← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 117 OF 143

Sashe 117

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Wani irin sama yake da kafafuwansa yana boxing da hannu kamar wani karamin yaro, sai kuma ya sauko saman gadon ya nufo ni da wata irin far'a ya daga ni sama yana juyawa da ni, kamin ya rumgume.

“Oh Allah na”

Ya fada yana matseni har ina jin zafin matsar saboda yadda ya rike ni da karfi.

“Aliyu minene?”

Be bani amsa ba, ya sake ni ya fadi yana sujada, sai kuma ya dago ya ya rike ni yana ta kallon fuskata murmushi ya gama cika masa fuska, hade bakina yai da na shi ya fara min abunda ya saba wato kiss sannan kuma ya cire bakin ya daga kansa kama.

“Wayyo Allah na, baby ban san abunda zan yi ba yau, kar na haukace”

Har lokacin da yai wannan maganar kansa a sama yake yana kokarin maida ni kirjinsa ya rungume. Ni dai sam ban gane dalilin wannan farincikin ba, da farko ganin layin biyu yasa na tsorata na fara tunanin ko dai ina da wani ciwon ne sai dai yadd Aliyu yake far'a yasa na daina zargin ciwo sai dai kuma ban kawowa raina komai ba, sai mamaki kawai na ke.

“Baby i love you, I love you Tomorrow, i love you everyday, i love you so so very much”

Na san abunda I love you, da everyday da tomorrow take nufi, kuma na jidadin furtasu a gareni da yai hakan yasa ni na rumgumeshi da duka hannayena, ina jin kamar nima na fada masa haka kuma ina jin kunya. Ji nai ya dago kaina yana ya sumbatar ko'ina a fuskata da jiki kamar mahaukaci sai kuma ya sake rumgume, sake ni ya sake yi fara rawa a gurin yana jujjuyawa kamar wani mace, sai kuma ya rikoni yana cilastani ni ma nai rawar.

“Very Very soon Baby za ki zama uwar Baby”

Ya fada yana rike da fuskata har da wani turo min bakinsa yake kamar nai yi yarinya karama magana da zolaya.
Uwar baby kuma ban fahimce shi ba.

“Kamar ya”

Juyar da ni yai ya zamana bayana ne a kirjinsa sai ya saka dayan hannunsa yana shafa cikina.

“Kamar haka, idan kin haihu”

Zaro ido nai sai yanzu na gane komai barobaro da sauri ya juyo.

“Ina ciki kenan?”

Juyar da ni yai ya rungume.

“Muna da ciki dai Baby not just you, ko ma na ce ina da ciki Baby i love you”

Ya fada saitin kunnena. Sai na fashe da kuka.

“Aa yanzu kowa sai ya san abunda ya faru ko? Idan aka gan ni da ciki”

“Daman ai an san dole wani abun zai faru”

“Amman dai akwai kunya kuma ciki da wahala”

“Ba wani wahala, kunya kuma ai tunda kika yarda kika zauna gidan miji ta wuce”

Ban san dalilin rashin jindadin cikin ba, sai ma tsoro daya kama ni yo ni ya ma zan yi na haihu? Kuka na fara bana wasa ba tun yana rarrashina a hankali har abun ya koma bashi tsoro.

“Haba Babyn wannan fa abun farinciki ne, wannan shekarar ina cikin ta tara da aure amman ban samu haihuwa ba sai yanzu, Momy Mama Fulani Abbah Daddyn da duk family and friends da sisters idan suka ji dadi za su ji kuma su so ki sosai”

“A a nidai ba yanzu ba nidai bana ma so gaba daya”

Zaunar da ni nai saman gadon ya zuba min ido yana ta kallona.

“Dan girman Allah Babyna ki daina kukan nan, kar kukan ya cutar da abunda ke cikinki”

“Ba zan iya iya kallon kowa ba idan nai ciki, kuma ba zan iya haihuwa ba”

“Ciki ai kin riga kin yi, yi hakuri ba za a sake wani cikin ba”

“Da gaske?”

Dariya yai ya gyada min kai. Sannan na sausauta kuka shi kuma ya tashi yaje debo min ruwa. Yana fita na daga rigata na leka cikina sa nai sauri na rufe.

ALIYU POV.

Ya sauko downstairs wayarsa a hannunsa yana kiran Nasir, wannan karon be jira Nasir ya fara magana ba kamar yadda ya saba yana kiran daukar kiran Aliyu ya ce

“Congratulations to us na kuma zama Daddy nima na yi ajiya a cikin Ayusher”

“Wowooooooooooooo Aliyu are you serious? Oh my God”

“Na rantse da Allah Nasir har ban san irin farincikin da zan yi ba, na rasa abunda zan yi Wallahi ji na ke kamar na hadeye Ayusher a yau”

“Wannan abun murna ne a garemu gaba daya ai, amman Momy ta ji da Mama Fulani?”

