zaton Amina ce sai na ga Muhseen yana rike da wayarsa. daga can bakin kofar da yake ya tsaya yana kallona tun daga kaina har zuwa kafafuwana, daman rabin cinyata a waje suke. Ba zan iya fassara mana'anar kallonsa ba, domin a yadda na ke makaskanciya ban yi zaton wani mutum mai daraja dan masu daraja wato nera zai min kallon sha'awa ba, balle har yai tunanin yi min wani abu, sai dai yaba kyauwo na wannan na san wani abu ne da ba ko wane namiji ne zai iya rike bakinsa daga furtawa ba, sai miskilin mutum kamar Aliyu wanda nake ganin kamar ba shi be taba ganin kyau nawa ba domin be taba yaba wa ko nuna zai yaba din ba, kallon ma da yake min ina jin kamar na kurilla ne dan kawai nai magana ko kuma na tsargu. Ya dade yana kallona kamin ya karaso kusa da ni yana ta yawo da idonsa a kan surar jikina. Tsarguwa na soma yi irin tsarguwar nan ta jin haushi idan wani na kallonka tsabanin Aliyu da bana jin haka, ga kuma kallon da yai min lokacin da nake canja tufafi da lokacin da nake wanka, sai na soma jin ba dadi duk kuwa da kasancewar kallon mace ko tana jikinta a gurina ba wani abu bane, domin kuwa da wani babban abu ne da Nana ta zaunar da ni da fada min a matsayinta na mahaifiyata.

“Na rantse da Allah kina da matsifar kyau Ataa, look at you karamar yarinya da ke amman Allah ya miki sutura komai ya ji”

Ya fada yana kokarin zama kusa da ni sosai yana kallon kirjina da fuskata.Na sani kyau na daga cikin abunda yake burge Muhseen ba tun yau ba tun a lokacin da ya taba ganina a gidansu da sunan aiki ya umarce mahaifiyarsa cewar a zabe ni saboda kyau, sai da yadda yake koda kyau nawa har mamaki yake ba ni domin shi ma yana da na shi kyau daidai gwargwado.

“Ataa....”

Sunana kawai ya fira be fadi abunda yake da niya ba, sanadin shigowar da Aliyu yai dakin hannunsa rike da mug fuskarsa babu annuri yake kallona da kuma Muhseen.

“Wai kai baka jin kunyar kanka? Ka shigo cikin daki ka kebe da yarinya kamar wannan kuma da tawul kawai a jikinta? Ji yadda ka zauna jikinka na kusan taba nata”

Muhseen yayi murmushi yana mikewa tsaye.

“Ina ce yanzu nan Amina ta fada min cewar kai ka kawo ta, waya san inda ka fito da ita? Kai da ba a zarge ka ba? Kao kullum na zaka kyautatawa mutane za to ba? Ka dinga min abu kamar baka san inda na fito ba? Ko kuma mai mim fatar sheri? To yanzu muka fara tsakanina da kai Aliyu dan kana son ta be isa ya hana ni sonta ba, kai ma din ban san kalar son da kake mata ba”

Yana fadar hakan ya fice cikin bacin rai. Aliyu kuma ya nufo inda nake zaune ciki ba fada.

“Wai ke baki san haramun ne mutumen da ba muharramin ka ba ya kebe da kai?”

“Be min komai ba”

“Oh sai ya miki komai ne zai zama matsala? Kallon jikinki ko taba jikinki shi duk ba matsala ba ce? Ba ki tana sani ba?”Na gyada kai alamar ban sani ba din.

“Wace makarantar islamiya kika yi?”

“Bama zuwa makaranta saboda bara”

Na amsa masa ina dan turo baki kamar an min wani abu. Kallona ya rika yi irin kallon nan na mamaki jin furucina.

“To haramun kallon jikin mace da ba muharramar ka ba, kin san abunda ake nufi da muharrami ma?”

Na sake girgiza kai alamar ban sani ba.

“Kina cikin matsala”

Na fada yana juyawa sai kuma ya juyo ya ya nuna ni da tsaya.

“Kar na sake ganin kin zauna kusa da wani namiji, kar ki sake sakin jikinki har wani namijin ya gani ko da ni ne ko wani can dabam kuma ki kama kanki bana son yadda kike sakewa da kowa”

“To”

Na fada ina gyara daurin tawul din a kirjina sai ya matsa kusa da ni ya miko min mug din hannunsa.

“Ki shanye yanzu za ku tafi asibiti”

Hannu biyu na saka na karba garin karbar hannuna ya taba na shi.

“Kar hannunki ya sake taba nawa idan za ki karbi abu, kar kuma ya sake taba na kowa”

Yana fadar hakan ya juya ya fice daga dakin. Ni dai ban da binsa da kallon babu abunda nai yi.

ALIYU POV.
Chapter 69 · 0% Book details