← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 87 OF 143

Sashe 87

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Banza ta masa ta kawar da fuskarta sai ya mike tsaye ya nufi cikin gidan ya barta da kanshin turarensa. Tun daga shigowarsa falon ya ga tv a kashe babu kowa a ciki ya san ba lafiya ba, domin sun saba kunna tv ko ba sa kallo su barshi a haka, kitchen ya fara lekawa domin ya fi tararda Momy a can ganin bata nan yasa ya wuce dakinta sai ya same ta zaune saman gadonta da magani a hannunta tana sha, yana ganin yanayinta gabansa ya fadi, da sauri ya karasa kusa da ita ya zauna bakin gadon.

“Momy lafiya?”

Momy bata iya ce masa komai ba sai Husna da ke tsaye ce ta labarta masa abunda ya faru. Cikin wani irin bacin rai Aliyu ya mike tsaye da zimmar fita sai Momy ta kirashi.

“Ina za ka je?”

“Momy ba a haifi dan da zai fada miki magana na kyale shi ba, idan ba shi da hankali to yau zan amsa shi”

“Ban yarda ka ce masa komai ba, ban yarda wata magana marar dadi ta fitowa daga bakinka zuwa kunnen Muhseen, ban yarda ba”

Dawowa yai ta zauna babu wani abu a duniyar da ya wuce bin umarni uwa ko da ko ba shi da dadi.Zaman sa da minti biyu zuwa uku Daddy ya shigo shi ma hankalinsa a tashe, domin ko kadan baya son tashin hankalin matarsa kamar yadda ita ma take gudun na shi.

“Kin yi kuskuren aikata abunda kika aikata Hajiya, ba lallai ne Muhseen ya fahimce ki ba, kuma tabbas zai dauka kin yi hakan ne saboda ki hana shi ita ki aurawa Aliyu ita”

Dagowa Momy tai ta kalli Daddy.

“Ban san na yi kuskure ba sai a yanzu, kuma ta hanya daya ce na ke ganin zam iya gyarawa”

Aliyu ya yi saurin kallonta.

“Wace hanya?.... Momy karki ce dai za ki aurawa Muhseen ita? ”

“Ta hanyar bata dama ta zabi wanda ta ke so tsakanin kai da Muhseen ko kuma wani ma dabam, idan kuma bata son auren zai tai ta karatu har lokacim da zata ji karatun ya gundireta”

“Momy karki bata damar za bi Wallahi Ataa bata san wanda take so ba”

“Aliyu.... ”

Daddy ya kira sunansa yana kallona ya kada masa kai.

“Tashi ka fita”

Mikewa Aliyu yai ya fice yana jin cewar abunda Momy take son ta aikata be masa dadi ba.

“Ta wannan hanyar ce kawai na ke jin cewar zan yi ma Ataa da mahaifiyarta adalci kuma na wanke kaina a gurin Muhseen, so babu abunda ba ya sakawa, idonsa ne ya rufe har ya iya fada min ba dadi kuma ya aikata abunda ya aikata, amman ba halinsa ba ne”

“Amman ko ma minene ai be dace yai miki abunda yai ba, tun da ba karamin yaro ba ne shi”

Husna ta fada, sai Momy ta kalli Daddy da idonta dake cike da kwallah ta ce.

“Ina son ka min izini, na tafi Abuja gobe kamar yadda muka tsara, idan ma babu jirgi zan iya zaman mota”

“Zuwan ki Abuja yanzu ba shi da fa'ida, zai kara lalata abun ne kawai”

“Murna kawai zan tafi saboda na fadawa Fulani zan zo gobe nai mata murna”

Daddy be ce komai ba ya juya ya fice daga dakin.Daddy na fita Aliyu ya dawo dakin ya xauna a inda ya zauna dazun.

“Momy kar ki yi haka dan Allah, Wallahi Ataa ba zata taba ce miki tana so na ba”

“Ba kai na ke son ta ce tana so ba, wanda duk zuciyarta ta natsu da shi na ke son tace tana so, idan kana da dama gobe zamu je Abuja tare da kai, Husna ki kaiwa Daddynku abinci”

Tana fadar hakan ta kwantan saman gadon saboda zazzabin da take jin yana taso mata.

ATAA POV.

Bayan ya wuce na tashi na shiga ciki na cire kayan jikina na saka uniform din islamiyar da hijab din na fadawa Nana cewar zan tafi makaranta sannan na fito sanye da takalmina na nufi gate na fice abuna, domin an san hanyar da ya bi da ni lokacin da zai kai ni dan haka zan iya kai kaina a kafa ma domin na saba tafiyar kafa.

Ban ankara ba na ga an faka mota gabana tare da bude min ganbun motar.

“Shigo”

Yau ya furta ba kamar ranar da ya kasa ce min na shiga ba, ba musu na shiga na rufe motar sai na dan kalleshi kadan na dauke kai, yanayinsa na canja fuskarsa da bawa mutane tsoro da yi musu barazana ta koma kalar tausayi da damuwa. Sai da ya fara tuka motar sannan kalleni a raunane ya ce.

“Momy zata ba ki zabin wanda kike so”

A tsakanin tambaya da labari sai na rasa wanne yake ba ni daga ciki, tambaya yake za ta ba ni zabin? Ko kuwa fada min yake.

