← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 73 OF 143

Sashe 73

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya farka da wuri saboda be samu kwanan ba har garin Allah ya waye, bachi barawo ne amman ya san wanda yake sata, akwai gajiya sosai a tare da shi amman ko da wasa bachi be ziyarci idonsa ba. Bayan sallah asuba ya dawo dakinsa ya zauna, idonsa na masa nauyi na rashin samun bachi da be yi ba jiya, a yadan bangaren kuma tunanin Ataa ya cika masa zuciya, baya jin zai iya janye ya bawa wani damar daukarta a matsayin mata bayan shi ya fi kowa cancantar wanin ma kuma Aliyu. Idonsa sun yi arba da mata masu kyau masu aji masu natsuwa da hankali ya so mata da yawa saboda kyau amman be taba ganin wacce hankalinsa ya kwanta da ita kamar Ataa ba, kyauwonta ya dauki hankalinsa sosai kusan duk mace daya hadu da ita da kuma wandanda yai so a haya har Mama Fulani tana ce masa ya cika ruwan ido, be taba jin son wata kamar Ataa ba, wani bangare na zuciyarsa yake jinta dabam, ta ina ma zai iya yafe ta a zuciyarsa idan har ya yarda yace zai yafeta hakan na nufin ya zama ragon maza kenan. Kurciyarta mu'alamarta kyauta na daga cikin abunda yasa yake son Ataa.
Da gangan yai zamansa ya ki fita ya karya bangaren Mama Fulani kamar yadda ya saba, ya kwanta a cikin dakinsa ba dan kuma yana jin bachi ba sai dai Mama Fulani ta fahimci cewar yana cikin damuwa, domin ya san matsalarsa ba karama bace a gurinra yadda take tsanar talaka ba zata amince ya auri Ataa ba, balle kuma Ataa din da ta tsana tsana ta musamman.

Maryam ce ta shigo part dinsa ta tsaya daga bakin kofar bedroom dinsa tana kiran sunansa.

“Ya Muhseen Mama ta ce ka fito mu yi breakfast”

Na tare daya juyo ya kalleta ba ya ce.

“Bana ci”

Juyawa tai ta koma ba sai ga Mama Fulani ta shigo dakin hankalinta a tashe.Saman gadon ta zauna ta kai hannun tana tashinsa domin ya bata baya ne.

“Muhseen lafiya kake?”

Juyowa yai yana kokarin tashi zaune kallonta yai idonsa sun kade sun yi ja fuskarsa ta dan kumburo saboda ciwon kan da yake ji da kuma bachin da be samu yi ba.

“Mama ina kwana?”

“Lafiya Kalau Muhseen mi yake damunka?”

“Ba komai kaina ne kawai ke ciwo”

“Ba wani ciwon kai daga ni har Abbah ku jiya da tunaninka muka kwana, ka dawo cikin dare a yanayin da kowa ya ganka ya sam akwai abunda yake faruwa, yau kuma baka fito cin abincin safe ba na aiko Maryam ta kira ka ce wai baka cin komai, yanzu kuma ka fada min babu komai?”

Kallonta yai

“Mama ko na fada miki damuwata ba daukarta za ki yi da muhimmanci ba, ba lallai ne ki min maganin matsala ta ba”

“Mi zaka nema a duniyar da ba zan maka ba Muhseen? Kai fa da na ne karka manta wannan, matukar ina da yadda zan yi to zan maka ka samu ko mi kake so a duniyar nan”

Yaja wani dogon numfashi ya sauke.

“Kamin na fada miki damuwata ina son nai miki tambaya”

“Minene?”

“Mama ba dan ina danki ba, ina son ki fada min gaskiya shin ina da wani nakasu ne da zan ce ina son wata a hana ni? Ba ni da abunda ake so a namiji ne ko kuwa tarbiya ce bata wadace ni ba?”

“Babu, babu wance zaka furtawa so ta ki karba maka Muhseen babu ta babu abunda ka rasa a cikin abunda ake so a gurin ďa namiji, fada wace yarinya ce ta tashi hankalinka haka? Wa kake so Muhseen? Zan nema maka ita ko yar idan shugaban kasa ce”

“Mama Momy ta Aliyu sun bata ni a gurin yarinyar da na ke, saboda suna min kallon mazinaci alhalin ban taba aikata alfasha ba a rayuwa Allah shine shaida ta”

Kallonsa Mama Fulani take tana son tantance abunda ke fitowa daga bakin ďanta.

“Wa kake so Muhseen?”

“Ataa Mama Ataa”

Ya bata amsa kai tsaye yana wani marairaicewa.

“Momy da Aliyu sun yi min daidai, suna nuna maka, hanya kana cewa ba haka ba, sai yaushe zaka level dinka dana yarinyar nan ba daya ne ba? Sai yaushe zaka daina yaudarar kanka? Ka rasa wacce zaka so sai yar talakawa yarinyar zuri'ar kaskantattu, Aliyu ba kamako ba ne irin ka shiyasa ya ke nuna maka ka daina son ta kana ganin kamar takura maka yake amman matsayinka da na yarinyar nan ba daya ba ne Muhseen”

“Miye banbanci na da ita Mama? Talauci? Saboda ita yar talakawa ce ko? Idan har wannan ne kawai miyasa shi Aliyu yake son ta kuma Momy ta goya masa baya?”

