← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 143

Sashe 79

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Dariya suka yi har ita da tai maganar domin ta kareshi maganar ne tana wani murmuda ido irin na su na manyan mata.

“Ina yarana? Ban ji motsinsu ba”

“Husna da Amina sun fita Siyama kuma tana can bangarensu Ataa”

“To Alhajin Fulani ya samu cigaba kamfanin nan da yake ikirarin za a siyar wani dan kasuwar kasar nijar ya siye shi, Kuma ya bar ragamar tafiyar da kamfanin a hannunsa, ya kamata ko ban samu zuwa ba ki shirya da yara ko kwana daya ne suke ku masa murna, samun cigaban dan'uwana kamar nawa ne, ba ni da wani wanda ya fi shi a yanzu”

“Gaskiya na masa murna sosai, Allah ya dafa ya taimaka, daman haka muke so ai, to wannan tafiyar fa?”

“Ki samu wata kuje daman biko ai na mata ne”

Yana fadar hakan ya fice daga falon ta biyo bayanshi tana ta taya shi murnar samun siyen kamfanin da akai har tana fadar ranar da ya dace suje.Bayan sallah magariba Momy ta kira kawarta Hajiya Ramatu ta fada mata cewar za su je bikon Rahma. After sallah isha'i idan tana da time, ana saukowa daga sallah isha'i sai ga Hajiya Ramatu ta zo gidan ita da danta wanda shi ya janyo motar ya kawo da ita a gidan, tana shiga falon Momy ta fito sanye da mayafi suka gaisa a tsaitsaye suka koma cikin motar Hajiya Ramatu, kamin su isa gidan Alhaji Nasiru Gobir wato mahaifin Rahma Momy take labartawa aminiyarta Hajiya Ramatu abunda ya faru tsakanin Rahma Aliyu. Tsaki Hajiya Ramatu taja cike da jin haushi ta ce

“Wai Hajiya Hadiza miyasa ba za ki saka Aliyu ya kara auren ba? Wannan iskacin da jin kan da yarinyar nan take masa ya yi yawa, wallahi idan yanzu ya kara aure duk wannan iskancin dainawa za ta yi kuma dole ta kama kanta idan ta ji ba zata iya zama ba ta fita”

“Kamar a gaban ki akai, Wallahi dazun mahaifinsa ma haka yace kin san ko maza ma basu cika kula da sha'anin aure kamar mu mata ba”

“Wallahi akwai haushi Hajiya Hadiza abunda ake masa ne ai yayi yawa, duk irin hidimar da yake musu basa gani? Bawa ne shi?”

“Ido ne nawa idan ya ji wuya shi zai nemi karin auren da kansa ai, amman na san da Fulani ta san da wannan Wallahi da sai tana zuwa bikon nan daman can ba son aurenta da Rahma take ba”

“Ke ma dai ai da ba ki je ba Wallahi da ya zuba musu ido ya barta tai ta zaman gidan har sai zaman gidan ya isheta”

“Kin san iyayen miji idan ba su yi ba, basa fita idan ma suka kai ba fitar suke ba, yanzu ma sai an dora laifin a kanmu”

Hajiya Ramatu ta tabe baki cike da jin haushi. Ba laifi yan'uwan Rahma yayanta da kannen sun tarbesu cikin girmamawa da mutunci, sai dai mahaifiyar Rahma na fitowa sai ta canja musu fuska kamar wacce bata son zuwansu. Ciki ciki ta gaisa da su Momy na ganin hakan ta dauke kai ta ki cewa komai sai Hajiya Ramatu ce tai bayanin abunda ke tafe da su.

“To ya gaji kenan? Yarinya ta zo gidansu sati biyu dan tsabar wulakanci be zo ba be aiko ba, sai yanzu idan ya gaji da ita ai ba sai ya wulakanta akan yar talakawa ba, wai har ya mari Muneera akan wata banza can sha sha sha, yarinyar da be san inda ta fito ba, idan ma gajiya yai da ita mu ai muna son ta ba mu gaji da ita ba”

Wani wawan kallo Momy tai mata har tana kashe ido tsabar bacin rai.

“Yar talakawa da ba a san inda ta fito aka dauki kodarta aka sakawa yarki, sai yanzu na gane ashe Rahma bata rage komai daga halinki ba, ke kika koya mata kyamar talaka talakar ma wacce ta taimake ke ku, ba mu damar zuwa bikon Rahma ba sai yanzu, shi kan shi mijin na ta ma be so mun zo ba, domin ba shi ya koreta daga gidan ba, yarinya kamar wata mai shan nono da an yi abu ta dauki kafa zuwa gida ko kunya babu, mi Rahma zata nuna mana? Gata ko kudi ko family? Ba ta nuna mata dukiya ke kanki kin sani zuri'a kuma duk sokoto an sani babu wanda ya fi torankawa asali da tarin yan'uwa, duk abunda take muke shanyewa muna shanyewa ne saboda muna son ta zauna lafiya da mijinta, domim Rahma bata san wani abu wai aure ba, dan abu kadan ta kwaso kafa zuwa gida haka ake yi?”

“Au daman ba shi ya aiko ku ba kuka zo? To ki koma Rahma ba zata koma yanzu ba sai ta huta, sai Aliyu tako da kansa ya dauki matarsa, dacan idan ba nan ba so kike ta koma gefen titi tana bara kamar yar da danki ke so? Abun kunya wai kamar SSG ace dansa yana son yar bara a titi, mutum mai daraja wanda ya rika mukamai masu girma ace an rasa wacce dansa mai kamfanin Sky global resources yar talakawa makaskanciya, ku kanku ai abun kunya ne a wajenku”Momy ta girgiza kai tana kiran sunan Aliyu baro baro.