“Ban sani ba wata kila yau ko gobe ko jibi ko anjima”

Sai kuma yai shiru ya cigaba da tukinsa, ni kuwa ina ta karantar abunda yake kokarin sanar min.

“Ba za ki za be ni ba saboda ba ki so na, ba za ki za bi Muhseen saboda ya bata miki rai, Kamal za ki zaba saboda kina jin cewar shine kawai mutumen da be taba yi miki komai ba”

Shiru ya kara yi kamar dai dazun ba sake cewa komai ba har muka isa islamiyar, waya yai ya sanarwa da malamin zuwana sannan ya fita daga motar ya zagayo gefena ya bude min na fito, sai ya tsaya yana kallona har na shige cikin makarantar.Kamin na karasa cikin makarantar malamin jiya nan ya fito ya tarbe ni, wani ajin ya kai wanda ni kadai ce a ciki sai kuma shi da ya dawo dauke da tarin littafai ya miko min. Tambaya ya soma min inda na tsaya a karatuna abunda na ke iyawa da wanda bana iyawa, sai ya fada min cewar zai mayarda ni alifun ba'un ta yadda zai zama ina iya hada harafi da kai na karanta abu, har yana fada min wai sai na yi hakuri domin zan ga a cikin sa'anina ni kadai ce na ke wannan karatun, sam hakan be dame ni ba, domin neman ilmi ne, ilmin ma wanda zai amfane ni duniya da lahira, ban taba jin cewar na girmi karatu ko kuma karatu ya girme ni ba, a kullum fata na bayan samun lafiyar Nana na samu na yai ilmi ko da kadan ne. Bayan ya gama mim gwaje gwajen da zai min ya mayarda da ni wani dakin mai cike da dalibai wasu sa'ana wasu na girme su wansu kuma sun girme me sai dai dukansu suna da karatu gwanin sha'awa abun ke nuna cewar makaranta ba a wasa da karatu.
Karfe shi da daidai aka tashe bayan an saka wata Rukaiyah ta yi mana addu'ar rufewa, haka muka jero muka fitowa daga makarantar wasu na tafe suna fira da abokan tafiyarsu wasu kuma sun koma can wani bangare suna siyen wasu abubuwan na kwalan da makulashe, sosai da sosai na jidadin zuwana makarantar sai ya tuna min da lokacin da na ke karama ina zuwa wacan ilamiyar ta Clapperto ta Khalifa. A inda na bar motar Aliyu fake da zan shiga a gurin na same ta sai dai yana cikin motar zaune kuma da alama ni yake jira. Karasa nai ina kallonsa ta cikin gilashin motar wanda ya kasance fari ba kamar na dayar motarsa ba wanda ya kasance baki, ya kwantar da kujerar motar ya kwanta jikinta ya rumgume hannayensa a kirji ya lumshe ido.Ina kwankwasa kofar motar sai yai saurin bude idonsa ya kalleni tare da miko hannunsa ya bude min motar na shigo, hannuna na kai na rufo motar sannan na maida hankalina gurin littafan da ke hannuna. Shi kuma yai ma motar key mu ka kama hanyar gida.

“Ataa.. Idan Momy ta ce ki fadi wanda kike so ki ce ni kinji....?”

Yayi maganar ba tare da ya kalleni ba maganar ma sai rabewa take kamar an tausar numfashinsa, ban yi mamaki abunda ya fito daga bakinsa ba domin na san Aliyu yana son Momy zai iya komai dan ya faranta mata ya saka ta farinki, Saboda ya cikawa Momy burinta, Saboda ya faranta mata rai ko da baya so na zai iya rokon nai haka domin ya san a yanzu ba zai iya cilasta ni na yi dole ba. Kamar ya san abunda na ke sakawa a rai sai naga ya faka motarsa gefen titi ya kalleni ido cikin ido ya ce.

“Saboda Ina son ki....!”

Waigawa nai na ga ko wata aljana ce a baya da yake gani ba ni ba, sai na ga babu kowa, to ko dai shi ma ya sha wani abun ne kamar Muhseen? Anya ma dai Aliyun ne ko waninsa.

“Ni ce Ataa ce”

Na fada dan na tunatar da shi idan na manya wata kila ya dauka wata ce dabam ba ni ba ko kuma Rahma. Idonsa na raurau ya ce.

“Ki zargi duk abunda za ki zagar Ataa, ki fada min kalamai masu zafi da da ci irin kalaman da kika san za su taba kwakwalwata, ki tsane ni adadin tsanar da kike tunanin na cancanci samu daga gareki, amman karki zabi wani bokin rayuwa bayan ni”

Da gaske kalaman nan daga bakin Aliyu suke fitowa, mutumen da baya kaunar talaka da talauci shi ne ya zaunar da ni gaban motarsa yana fada min irin maganganun nan, sam ban yarda a gaske ne ba wata kila wata gadar zanen yake kulla min idan na aureshi ya rika cin ubana kullum ko kuma wani abun ne dabam, amnan idan ba shi ba taya ma Aliyu zai ce yana so na? Taya ma zai so ni da gaske? Ina da kyau ai wata kila shiyasa na canja ra'ayi ya ji yana so na.“Ban taba jin ina son ki dan wani abu na jikinki ba”

Ya fada yana girgiza min kai, ashe a fili nai maganar ban sani ba.
Chapter 87 · 0% Book details