← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 27 OF 143

Sashe 27

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na fada ina sakar mata murmushi. Sannan na tashi naje na waje na dauko duka kayanmu tare da Farida na dawo da su dakinmu, ni da Farida muke ta zagin masu kudi da irin wulakancinsu, Mahaifiyarta kuma nata shigar musu wai idan ban musu wani abun ba ai ba za su zo har cikin gida su mana haka ba. Ni dai ban ce da ita komai ba, ni da Nana muna ta jiran tsammanin idan mahaifin Farida ya dawo ya kore mu ya ce mu bar masa gida, amman be kore mu, kirana kawai yai ya tambayi ba'asi sannan yai min jan kunne akan gaba kar na yarda irin hakan ta kara faruwa, na jidadin yadda yai mana daman sanin darajar talaka sai talaka dan'uwansa, ko da yake wasu talakawan ma basu san darajar talakan dan'uwansu ba kamar Maman Farida.
A daren taliya na dafa mana, muka ci ni da Nana sai da muka koshi nas sannan muka kwanta bayan mun kashe kyandir din dake haska mana dakin duk dare, yau ma kamar yadda na sabawa kaima da tashi da wuri na tashi sai dai bayan na yi sallah asuba na koma na kwanta tun da bana aikin komai kuma ina da bukatar bachi. Ko da na farka ranata fito ko'ina kusan duk wani abun da ake saidawa na kari kama daga koko ko waina sun kare a lokacin sai dai na yamma idan anyi, dan haka na dimama sauran taliyar da muka raga ni da Nana jiya mu ka sake cinta da safe. Sannan na shiga nai wanka na fito na shirya cikin yadinmu na gado na rufe kaina kamar yadda muka saba yi idan zamu je bara, wannan karon har da gashin kaina na saki ya sauko har gurin mazaunaina, sannan na dauki dubu daya a cikin yan kudi da suka rage mana dan na siyo takalmin zuwa Abuja domin takalmina sun cinye daga kasa.

“Ki siyo mana tuwon ruwa daga can (bula) da kuli da zogale sai mu yi kwado”

“To Nana sai na dawo”

Na amsa ina saka kafata na bar gidan, misalin sha biyu na rana na kama hanyar kasuwar yar murna, domin bana son zuwa tsohuwar kasuwa ko sabowa saboda cinkoson mutane, alhalin ba wani abun kirki zan siya ba, a kafa na tafi duk kuwa da irin nisan da ake akwai amman ina jin kamar hasara ne na biya kudin achaba bayan muma muna da bukatarsu, kara dai idan zan dawo sai na hawo achaba ko Napep na dawo shi ma idan na rago canji.

Abun ka da wanda ya so tafiyar kafa, kuma gwanim tafiyar nan da nan na isa kasuwar murna, wata karamar kasuwa ce wance za a iya kiranta da unguwa ma domin mutane da yawa suna da gidaje a cikin kasuwar ba kamar sauran kasuwani ba. Daga bakim titi ma tsaya na siye takami na roba sai da natsaya na gwada wandanda suke yi ma kafata sannan na biya kudin dari shida da hansi, murna ta cika min zuciya domim rabon da na saka talkami mai tsada kamar haka har na manta duk talkamin da zaka gani a kafata ko dai an bani ne ko kuwa wasu sun gaji da amfani da su ne sun jefar na tsinta na gyara ina sakawa, kusan ma sai na ce ko a lokacin sallah da ake siyayya ni ba asiya min sabon kaya ba balle wani sabon takalmi. Bayan na bashi kudin na shiga cikin kasuwar na siyo abunda Inna ta aike ni sannan na fito na tsaya titi jikin wata mota ina jiran wasu motocin su gama wuce saina tsallaka na koma ta dayan bangare na hau Napep da naira hansin din da suka rage min. Ina kokarin tsallakawa wata motar na kokarin parking kusa da wance na ke tsaye sai ji nai motar ta ture ni da karfi har sai da na fadi zaune. Lambar motar kawai na kalla na gane cewar mutumenan mijin matar nan, wani abun isa yaga ya kade mutum amman ba zai iya fitowa ya duba waya kade ba, waya sani ko da gangan ya kade ni. Unkura nai na tashi na nufi inda yake na daki gilashin motar da karfi sai ya sauke gilashin yana kallona da cat eyes dinsa.

“Me na maka za ka kade ni? So kake ka kashe ni? Wulakancin da ka tura aka mana a gida be wadatar da kai ba, sai ka kade ni? Kai wa wane irin mutum ne? Kana son matar ka kasa cire kodarka ka bata sai da kasa a zalince mu aka cire aka dasa mata, kuma yanzu dan tsabar zalinci na yi magana shine zaka aiko har gida a ci mana mutunci a wulakanta mu? Hakan bw maka ba yanzu kuma ka ganni zaka nemi wulakanta ni?”

“Ba a nuna ni da yatsa”

Shine kawai abunda ya fada yana hakimce cikin motarsa yana kallona ido cikin ido kamar ba da shi na ke masifar ba, ba dan cewar na ji maganar ba da sai na rantse ba daga bakinsa ta fito ba. Ni sai a yanzu na lura da cewar na nuna shi da yatsa din ma, a maimakon daya sai na saka yatsuna biyu na nuna shi da su.

