← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 124 OF 143

Sashe 124

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da na mike tsaye sannan ta kalli inda na ke sai kuma ta dauke kai, ni kuma nai ficewata ba tare da na sake ce mata komai ba, a harabar gidan na ga karin motoci har biyu ba zan iya shaidar motar waye da waye a wajen ba, amman dai na san bayan motocin da suke fake a cikin gidan sai kuma ta Aliyu da Nasir yanzu kuma wasu ne har biyu irin mayan motocin nan na alfarma. Littafin nan na kudi ne, idan kin ganshi waje na sata ne. Bangaren Ammy na nufa kai tsaye daman na fi zargin bakin ko can suka zo tunda ban ga kowa ya shigo gurin Mama Fulani ba. A lokacin da na shiga falon Ammy sai na tarar babu kowa a ciki, kamar yadda na barta dazun zaune da Mama wato Nana da Aliyu ya lakanta min sunan Mama a saman nata na Nana da na ke kiranta da shi. Zaunawa nai na maida hankalina gurin tv dake kunne. Ba jimawa Ammy ta fito daga bandakin da ke falon tana kallona ta saki murmushi.

“Yanzu nan kuwa Hajiya ta fita”

“Ina suka je?”

“Suna bangaren Abbah, ya zo da wasu baki shine ya kirata”

“Ok”

Na fada ina ta tunanin ko su waye ne. Sai ga Aliyu ya shigo falon rike da line a hannunsa.

“Ina wayarki”

“Gata nan”

Na ciro ta daga koguna na mika masa ni na ma manta da wayar sai yanzu da yai maganar, tun a lokacin da na nunawa Mama ita na biyo ta ajikin gudun kar na manta da ita ban tuna ba sai yanzu.

“Ina kika saka ta?”

Ya tambaya yana min wani kallo kamar na mamaki ba tare da ya karbi wayar ba, kamar dai ya manta cewar ba daga ni sai shi ne a falon ba Ammy ma tana nan.

“Aliyu dan ta saka waya a jiki sai ya zama laifi?”

Cewar Ammy tana murmushi shi ma murmushin yai sai dai ba sosai ya karbi wayar ya bude yana saka Sim wani dadi ne ya lullube ni ganin layi ne zai saka min hakan na nufi zan iya kira kuma a kirani.

“Ta so muje”

Tashi nai na bi bayansa yana gaba ina biye har muka isa bangaren Abbah, tun kamin mu shiga na fara jiyo muryar wasu na watso turanci kamar turawa sai hayani suke a falon har da muryar mace. Dan tsayawa nai na janyo rigar Aliyu.

“Su wanene?”

Na tambaya kadan kadan kar su ji.

“Idon ki za su cire”

Ya fada min babu alamar wasa a fuskarsa kamar da gaske haka din ne. Sannan ya tura kofar falon ya shiga, ni ma na shiga da dan tsoro. Dukansu suna sanye da suit mata biyu maza hudu mace dayar tana sanye da karamin Hijab a wuyanta, dayar kuma kanta a sake ta saka jam gashi mazan biyu kuma suna rike da abun rubutu.

“Ke ce Ataa?”

Kabilar ta fada da hausa sai na gyada mata kai. Ina ta bin Aliyu duk inda yai har na zauna a inda ya zauna.

“Bude ba ki za ki yi ki mana magana, daga sama aka turo mu nan”

“Ni ce”

“Miye sunanki na gaskiya?”

“Aisha”

“Ya kike da wannan?”

“Mamana ce”

“Ita ta haife ki?”

“Eh”

“Mamanki tana da wani rashin lafiya ne ko wani ciwo?”

“Eh bata da koda daya”

“Garin ya?”

“Wani likita ne ya cire mata”

“Ya akai ya kai cire mata kodar kuma ya akai kika tabbatar cewar bata da koda?”

A take na fara zana musu yadda komai ya faru. Har suka fara tambayana kamaninsa na bayyana musu da kuma inda asibitinsa take. Namijin ya nuna min hoton group din mutane a guri daya ya ce na nuna masa shi sai na nuna fuskarsa.

“Za mu mika wannan statement din aga kungiyar likitoci reahen jiyar sokoto, su fara na su bincike kamin ya iso zuwa nan, and After that za mu dauki ke mu kai ki asibiti a sake miki hoto domin tabbatarwa”

Ta karasa tana kallon Nana. Sai ta gyada mata kai. Sannan ta juya sukai magana da sunan su sai kuma suka mana sallama suka fice tare da Abbah ni sai a lokacin ma na ke lura da Nasir ashe har da shi yana zaune a falo har ma dayan jikan Mai Martaba wanda suka zo da shi. Aliyu da Nasir suka bi bayan Abbah, aka bar mu ni da Mama murmushi na gani a fuskarta na san ba zai wuce na jindadi ba kamar yadda nima na na jidadin ganin cewar za a kwato mata hakkinta, na yi zaton maganar zata fara min sai na ji ta ce.

