← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 128 OF 143

Sashe 128

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Wa ake aikatawa laifi be yafe ba? Allah ma muka masaba daidai ba yafe mana balle mu? Na san kin aikata kuskure amman Mai Martaba ma bayan tafiyarki ya ji cewar be aikata daidai ba ta hanyar nuna cewar zai aura miki wanda ba ki so, shi kan shi abun ya dame shi domin da be yi hakan ba da duka komai be faru ba, da yanzu wannan ciwon zuciya da na ke fama da shi na ki be same ni ba, da yanzu kina nan cikin yan'uwanki ana yin komai da ke, a duk lokacin da kowa ya taru sai na ji kamar ace kema kina nan, idan jikoki suka taru sai na tambayi kaina ko ina nake suke wane hali kike a yanzu, a mace ko raye ko kuma a cikin wata mummunar rayuwa”

“Ba laifi ba ne dan uba ya zabawa yarsa ko dansa abokin rayuwa na gari, Mai Martaba ba aikata laifi ba, kuma be yi hakan dan ya jefa rayuwata a matsala ko damuwa ba, yayi hakan ne saboda al'adar gidan nan ce, ni kuma sai na bijire na gudu na bar muku abun kunya da magana a gari, soyayya da kurciya a wacan lokaci ta debi da yawa har na kasa gane cewar abunda na ke kokarin aikatawa babban abu ne kuma be dace na aikata hakan ba, a lokacin dana farga daga abunda na aikata kuma sai na ga lokaci ya kure min ba zan iya gyara komai ba, amman na gode Allah daya ba ni ikon neman yafiyarku a lokacin da na ke da rai kuma kuke raye, Wallahi ba zan iya kwatanta irin farincikin da jindadin da na ke ciki ba a tsakanin lokacin da nai arba da mai martaba da kuma ganin ki a yau”

Mama ta fada tana hawaye. Sun dade suna tataunar magana tun tana a tsaye har ta kai g zaunawa, tana sako labarin Babana wai ai ga fuskarsa nan a fuskata, a lokacin da Mama ta bata labarin cewar tana da wani dan bayan ni wanda ya rasu sai da Kakar tawa tai kuka, sai dai Mama bata sako mata labarin ciwon kodarta ba a cikin labarin da ta bata. Ban bar dakin sai da na fara jin bachi kusan ma a cinyar Mama na fara shi sai da ta tashi ta ce na koma wai na baro mijina can shi kadai. Sannan na tashi idona da kufan bachi na dawo inda aka sauke mu kamin na iso har na gaji domin akwai tazara sosai a tsakanin bangaren matan sarki da kuma inda aka sauke mu. Ban yi mamakin samun Aliyu a farke ba, daman ban kawowa raina cewar zai iya kwantawa ba tare da ya gan ni na dawo ya tabbatar ni na fara yin bachin ba, hakan kuma ba karamin dadi yake min ba. Na yi zaton ko zai yi magana ya ce yaje na zauna na barshi a gurin, sai na ji shiru be ce komai ba kamar ma hankalinsa yana wani gurin. Bandakin na shiga nai fitsari na fito ina hamma har da hawayen bachi na cika min ido na ce.

“Baka kwanta ba?”

“Ba zan iya bachi ba sai na tabbatar ke kika fara yi”

Hawa saman gadon nai ba tare da na ce da shi komai ba.

“Ba za ki canja tufafin jikinki ba?”

“Bachi na ke ji sosai”

“Na canja miki?”

“A a ka bar su hakan nan”

Tashi yai yaje ya rufe kofar falon sanna ya dawo ya tura ta dakin sai kuma ya kashe wutar ya bata bayana ya rumgume hannunsa a kan ruwan cikina.

“Babyna gobe zan koma”

Ya fada min kamar mai rada bakinsa daidai kunne na.

“Miyasa baka son zaman nan ne?”

“Ina son na ga yan'uwanki su san ni na sansu, amman tafiyar ta dole ce”

“Miya faru?”

“Rahma bata da lafiya, ina bukatar na je na dubata”

A take bachin da nake ji ya wartsake wani abun na ji ya soke ni a cikin zuciyata wanda ban taba jin irinsa ba.

“Ko kadai kana neman wani uzurin ne daman?”