“Aliyu ba zai taba son wannan yarinyar ba har a bada, Aliyu ya san abunda yake ba shashasha ne kamar kai ba, ba dan wannan abun daya faru ba ina da tabbacin Aliyu ko a hanya ya hadu da ita ba zai taba bata sadaka ba ma balle har ya taimake ta, kuma ka jira ka gani yana gama taimakonta zai watsar da ita”

A fusace Mama Fulani take wannan maganar ta juya zata fice Muhseen.“A niyarsa ta watsar da ita yasa ya dauketa ya kai ta gurin Momy ko? Aka sama mata daki a cikin gidan, suka sauke ta a ciki aka bata gurin waka da tufafi, ana kula da mahaifiyarta, idan ba sonta yake ba mi zai saka yayi mata duk wannan Mama? And if ba kaunarta yake na mi zai saka Momy bata ba ni goyon baya ba?”

“Ba zata taba baka goyon baya ka auri yar matsiyata ba, yarinyar da ba a san asalinta ba, wata kila ma dangin mayu ce ta tafi da kurwarka tana can tana azzabtar da kai shiyasa kake ta haukan son ta, daman buzayen nan ba su aje komai ba sai bakar maita, Aliyu yana nuna maka abunda kake ba daidai ba ne kai kuma ka saka fahimta, kuma bakinka ya daina furta son wata yar talakawa ga Aliyu har abada Aliyu ba zai taba son Ataa ba ba kuma zai taba son wata banza kamar ta ba, ni na raini Aliyu tun yana karami har ya girma na san waye ďana tir Aliyu ya so Ataa balle har ya aureta”

Ta fada tana tofar da yawun bakinta sannan ta fice daga dakin tana kara fadin.

“Ka mutu indai akan Ataa ne”

Wani irin Muhseen ya ji kamar an saka takobi an fasa kirjinsa an fiddo zuciyarsa an raba ta gida biyu. A take kan ya kara safa masa, daman ya san Mama Fulani ba fahimtarsa zatai ba, ba kuma shige masa gaba zatai kamar yadda ya so ba, ba dan komai ba sai dan ta tsani talaka, kwantawa yai saman gadon ya rumshe ido kamar mai bachi yana jin yadda zuciyarsa ke masa mugun zafi.

A fusace Mama Fulani ta dawo part dinta har wani huci take saboda bacin rai.

“Mama Lafiya?”

Rukaiya dake falon ta tambaya.

“Wai ni Muhseen zai kalla ya fadawa yarinyar can Ataa yake so bayan na gargade shi akan kar ya sake kula ta?”

“Ataa kuma? Yana nufin saboda ita ya shiga damuwa?”

“So yake yai hakan saboda na tausaya masa ni ko mutuwa zai yi ba zan taba bari ya auri wannan yar iskar yarinyar ba, wai har wani cewa yake Aliyu ma son ta yake Momy ta goya masa baya”

“Taf Ai Wallahi Ya Aliyu ba zai taba son ta ba son ta ba, idan ma ya ji Ya Muhseen ya wannan maganar sai sun samu matsala da shi”

Cewar Rukaiya tana kai bread a bakinta.

“Shine dai dan ya ganta yana son ta sai ya dauka kowa ma son ta yake, maganar Maryam ce kyau nn ne yake dibarsa”“Ni wannan yarinyar zuwanta gidan nan ya zame mana fitina, daga ganinta shi da Kamal har da Ya Aliyu ma suka haukace”

“Kaddara ce ta saka aka kawo min ita daman, ba zan sake daukar ko wace yar aiki ba, dan nan gana sai a a kawo wacce Abbah ku zai gani yace ita yake so ma, shi kuma Aliyu bar ni da shi har wani sauke ta gidansa yake”

“Wata Momy ce ma ba shi ba, kin san halin Momy Allah yayi ta da son jan mutane a jiki ko tsoro bata ji”

“Ai zan kira shi sai na saka ya dauke ta daga cikin gidan nan, idan mai kyau Muhseen yake so ya koma tsason mu mana, akwai kyaun da ya wuce yayan fulanin asali ma, wannan da ba a san inda ta fito ba ni abun nan har mamaki yake ba ni wallahi, mtssss”

Mama Fulani ta fada hakan tana nufi dakinta har yanzu bata daina jin haushin maganar da tai da Muhseen da ta sam tun farko abunda zai fada mata kenan da bata dame kanta da son sani ba, ita dai bata da wani abun a gurin Ataa ba, ta san tana da kyau amman a gurin ko kafi kowa kyau a duniyar matukar baka da nera ko kuma kai ba dan kowa bane, biri ya fika a gurinta indai har birin nan yana da masu gida rana.

Bayan fitar Mama Fulani dakin ya sauka daga kan gadon ya nufi gaban madubinsa ya tsaya yana ta kallon kansa, a zahiri kansa yake kallo amman a badini tunanin mafita yake, har ga Allah yana son Ataa shi a yanzu ma yaji yana bukatar aure daman rashin samun wacce tai masa ne yasa shi be maida hankali gurin auren ba, amman yanzu ya yana jin son aure sosai a ransa, kuma yana matukar jin kaunar Ataa a ransa.

“This is the right time daya kamata nai fighting akan abunda na ke so, this is the right time da zan tsayawa kaina da kaina, ba zan iya barin wannan ta wuce ni ba, idan har ba zata so ni to be kamata ta so Aliyu ba, idan har zan iya hakura na kyaleta to ko ba sonta na ke ba”
Chapter 73 · 0% Book details