“Saboda kana wa? Mai arziki? Mai arzikin da ba zai iya zuwa gida da ko naira ba? Mai arzikin da bai iya komai da duniyarsa ba sai zalinci? An nuna ka ka yanka ma idan ka iya, bana tsoronka kai da muguwar matarka da mugun likitan nan, babu tsoronku babu kaunarku ko kadan a zuciyata”

Ina gama fadar hakan na tofa masa yawu a motarsa na koma inda nake tsaye, na tsallaka titi ina ganinsa yana ta kallona har na tari achaba na na hau, shi da mutanen da suka fahimci fadanmu. Sam babu tsoronsu yanzu a zuciyarta ko kadan, sai ma tsanarsu da nai har na isa gida zuciyata zafi take saboda bacin rai. Sai dai ban fadawa Nana ba, kuma ban nuna mata cewar wani abun ya faru ba, ina shiga na shirya mana tuwon ruwan na gyara zogale na kwada mana muka ci, sannan na cigaba da shirye shiyena a yar ghana must go dita da na siyo sabowa.
Bayan sallah isha'i muka kwanta ni da Nana, sai da na tabbatar ta yi bachi sannan na taso na baro mata dakin na zauna a tsakar gida cikin farin wata ina ta kallo taurari kamar mai kirgasu, tunani a zuciyata lallai ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da mahaifiyata. Kukana nai ni kadai babu mai bani hakuri har nai na gama sannan na wanke fuskata na koma dakin na kwanta amman bachi ya kasa daukata, sai na juyo da fuskata kusa da ta Nana ina ta kallonta kamar ance idan na tafi ba zan dawo ba.

Tun kiran sallah fari na farka, domin maman salma ta fada cewar da na yi sallah asuba na zo mu kama hanya, ina sallah Nana na kuka har nai na gama, ina cikin yin addu'a aka buga kofar gidansu Farida na san ba zai wuce Maman Salma ba, a nan ni ma na fashe da kuka na kama hannayen Nana na rike ina ta shafasu a fuskata, Farida ta shigo dakin ta dafa ni tana ba ni hakuri. Sai na juyo na kalleta.

“Ga Amanar Nana nan na baki, ki kula min da ita iya gwargwadon ikonki, ki yi mana gwargwadon abunda za ki iya, kin sani Farida ba dan talauci ba babu abunda zai nisanta ni da ita, tana da bukatata amman dole na tafi na nemo kudi. Dan Allah ki kula min da ita”

“Na miki alkwari Ataa zan kula da Nana In-Sha-Allah”

Na rumgume ta ina kuka kamar yadda ita ma take, sai kuma na sake ta ka saka hannayena na kama kafar Nana ina Shafawa.

“Na yafe miki Ataa na yafe miki duk abunda ke tsakanina da ke, tashi kije Allah ya tsare ya kai ku lafiya”

“Amin”

Na fada sannan na mike tsaye ina kuka sosai na fito nai ma mamar Farida sallama da mahaifinta na karasa gurin Maman Salma sai wacce ke tsaye tana jirana, sau biyu ina waigowa ina kallon kofar dakin da Nana take, ina ta jin kamar kar na tafi na barta amman tafiyar ta zame min dole. Gidan Maman salma muka koma ta dauki kayanta a nan na gane cewar ba ni kadai zata kai ba, domin tare da yan mata shida muka kama hanyar Abuja bayan direba ya zo har gida ya same mu, da alama direbanta ne sun saba da juna ita da shi.
Tafiya mukai ta yi, tun ina hawayen rabuwa da Nana har na soma wayewa, tafiyar ta fara ci min rai, a zariya muka tsaya muka karya sannan muka cigaba da tafiya mai isa, a takaice ba mu isa Abuja ba sai cikin dare...

ALIYU POV.

Yana rike da jarida a hannunsa amman ya kasa karanta komai, abunda Ataa ya fada masa jiya kawai yake tunani, wani be taba karfin halin fada masa magana mai zafi kamar ta jiya da Ataa ta fada masa ba, beside shi be san ya tura kowa gidansu ba, be ma san inda gidansu yake ba, and kadewar da yai mata ma bada gangan yai ba. Sai dai ko ba komai yadda take ta karfi hali ta burge shi, and yana da right din yi mata excuse tun da Azzalumi take ganinsa, kuma zalintarta akai? But waya tura wasu gidansu? Ko Doc Asim ne kamar yadda Momy take masa hasashen cewar zai iya cutar da ita? Ko kuwa mahaifin Rahma ne wanda shi ma yasan ba a zai kyale ba? Ko dai wanene he need to know ta dalilinsaba zai yarda sake zalintar kowa ba. Zaman da Rahma yai kusa da shi yasa shi dagowa daga dogon tunanin da yake ya kalleta yana kai hannu ya shafa gefen kafadarta.

“Dear na gaji da garin nan, bana son mu sake neman wata mai aikin wani abun ya faru, kuma gidan nan zamansa da datti ni bana so kyankyami na ke ji”

Be ce mata komai ba, daman can ta san ba zai ce ba.

“Ni mu koma Abuja kawai tun a can komai yi mana ake”

Ya aje jaridar hannunsa ya janyota jikinsa.
Chapter 27 · 0% Book details