“Ko kusa, tafiyar ta zame min dole ne tun da ciwo ne ke damunta, ya kamata na je na dubata”

Shiru nai ban ce masa komai ba, sai dai ban jidadin ko sunanta daya ambata ba balle kuma zancen dubata, wata kila shi ya kitsa haka saboda na bishi mu koma ni kuma bana jin zan yi haka, ko kuma yayi hakan ne domin ya koma wata kila kuma ita ce ta tsara hakan saboda ta samu damar da zai dawo ya baro nan ko kuma ta hargitsa mana tafiya ko wani abun da dabam da ban san ma'anarsa ba. Ni kan har na manta da yana wata mata wai Rahma ashe fa Aliyun ta ne nake aure, ko tana ina ma iho ban sani ba, kuma ban ji zan iya tambayarsa ba domin bana son ji wani abun daya shafi sunanta ma balle kuma ita din da kanta.

“Ki min alkawarin kula da kan ki pls”

Ya fada yana sumbatar saman kaina, sannan ya juyo da ni ya shiga aikawa ko wane bangare na jikina da sako. Mun farka da wuri sakamakon kiran sallah asuba da ya tashe mu wanda ake yi aciki masarautar, sai da ko wannen mu yai wanka sannan mukai alwala shi ya fita zuwa inda yake jin karar loudspeaker masallacin na fito ni kuma nai tawa sallah a cikin dakin, ina ta tunani ta inda ya ji cewar Rahama bata da lafiya bayan ma layin Nigeria ba yayi a wata kasar kamar yadda ya fada min, kwata kwata zancen tafiyar nan be min dadi ba, wata kila saboda na saba da shi ne ko kuma saboda Rahma zai je gani yasa na ke jin ba dadi oho ba dai zan iya fadar dalili ba.
  Bayan an gama sallah da kamar minti talatin sannan ya shigo inda na ke.

“Good Morning”

Ya gaishe ni tun kamin na mika masa tawa gaisuwar, nikan kasa amsawa nai sai kawai na gaishe shi da halshen hausa sai ya amsa min yana kissing goshina.

“Lafiya kalau, kin tashi lafiya?”

“Lafiya kalau”

Hannunsa ya miko ya kama nawa.

“Ta so mu kwanta ina son kiji dumi jikina kamin anjima”

“Da rana zaka tafi?”

“Ban sani sai an bincika min idan akwai jirgi”

“Wa zai bincika maka? Taya ina ma ka ji bata da lafiya?”

“Na kira wayarta ne, sai Yayarta ta dauka ta fada min”

“Amman ka ce layin Nigeria ba yayi a wata kasar”

“Yeah ban da Airtel na can yana yi a nan, har daga saudiya ma ina kira da Airtel, na saka Nasir ya bincika min, ke kuma yanzu ina son ki fada musu zancen tafiyar idan mun shiga gaishe su”

Na gyada masa kai kawai ba tare da na ce komai ba. Kamar yadda ya fada na ji dumi jikinsa sosai ta a kuma wanin abun mukai ba bayan dogon bachin safe normal sleep, sai dai yadda ya shigar da ni jikinsa ya rumgume ya saka na jidadi kuma na ji dumi da yake fada.

Misalin tara aka kawo mana abincin karyawa tun daga kan shigar masu kawo abinci za ka tabbatar da cewar bayin gidan ne, domin sukansu suna sanye ne da tufafi kala daya sun jero kamar tururuwa. Duk yadda ya so na ci abinci sosai sai na kasa, sakamakon dadin da raina baya min kan tafiyar da zai yi.
Sai dai na yi kokarin boyewa domin ni ma ban ga abun damuwar akan zai tafi gurin matarsa ba. Daya daga cikin yan matan gidan aka aiko wai na shirya na fito ni da mijina za mu je mu gaishe da Mai martaba da matan gida. Ni ce kawai nai wanka na shirya shi Kan Aliyu tun kamin mu fara karyawar yai wanka ya shirya.
  Rana ta fito sosai ko da muka shiga bangaren Mai Martaba tare da mai mana iso, na yi zaton wani gurin dabam za a kai mu inda Mai Martabar yake kebe sai ga mu a fadarsa ta jiya duka iyalansa da hakimansa suna ciki ban da shi. Muna shiga sai idon kowa ya dawo kan mu

“Zo nan ki zauna”
Chapter 128 · 0% Book details