← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 125 OF 143

Sashe 125

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Bayan mun gama ya kai plate din a kitchen, ni kuma na nufo dakin domin a falo muka ci abincin indomie. Bathroom na shiga na yi fitsari ko da na fito yana rike da wayarsa da alama kira yake ko kuma karanta sako domin screen din wayar kawai yake kallo na tsawon lokaci sannan ya aje wayar ya zo bayana ya kwanta.
Washe gari da wuri na tashi fiye da ko yaushe saboda marmarin tafiyar da za mu yi, Aliyu ne ya hada mana abun karyawa muka karya tare a dinning sannan na shiga bathroom din dakina nai wanka, na saka farin material marar nauyi kamar yadda ya umarce ni, na saka sarka da abun hannu na manta rabon da nai kwallaiya da sarka tun ina karama a lokacin da Mahaifina yake raya ya siya min wata sarka a lokacin karamar sallah, sai kuma lokacin bikina da aka min kwaliya aka saka min sarka, sai kuma yau wani kwarji da kyau sarkar ta kara min kasancewar mai tsada har wani haske ba, kumatuna ya dan kumboro kamar ba nawa ba, mayan idanuwa sun kara fitowa sakamakon cikar da naman idona nai fari na karu sosai har wani shining na ke, ban tana lura da haka ba sai yau da nake kallon kaina a madubi. Murmushi mai wanda ya kara min kyau madaidaicin bakina ya kwanta dan jan bakina da na shafa ya kara fitowa, hannuna na kai na janyo gashina da nai parking a baya zuwa saman wuyana, sannan na dauki wayata ina daukar kaina hoto. Ta cikim madubi na hango Aliyu wanda ya saka wani boyal sky blue kamar na nawa sai dai nawa yadi ne kalar ce kawai daya. Zuwa yai gabana ya tsuna tana ta kallon fuskata ni ko ina aika masa da murmushi mai kyau da saukar da natsuwa.

“Kalle ki Babyna kamar ba ke ba”

Wannan karon dariya nai ya lumshe idona na bude, ni kaina ina jin cewar kamar ba ni ba ce, ta wani bangaren duk wani abu da ke ta yar min da hankali a yanzu babu shi, na samu rayuwar da ban taba mafarkin samu ba, kuma a cikin sauki ciki kuwa har da saduwar da Mama za tai yau da iyala wanda shi yafi komai faranta min rai a yanzu, da kuma muhunta Asim da za ayi, ga kuma auren Aliyu wanda na san shi ma babban nasara ce a rayuwata domin har ga Allah ina jindadin yadda yake kula da ni yana nuna min kauna, babban abun fargaba ko damuwa a rayuwar aure shi ne samun miji da baya baka kulawa ko kuma baya kaunarka, amman ni ina jin cewar na yi wannan dacen duk kuwa da ban san mi gaba zata haifa ba amman ina jin cewar Aliyu zai iya tsaya min a ko wane hali na samu kaina. Ta dayan bangarem kuma ida na tuna yadda Allah ya daukaka daraja da martabata a take ta ba kuma ta hanyar kowa ba sai ta hanyar mahaifiyata wacce kowa ke gani a wulakance yana raina mu. Lallai bayan tsananni akwai dadi a tafe wani a kusa wani kuma a nesa, a duk inda duhu yake a akwai haske, a tsoro na da rashin gatana na samu kwarin guiwa da gatan da ban yi tsammani ba. Idan na tuna farkon abunda nai ma Aliyu na fasa masa mota da ruwan da ya watsa min a tufafi sai abun ya bani mamaki kuma ya bani dariya, kamar ba mu ba, mutumen da ke kyamar talaka yana ganin kamar ba su da raja yau shi ne a gabana a matsayin mijina har yake yabona ya fada min cewar yana kaunata.
Hannuna na ji an kama wanda hakam yasa na dawo daga duniyar tunanin da ke, agogon hannu ya saka min mai kyau sosai sannan ya saka min wata tsarkar hannuna dake tare da agogon, sai yai ma hannun nawa kiss.

“I love you both”

Ya fada yana min wani lallausan murmushi mai kawata fuskarsa da siffar zatinsa. Goma saura muka fito tare da shi, ina rike da wani jakarta ta rayatawa shi kuma yana rike da karamin akwati kuma ya janyo babban, da kansa ya saka akwati bayan mota sannan ya bude min na shiga kamar yadda na sawa kaina a yanzu ko kuma na ce ya sabar min na bude min mota da kansa.
Tun kan yai horn ko yi ma motar key mai gadin ya bude mana gate.