“Sam ni nikam abun alfahari ne yau Aliyu ya auri Ataa ko babu komai zai inganta rayuwarta kuma sai san yayi aure, ya kuma gane banbancin tarbiya da rashinta”

“Daman ai saboda kin cusa nasa son wata ne kike wannan bobotan, indai yana son Rahma ta koma dakinta to ya janye neman aurensa da wannan kazamar yarinya, ya hada Rahma kishi da yar wani mai kudi ba amman ba wannan ba”

Momy ta yi yar dariyar takaici tana mikewa tsaye tare da Hajiya Ramatu wacce ta kasa cewa komai tun da aka fara fada.

“Hajiya Talatu kin yi tutu gonar mai munta, zaman gida dai ko? Rahma tai ta zama har Mahdi ya bayyana, idan kuma zaman ya isheta sai ki dauke ta ki kaita dakinta, amman wani daga ni ko Aliyu ba zai zo bikon wannan yar ta ki ba, kuma ki zuba ido indai ina raye Rahma sai ta kishi da yar talaka...!”

Momy na kawai nan ta nufi kofar fita a fusace, daf da zata fice Hajiya Talatu Mommyn Rahma ta ce.

“Ai dole ku nema masa yar talaka, domin kin san babu yar gata gabas da yamma da zata zauna da juya, dimmar da yai mata ai ya mata ne saboda ya san baya haihuwa su taru su mutu tare”

Momy ta juyo ta kalleta.

“Ke Hajiya Talatu idan ba ki gode ni'imar Allah ba za ki gode ma azabarsa, ruwan cikin lokali ya ishe mai hankali wanka kuma ki rubuta ki aje da ikon Allah sai Aliyu ya yi aure ya haihu....”

A fice Momy ta fice daga falon tana nadamar zuwan bikon da tai. Momy na fita Rahma ta fito idonta shakaf da hawaye ta fadi a kusa da Mommynta kamar zata narke.

“Na shiga uku Mommy mi yasa kikai fada da su? Na rantse da Allah Aliyu ba zai zo bikona ba, tun da kika taba masa uwa, Wallahi ba zai sake ganin kimata ba, Aliyu baya son a taba masa family”

“To sai mi? Aliyu shi kadai ya rage a duniya ne? Ko sakin ki yai sai kije ki auri mai haihuwa ki haihu, kar wannan abun ya daga miki hankali matukar yana son ki dole ya dawo, ai yasan gidan da ya dauke ki gidane mai daraja da kima”

Cikin kuka Rahma ta tashi ta koma dakinta, Muneera ta taso daga dayan bangaren na falon daman falon ya kasu biyu ne, ta nufo inda Mommynsu take tana dariya.Husna ta tashi ta nufi karamin firjin din dake dakin ta dauko mata ruwa da kofi ta kawo mata ta zuba mata, sai da Momy ta sha sannan ta labartawa Husna abunda ya faru.

“Mutanen nan suna ba ni mamaki, wai talauci hauka ne? Shikenan dan suna da arziki sai su taka mutane yadda suka ga dama”

“Su taka wanda yake neman abu gurinsu dai, arzikin da ba na shi ba, mai tinkaho da abun wani duk uwar dukiyar da yake kuri da ita idan aka kasa uku ko kashi daya ba zai dauka ba, dukiyar wani ce wanda idan yau ya kaushe abarsa sai dai tu koma rabe raben wani, shi har abun tinkaho ne? Wai wanda ya gaji arziki baya haka”

“Gaskiya abunda suke yayi yawa, haba jama'a wai Wallahi sun ja mata domin Ya Aliyu ba zai je bikon ta ba”

“Tai ta zama a can har sai zaman gidan ya isheta ta yi hankali aure dai sai Aliyu yayi kuma Ataa zai aura sai dai su mutu?”

“Momy da Ataa?”

Husna ta tambaya tana zare ido.

“Eh ba ni za su nuna isa ba? Sai ya aureta?”

“Ya Muhseen fa?”

“Amina zan bashi, daman ai Fulani ba zata yarda ya aureta ba, kuma ko aurenta yai ba dadin zaman zata ji ba, amman yanzu Aliyu nake son ya aureta ya maida mutum kamar yarsu in ya so sa su mutu”

“Amman Ya Aliyu zai yarda ya aureta ne? Kin san fa ba sonta yake ba?”

“Ba son ta yake ba yake kishinta? A banza ake kishin mace? Idan ma baya son ta sai ya fara daga yanzu”

Cewar Momy tana wani cika har yanzu zuciyarta ta ki ta sauka daga bacin ran dake tare da ita.

“Amman Momy Ya Muhseen zai ga kin masa rashin adalci”

“Na ce miki Amina zan ba shi ai yasan idan bana sonsa ba zan ba shi yar cikina ba, amman Ataa sai ta auri Aliyu In-Sha-Allahu”

“Idan kuma ita Ataa din bata son shi fa?”

Momy ta yi shiru alamar tunani kamin ta daki kan gadonta tana ta rawa da kafa.

“Ina bukatar sanin waye Ataa ina suka fito, shine kawai abunda na ke son sani a yanzu, amman bayan shi talauci ko wani abun ba zai hana wannan auren ba”

Husna dai ta kalli Momy ta janye fuskarta tana tunanin yadda za ayi wannan chakwakiya domin Muhseen ma ba kyalle ba ne, kuma yadda yake nuna yana son Ataa yana da wahala ya iya yarda ta auri Aliyu yana kallo.
Chapter 79 · 0% Book details