← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 138 OF 143

Sashe 138

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Mama kin san aikin nan fa ba mu saba ba, taya jiki irin nawa zai iya aikin wahala dan girman Allah? Kara dai a nema wata nai aikin”

“Wallahi ba zan dauko wata mai aikin ba, wato n dauko wacce Aliyu ya aure yanzu kuma na dauko wacce ubanki zai aure ko? To ba za a koma ba”

Mama Fulani na rufe bakinta Rukaiya na shigo cikin falon makkale da waya a kunnenta baki har kunne tana wasa da keys din motar hannunta, zaunawa tai kusa da Mama Fulani a lokacin da ta sauke wayar ta rumgume Mama Fulani tana murna kamar wacce akai ma albishir.

“Mama ke dai wani ne na hadu da shi, ya hadu Mama ga motarsa yar yayi”

“A'ina?”

Mama Fulani ta tambaya baki a sake Maryam kuma ta tashi zaune tana jin kamar ita ce.

“A gidan mai shi ya biya min kudin mai aka cika min motata tam, sannan ya karbi number wayata yanzu haka ina isowa yana kira wai na ji na isa lafiya, yana ta tambayar gidanmu”

“Wow Allah yasa mijin ne yanzu nan Mama take ta fada sai ka ce mu muka dorawa kan mu bakin jini”

Cewar Mama. Rukaiya ta kyalkyale da dariya tana kara rumgume Mama Fulani da ke murmushi cikin jindadi.

AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.Kamar yadda aka aje cewar Assabar za a koma, haka kuwa akai duk kuwa da kasancewar ranar ba a aiki amman a haka muka tafi ashe su suna shiga office saboda irin wannan case din har sun fi son ya fada weekend saboda kowa ya samu halarta. Kamar yadda akai wacan karon wannan karon ma haka kai daga gurin zama har mutanen su dai.
  Sai dai mun samu karin Shukura wato nurse din da fada cewar ita ce shaiduna. Ko da wasa Doc Asim be kalli inda take ba, sai dai ni da Mama yana ta kallonmu kamar be taba ganinmu ba, ya rame sosai ba kamar wacan lokacin ba idonsa har sun fito saboda ramar da yai.

‘Ai baka ga komai ba tukuna’

Na fada a raina ina kallonsa cikin jin haushinsa da kuma jindadin abunda zai same shi. A bangare daya kuma ina dan jin tsoron kar Shukura ta ki fadar gaskiya wata kila ma ya siye ta ballantana a asibitinsa take aiki. Sai da suka gabatar da wasu abubuwan sannan suka fara da tambayar ko Shukura ta san ni, haka ta tsura min ido tana ta kallona kamar bata gane ni ba, na san na yi kiba na kara kyau jiki da sura saboda samun jindadi da kwanciyar hankali da nake samu a yanzu, amman ba zai iya zama wani canjin siffa da zai saka Shukura ta kasa gane ni ba.

“Eh na santa”

“Kin san sunanta”

“Ba zan iya tuna sunanta ba, amman kamar Ita ne ko Aita na manta dai”

“A ina kika santa?”

“Asibitin da tai jinyar mahaifiyarta”

Sai da suka tambaye ta a wace Asibiti ne kuma ko ta san wanda ya kula da mu da kuma ciwon da yake damun mahaifiyata.

“Asibitin Doc Asim, na yi kula da ita a lokacin idan ina duty kuma Doc Asim shine likitan da ya duba ta”

Sannan suka bukaci na ta fada musu gaskiya tsakani da Allah abunda ta san yana damun mahaifiyata.

“Ciwon koda ne”

“Me kika sani a gake da Doc Asim?”

“Litane kwarare mai asibitin kansa wanda na ke aiki a ciki”

“Mun kira ki a nan ne saboda ki bada shaidar akan zargin Doc Asim da ke na cire kodar mahaifiyar Ataa ba tare da saninta ba, har ma tana ikirari ke kika bata shawarar ta dauke mahaifiyarta daga Asibitin ta kai ta wata idan ba haka ba zata iya rasa ta, kuma kina ta yi mata alama da kada ta saka hannu a takardun”

Kallona tai ta hade gayu kamin ta kalli Doc Asim sai kuma ta kalli masu yi mata tambayar ta gyada kai.

