← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 143

Sashe 58

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Kara ni na mutu ita ta rayu da ta muti ta barni, jiya ba tai bachi ba saboda azabar ciwo, bata iya tashi komai a inda take take yinsa bata gane kowa ni ma da nake yarta bata gane ni ba, kuma ba mu da inda za mu babu wanda zai taimaka mana ina son mahaifiyata bana son ta mutu”

Na karasa cikin kuka mai karfi daman tun da na soma maganar hawaye ke sauko min. Shi ma hawayen na gani a idonsa sai yai saurin daga kansa sama ya zuba hannayensa aljihu.
ZAKI

By Khadeeja Candy

29...

Dukawa nai a gurin saboda kukan da ya ci karfina. Sai ya bar ni a gurin ya nufi cikin gidan be dade ba sai ga shi ya fito rike da gorar ruwa da cup dayan hannunsa kuma rike da tissue, ya nufo inda nake, tissue ya fara bani ba tare da ya ce min komai ba, na karba na share hawayena sannan ya bude gorar ruwa ya zuba min a kofi ya miko min. Karba nai na sha rabin ruwan sai na risina na aje kofin kasa dana dago sai na ga ni yake kallo ba ko kyaftawa, dan kawar da fuskata nai ina goge hancina.

“Ina Mamarki ta ke?”

“Tana can gida”

“Wane gida?”

“Gidansu kawata”

Shiru yai be ce komai ba har na wani lokaci idonsa na kaina ban san abunda yake kallo a jikina ba.

“Shigo ciki ki zauna kamin na shirya”

Yana fadar hakan ya juya da zimmar komawa ciki sai kuma ya juyo ya kalleni ganin na tsaya a gurin na ki na bi bayansa.

“Ni ba zan shiga ciki ba”

Na fada ina turo baki ba tare da na kalleshi ba. Matsowa yai kusa da ni sosai kamar zai hade jikinmu gabana ya shiga faduwa kamshin turarensa ya cikani sai dan matsa baya na kalleshi ido ya zare min.

“Idan na ce ayi yi ake ba a min gardama, wuce ki shiga ciki”

Yadda yai maganar is like yana bani umarni ne kamar wani boss. Kara tubo masa baki nai na juya sai na ji an fisgo ni da mugun karfi an juyo da ni.

“Wuce ki shiga na ce”

Ya fada cikin muryar dake nuna bacin ransa yana zare min ido.

“Bana shiga gidan da matan gidan ba sa nan”

Cikin daga murya na yi maganar har Mai gadinsa daya koma gurin gate ya zauna sai da ya kallemu. Matsowa yai da fuskarsa yana fitarda numfashi da karfi.

“Haka Muhseen yake miki ko? Shiyasa kike dauko ko wane namiji dan iska, mahaukaciya kawai”

Yana fadar hakan ya sake ni da karfi har yana ture baya kamar zan fadi, sannan ya juya ya koma ciki ya bar ni a gurin tsaye. Juyowa nai na dawo gurin mai gadin na ce masa.

“Dan Allah ka kira matar gidan ka fada mata yanzu”

“Ba kun yi magana da shi ba?”

“Be ce min komai ba sai bakin fada, ni dai dan Allah ka kirata”

“Wallahi Alhajin ne ba a iya masa yanzu zan iya kiranta ya zama ganin laifi”

Na marairaice masa fuska tare da dukawa kasa ina rokonsa.

“Ka taimaka min dan girman Allah, Wallahi ina cikin matsala sosai”

“Gaskiya tun da ya nuna ba ya ra'ayi kara ki hakura kawai, ko kuma na baki number ta kina da waya?”

“Ba ni da waya Wallahi amman dan Allah ka taimaka min”

“Zan kirata amman sai mai gidan ya fita, domin ni bana iya magana kadan idan kuma nai karai ya ji zai iya korata dan ya fada min baya son hayani”

“In tafi zaka kirata kenan?”

“Eh zan kirata In-Sha-Allah”

Daya bani tabbacin zai kirata ne yasa na taso na fito daga gidan, cikin rashin jindadin domin haka ta bata cin ma ruwa ba, daman nasan indai shi ne za ko zai siya sai ya wulakantani tunda dan wulakanci ne. Har na kama hanya sai kuma ya juya na koma saboda bacin ran daya same ni gate din gidan na buga da karfi mai gadin ya sake leko ganina ya bude min karamar kofar.

“Dawowa kikai?”

“Eh”

Na fada da kamar Fada sannan na wuce zuwa bakin kofar falon na taka na kai jikin kofar na buga kofar da karfin tsiya.