“Ban fadawa kowa ba sai kai, nima yanzu na ga result din”

“Ni zan yi musu albishir karka ce zaka fada musu na san baka da kunya”

“Ai na zancen kunya a nan Nasir, wane irin kunya a gurin farinciki? Ai ba wannan zancen shi dan na fada na ce tana da ciki kuma wani abun kunya ne? Ita ma yanzu ta gama kuka wai idan suna ji zata ji kunya”

“Ai kai ba saka gane ba ne saboda ka saba yin abu normal ne”

Murmushi Aliyu yai ya kashe wayar, har ga Allah shi be ga abun kunya a fadar matarsa ta yi ciki ba, shi ba duk abunda ya san idan ya aikata ba haramun yai ba to be ga abun jin kunya a ciki ba, da dai zina ya aikata ko wani alfasha shine abun jin kunya, domin shi ya fi dacewa ka ji kunyar Ubangijinka sama da na kowa. Freezer ya bude ya dauko ruwan gora ya zuba sai da ya sha dan ya ji yanayin sanyinsu kar su cutar da abun cikinta sannan ya sirka da wasu ruwan sai ya dauko kofin ya dawo dakin da take. Inda ya barta a nan ya same ta zaune da kansa ya kai mata ruwan a baki yana bata a hankali har ta sha rabin kofin sannan ya aje ya zauna kusa da ita ya zuba mata ido. Be san abunda zai mata ba, rumgumatar ba zai wadatar da shi ba, kallonta ba zai wadatar da shi ba, saurarenta ko yi mata wani abu ba zai wadatar da shi ba, yana jin cewar hadeye ta kawai zai yi ta zauna tana cikin cikinsa ita da abunda ke cikinta sannan hankalinsa ya kwanta sai dai kuma babu wannan damar ya rasa inda zai sakata tsabar farinciki.
Haka yai zaune ya sakata a gaba har aka kira sallah la'asar sannan ya sumbaci goshin nata da cikin ya fita zuwa masallaci, daga masallacin ya wuce restaurant ya siyo musu abinci, ya so ya kira ya tambaye ta abunda take so amman babu yadda zai yi tunda bata da waya. After restaurant ya wuce wani babban shago ya siyo mata sabon phone mai tsada wacce ake yayi sannan na nufo gida, ko da ya shigo ya ji motsinta a kitchen sai ya nufi kitchen din kai tsaye taliyar indomie ya tarar tana zubawa a plate tana murmushi.

“Yunwa na ke ji sosai shi ne na dafa indomie”

Ta fada masa ganin ya tsaya yana kallonta da murmushi.

“Wow yau Gimbiyata ta yi aiki da kanta bari na dan dana na ji, ashe kin iya girki ko?”

“Eh na iya tuwo na iya dafaduka na iya dafa taliya na iya sararafa kanzo na iya shimkafa da miya kuma na iya da wake, amman ban iya amfani da wacan abun ba sai na daka a turmi”

“Wow amman dai ai ba sai kin yi aiki da yawa haka ba”

Ya karasa kusa da ita yana rike da ledodin a hannunsa. Fork ta dauko ta saka ya debo taliyar sai ya busa masa a bakinta sai da huce sannan ta kai masa a baki, luma daya ya rumtse ido saboda wani azababen yaji da ya ji, da sauri ya aje ledodin hannunsa ya dauke plate din.

“Wallahi ba za ki ci wannan abincin ba”

“Mi yai?”

“Wannan uban ya jin?”

“Ji nai ina son ya ji shine an cika kadan”

“Wannan cikin be wani kwari ba za ki ce za ki ci wannan yajin, noooooo ga wani abincin na siyo miki ai zo mu ci tare”

Ta mairairaice fuska.

“Haba Aliyu ina so Wallahi”

“Haba Baby ki tausaya min mana”

Aje plate din yai gefe ya bude dayar ledar mai waya ya dauko ya mika mata.

“Ga waya ke ma ki fara bugawa kina daukar hoto”

Ba shiri da zaro ido ta karbi wayar da sauri da daka wani irin tsalle kamin da dire yai saurin cabeta.

“Ke yanzu fa ba ke kadai kike ba, ki daina irin wannan abun”

Ina bata ma jin me yake fada sai ihu take ya rumgume shi sabar farinciki har da yi masa kiss a fuska.

“Na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na gode na”
Chapter 117 · 0% Book details