“Mai Martaba ya ce mu shirya duk abunda ya kamata a yau, gobe da safe za mu wuce Lagos daga can za mu tafi gida”

“Waya fada wa”

“Yusuf ya fada min lokacin da suka shigo, kuma ina fatar kin fadawa mijinki”

“Eh na fada masa amman yanzu zan kara masa maganar”

“Ina jindadi sosai zan ki ga iyalina ni ma kuma zan sadu da su da kuma mahaifiyata bayan tsawon lokaci, na jidadi sosai, na jidadi marar misaltuwa kuma ina cikin jindadin”

Ta fada ya yaren buzanci idon na cika da kwalla.

RAHMA POV.

A hankali numfashinta yake shiga jikinta, idonta kulle hancinta kuma manne da oxygen, ga wani katon tukuyar shakar numfashi da ke aje gefenta tare da wata nu'urar da ke taimaka mata tai numfashin, idonta a rufe suke amman hawaye masu zafi ne suke gangarowa daga cikin idonta da ke rufe zuwa gefen ko wane kuncin fuskarta.
Mommynta tana zaune gefenta idonta ya sumbura sosai saboda kuka gaba daya ta fita daga hayyacinta kamar ita ce marar lafiyar ba Rahma ba. Samun koda yanzu abu ne mai wahala, domin sun saka nema har yanzu ba a dace ba, balle kuma yanzu da likitocin suka tabbatar musu da samun ta a dole matukar suna son yar su a raye cikin koshin lafiya.
Ba zata iya kallon yarta ta mutu ba, bayan tsawon lokacin data dauka tana jinya kuma tana son Rahma a cikin yayanta fiye da kowa, matukar aka kwana biyu ba a samu ba zata yarda a cire nata daya a dasawa Rahma ko da ko ita zata rasa ranta ne ko kuma lafiyarta, ba zata iya kallon Rahma ta bar duniya ba saboda rashin abunda zata iya samar mata ba, tunaninta da bakincikin mutuwar Rahma idan har ta Allah ta kasance ta san ita ma ba zai barta ta rayu ba. Da wannan kara kawai ta bata kodarta daya idan har zai yi, ita kanta ta san abubuwa sun yi ma Rahma yawa a yanzu, samun cikin Ataa, barinta da Aliyu yai ya auri wata, ga Kuma bullowar wannan lamarin na kakanta Ataa wanda ya zama karkashin inuwarsa dukansu suke rayuwa, ta alfahari da bugun gaba ta kare.

*Ina mata son rage kiba? Ina mazan da kiba ta hana su sukuni? Ina masu jikin yai kyau kamar na yarinya? Ina masu fama da kujera ko wani ta bo a fuska? Ina masu fama da hawan jini? Masu diabetic? Ag cera an gwada yayi an tantance ingancin babu shakku ko kadan. AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.*
*Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
*******
55

Ba mu koma gida ba sai dare, Nana ta yi ta nanata min lokacin da za mu tafi kamar yadda Mai Martaba ya fada mata, a hanya Aliyu ya tsaya ya siya mana ayaba kankana sannan muka isa gida. Sai ya ya faka motarsa sannan na saki hannunsa na bude motar kamin na fito har ya zagoyo gefen da na ke ya karasa bude min ganbun motar. A hankali na sauko ina takawa yana rike da hannuna dayan hannunsa kuma rike da ledar da muka siyo ayaba.

“Mama ta ce nai tuna maka zancen tafiyar mu fa”

Be ce min komai ba, har muka shiga falon sai ya zauna saman kujera ya janyo hannun na zauna saman jikinsa ya rumgume.

“Na sani ai, tare za mu tafi”

“Da gaske?”

Na fada cike da jindadi ina wara ido sai ya gyada min kai, rumgume shi nai na lafe a jikinsa kamar wata kyanwa yana shafa bayana a hankali. Mun dade a haka kamin mu koma daki, duk wani abu daya san zamu bukace shi a cikin daren ya hada mana shi, jaka daya ya hada mana kayanmu kamar yadda yai mana a wacan karon da za mu tafi Las Vegas, misalin tara da rabi Nasir ya kawo masa maganin da aka rubutu asibiti, sun dade suna magana waje kamin su yi sallama ya dawo ciki.

A gado daya muka kwana kamar yadda muka saba ina cikin kirjinsa har sai da yunwar da dare ta fara damuna na fito kitchen na dora indomie a cikin daren nan domin duk wani abu da ke nan bana sha'awar cinsa ba, ciki kuwa har da kayan marmarin dana ci jiya. Ina cikin zuba magi Aliyu ya shigo kitchen din, hannayensa ya dora a kafata taya ta tayani duba indomie a haka har ta dafu muka ci tare sai ya fini cin ma.

“Ashe kai ma kana jin yunwar”

“Ba dole na ji yunwa ba”

“Ba ka ci abinci ba a gidan Mama Fulani?”

“Na ci”
Chapter 124 · 0% Book details