“Na bata shawarar ta dauke mahaifiyarta ta kai wata asibitin saboda samun lafiyarta, kuma tabbas Doc Asim ya cire mata koda domin tare da ni akai tiyatar kuma a gaban idona Ataa ta saka hannu a takardun, sai dai ba zan iya bada shaidar cewar ba da saninta aka cire kodar mahaifiyarta saboda ba a gana aka yi wannan maganar ba”

“Amman miyasa kika girgiza mata kai?”

“Ina girgiza mata kai ne, saboda karta saka hannu a takardun da bata masaniyar komai a kansu”

“Ba mu fahimta ba ki mana bayani dalla dalla yadda za mu ga ne”

“Takardun da Ataa ta saka hannu ba ita ce ta farko da take saka hannu a akan irin waennan takardun ba, ita ce ta uku daya an yi gabana na ta ma anyi a gabana dayan kuma labari aka ba ni”

“Mi takardun suka kumsa”

“Siyar da wani bangare na jikin dan'adam”

“Kina nufin Ataa ta siyarda kodar mahaifiyarta kenan?”

“Ba ni da tabbacin wannan, idan ma ta siyar ko akasin hakan ba a gabana akai komai ba, sai daia gabana Doc Asim ya rika hannunta ya saka hannu a takardar saboda bata iya sakawa kasancewar bata san komai a boko ba”

“Taya akai kika san cewar bata san komai a boko ba?”

“Ita ta fada min kuma a lokacin daya bata takardar ya ce ta saka hannu sai ta fada masa bata iya komai ba bata san inda zata saka hannu ba, wannan shine kawai abunda na sani”

“Miyasa kika ce ta dauke mahaifiyarta daga asibitin?”

“Saboda waenda suke jin irin nata daga karshe suna rasa ran waenda aka cirewa koda cikin asibitin”

“Su wa da su waye?”

“Akwai wata Hadiza Salisu wacce take unguwar mabera, da kuma Faruk Abubakar da ke unguwar Minannata sai kuma wannan Ataa din da ke unguwar Clapperto road”

“Za mu je da ke mu taho da su sati mai zuwa, au bada shaida a gabanki kin yarda”

“Na yarda”

Daga haka aka bawa Doc Asim damar magana sai ya sake nanata cewar shi saiyar masa da kodar Mama nai. Sai dai sun tuhumi she da siyen koda ba tare da neman yan'uwan masu ita ba, taya zai siye koda a gurin yarinya kamar ni bayan mahaifiyata bata cikin hayyacinta ba tare ya nemi yan'uwanta ba, kuma ya kamata ace akwai shaidu a tsakani.

Ni kaina sai a lokacin na kawo wannan tunanin a raina, lallai ya kamata ace ko a iya yan'uwan suka kai ya nemo su indai har da gaske ne, tun daga nan kowa ya san akwai cutar da yake shirin yi.
Mun dawo gida tare da Mama kamar yadda muka saba a gidan Momy muka wuni sannan muka wuce gida. A ranar Hamma yai min ba zata da wani form na makarantar koyon girki da ke nan cikin sokoto, ni ban taba sanin cewar akwai wata makaranta ta koyon girki ba na sai yau ashe abun na manya ne wai har certificate suke badawa ga wanenda aka koya musu suka iya. Babban abun jindadi daya fada min cewar sati mai zuwa zan fara zuwa domin yayi magana da malamar har ya kai mata hotona da sunana da duk wani abun daya shafe ni. Na jidadin sosai da yai wannan tunanin ni kaina na san akwai abubuwa da yawa da ban sani ba kuma ban iya ba ta fannin girki abunka da wacce bata saba ba hasali ma ba ya na ke ba a can baya sai idan an samu ganima, wacan lokacin taliya ce muke ci sai kanzo da shimkafa idan ta yi afki. Sai dai an san shiga wannan makaratantar koyon girkin zai taimaka min sosai.
Chapter 138 · 0% Book details