“Za mu tafiya zuwa Nijar yau, ban san tsawon yaushe za mu kai a can ba, amman dai ba za mu dade sosai ba, ka kula da gidan da komai, kuma karka bar kowa ya shiga ciki”

Ya fadawa mai gadin daidai lokacin daya tsayar da motarsa a gurin da yake. Sannan ya bude wani guri a cikin motar ya dauko kudi masu dan dama ya mika masa.

“Ka siya abinci kuma ka yi wata lalurar idan ta taso”

Hannu biyu ya saka ya karba yana ta masa godiya sannan ya ja motar kuma nufi gidansu Mama Fulani, kamin mu karasa har Mama Fulani ta kira shi a waya wai ana jiranmu.
A harabar gidan ya faka motarsa ta cikin motar ya miko hannu ya bude min kamin ya fita, muma fitowa muka nufi bangaren Mama Fulani tare da shi, a falo muka samu Maryam da Rukaiya da Mama Fulani zaune, Aliyu ya fara sallama sannan ni ma nai, ta amsa mana ita da su Maryam sai dai bata kalli inda ake ba, na gaishe ta ban yi zaton zta amsa min ba na yi zaton yar jiya zata min sai na ji ta amsa min amman salaf da ita gishiri kamar ba ita ba, ta wani sukuku kamar marar lafiya.

“Ya jikin naki Mama?”

“Al-hamdulillah, Tun dazun ake ta jiranku Ammy ta aiko sau biyu tana cewa na kira na fada maka wanda zai dauke ku ma ya zo”

“Okay, Ki yi Mama bankwana”

“Mama ina kike karanta bankwana sai mun dawo”

“Allah dawo da ku lafiya ya tsare”

Shine abunda kawai ta fada bayan an fada mata haka sannan ya mike tsaye ta nufi upstairs, Aliyu kuma ya kalli Maryam da Rukaiya dake zaune a saman kujera suna satar kallon mu.

“Allah ya kiyaye ya tsare”

Ko wace su ta fada sannan muka fito daga bangarenta muka shiga bangaren Ammy, Mama da Ammy na zaune a falon da kuma Yusuf wato dan'uwana kuma jikan Mai Martaba wanda suka zo tare, Humaira ma na falon ita da Zee da ke ta aikin chatting. Mama na sanye da wata kamfala ja mai kyau sosai kana ganinta kasan mai tsada ce wacce na ke kyautata zaton Ammy ce ta bata domin bata zo da tufafin ba a lokacin da zata baro sokoto ta zo nan. Na gaisa da Ammy kamar yadda na saba Aliyu ma ya gaisa da ita sannan ya gaisa da Mama sai ya fita daga falon yana lasa waya, ni kuma na koma kusa da Mama na zauna.

“Ki gaishe shi mana”

Ta fada tana nuna min Yusuf da ke murmushi yana kallona, da yaren buzanci muka gaisa da shi yana amsa yana min wasar tabasai kamar daman can ya sani, ni dai ban rama ba domin ban san yadda na ke da shi. Tare da shi muka fito daga bangaren Ammy, hakan kuma be yi ma Aliyu dadi ba, na fahmcin hakan ne ta fuskarsa da na gani a daure yana ta aika min da harara kasa kasa. Kowa ya fito yana mana Allah ya tsare sai mun dawo ciki kuwa har da Maryam da Rukaiya abun babu ko kunya, kuma babu sha'awar gani, ina kyautata zaton sun yi hakam ne saboda kar Aliyu ya ga laifinsu ko kuma Mama Fulani ce ta cilasta su domin ta san Yaran Ammay ma sai sun fito. Aliyu ya zauna gaba ni da Mama muka zauna baya, Yusuf yaja motar muka kama hanya, tsakanin ni da Mama aka rasa wane ya fi wani farinciki da zumudin ganin yan'uwan, ita da ta shekara ashirin rabonta da su ko kuwa ni da zan fara gaduwa da su a yau? Tun da muka shiga motar ni da Mama da Yusuf ne kawai muke magana Mama da Yusuf na yi da yaren buzanci ni kuma sai na maida wata maganar da hausa saboda Aliyu, shi dai be ce uffan ba.
Chapter 125 · 0% Book details