“Eh daman ai na san ba zaka siya ba, amman idan ta zalince ce kana so ko? Idan a hanya ka hadu da ni zaka iya sakawa a danne a min tiyata a cire a sakawa shegiyar matarka, mugu kawai duk halin da mahaifiyata ta shiga kai ne sanadi kuma ba zan taba yafe muku ba azzalumai masu.... ”

Ban karasa ba ya bude kofar falon sai nai shiru na kawarda fuskata ina hawaye. Farin jean ne jikinsa da bakar riga mai kwalliya sai fararen takalmi hannunsa rike da waya da kuma keys din mota, kamshin turarensa duk ya cika gurin shi kuma ya min fadi a ido tsoronsa ya cika zuciya, ba kuma tsoro na kar ya dake ni ba, yana da wani irin kwarjinin da ke saka mutun tsoro na rashin dalili. Yana tsaye jikinnkofar daga ciki ni kuka ina daga waje kaina na wani gafen shi kuma idonsa a kaina kamar yana hararata kuma ba harararba. Juyowa nai na sauko daga gurin na nufi gate na fice abuna ba tare da na kara cewa komai ba, shi ma kuma be ce min ba, hanya na biyo ina ta tunanina kala kala ciwon nana neman maganinta da kuma abunda mutumen nan da matarsa suka min. Da karfi aka faka mota gabana sai na ga an turo ganbun motar an bude shi, dana leka sai na ga Aliyu ne a ciki yana kallon wani gurin, ba zai iya cewa na shigo ba saboda bakin girman kansa, idan ma na shiga ban san inda zai kai ni ba, sai akwai nai gaba abuna na barshi a gurin. Sai ya kara cin gabana da motar ba tare da ya min magana ba nima na kara yin gaba abuna, sai ya fito daga cikin motar ya biyo bayana ya fisgo kafadar hannuna ya dawo da ni ya saka ni da karfi a front seat ya rufe motar ya zagayo gefensa ya shiga ya hau titi ba tare daya kalleni ba.

“Wallahi ni ba zan yarda ka cutar da ni ba, wacan zalincin da kuka mana ya isa cin amanar da muka min kai da Mama Fulani sai Allah ya saka min”

Na fada ina saka dayan hannuna na murza inda ya rikani cikin kukan dana fara tun a lokacin daya rikoni ya saka ni motar domin ba karamin riko yai min har yanzu ina jin ciwo a guri. Wayarsa ya ciro ya shiga wani guri yai dannen dannensa sai na ji karar kiran waya yana fita ta speakers din motar.

“Hello Ranka ya dade idan ka kira ta samu, idan ba ta samu ba sai dai mu kira mu gaishe ka”

“To ta samu Bukar kana ina?”

“Ina gida tare da iyalina”

“Ina da patient ne ambulance nake so”

“Subhanallahi waye ba lafiya?”

“Baka santa ba”

“Wani guri zan saka a turo maka yanzu”

Sai yai shiru be ce komai ba, ni yake jira nai magana ni kuma ban sammaci hakan ba tun da naga ko kallona be yi ba.

“Ko ba ki ji ba?”

Ya fada still be kalleni.

“A Clapperto road house number 11 amman ta bayan gidan zaka shigo kananan gidanjen da suke nan”

“Okay”

Yana fadar hakan sai Aliyu ya katse kiran ya dauki wani farin Bluetooth ya saka a kunnesa ya kara gudun da yake. Cikin kannnen lokaci muka isa Clapperto road, wani abun mamaki har kofar gidansu Farida ya faka motarsa ina ta mamakin yadda akai ya san gurin kai tsaye ba tare daya tambaye ni ba. Fita nai daga motar na nufi dakin na kwano ba tare da rufe masa motarta ba. Wasu tufafin na canja mata na saka mata Hijab, sannan na zauna kusa da ita tana ta kallona kamar bata gane ni ba har yanzu. Ina jin lokacin da motar asibitin ta tsaya sai na ji muryar maza biyu sun doso dakin kwanon da muke ciki.

“Ina marar lafiyar take?”

“Gata nan”

Na fada da sauri ina mikewa tsaye sai suka shigo suka dauki Nana suka fita da ita zuwa cikin motar asibitin Farida da Mahaifiyarta suka fito suna kallo har da wasu makota da ke kusa.

“Ni ina zan shiga?”

Na tambayi mutanen da suka shige cikin motar. Sai na ji muryar Aliyu yana fadin.

“Nan za ki shiga”

Da sauri na nufi motar na shiga daman ban rufe ba, shi ma kuma jin kai ya hana shi rufewa. Da na shiga motar sai yai mata keys muka bi bayan mutane sai da muka fara nisa sai na ga sun bi hanyar Uduth shi kuma ya dauki hanyar arkilla da ni.

“Kai ba fa ita za a cirewa koda ba ni, ita ba kasa an cire mata daya ba, idan aka kara cire wannan mutuwa za tai”

Na fada ina shirin fashewa da kuka.

“Karki sake min maganar kodar nan karki sake”
Chapter 58 · 0% Book details