← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 143

Sashe 18

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na gyada masa kai cike da fahimtar inda manufarsa ta dosa, ba sai ya fada min na fahimci dan iska ne, ashe abunda suke da matan da suke fita dasu da dare kenan.
Yadda ya fada haka ya nufoto ni da dare guraren karfe goma sha biyu ya bude cell din wai na fito, ni ko na ki yarda na fito din, da ya shigo ya jani da karfi sai na fasa masa kuka ina ta masa ihu kamar zai sace ni a dole ta saka ya kyaleni yai tafiyarsa.
A haka na kwana hudu a cikin cell babu wanda ya zo belina, abinci kuwa sai idan polisawan sun ci sun rage su ba ni raguwar ko kuma mutane za da ke cell din idan an kawo musu sun ci sun koshi sai su ba ni ragowar. A cikin kwana biyu Allah ya hada jinina da daya daga cikin yan matan cell din, na dauke ta kamar yaya ita kuma ta rike ni tamkar kanwarta kasancewar ta girme ni nesa ba kusa ba. Bata fada min dalilinta na zuwa cell din ba amman na fahimci kamar shaye-shaye take har aka kawo ta nan, da fira tai mana dadi take tambayata dalilin zuwana gurin na fada mata sai ta tausaya min sosai. Ita ce ta taimaka min ta fitar da ni daga cell a lokacin da aka zo belinta sai akai belinmu mu biyu ni da ita.

Ranar da na fito daga cell din har iskar sai na ji ta badan ina ra jina kamar mai hanci, abu ga marasa shi, daga station din zuwa uduth akwai dan karen nisa amman haka na taka da kafa idan na gaji sai na tsaya na hutu har na isa cikin asibitin, ban san time din da na isa ba, sai dai da naje sai suka hanani shiga, a gurin na zauna har hudu tai sannan na shiga ciki, gurin da na san na bar Nana na nufa sai na samu babu ita a gurin gadon ma har an dora wata, ban tambayi kowa ina take ba na juyo na kamo hanyar Clapperto ina kuka. A iya tunani Nana ta rasu, idan ma ta rasu ina suka kai gawarta? Kangon gidan na nufo sai na tarar an saka kwano an zagaye shi an rufe ruf ba ta inda mutum zai iya shiga, a gurin na zauna nai ta rare kukana sai da nai mai isata, ban dauki wannan abun komai ba, face kaddara da kuma jarabawar rayuwa wacce ko waji dan adam yake fuskanta sai dai kowa da irin tasa, amman a iya ganina da jina ban tana ganin wanda ya shiga matsanaiciyar rayuwar da na shiga ba, kullum abun gaba yake ba baya ba, idan na natsu ina tunani sai na ga ban kashe kowa ba, ban hada Allah da wani ba, amman abubuwan da suke faruwa da ni kamar na kauce hanya ne, wata kila akwai wani abun da na ke ba daidai shiyasa Allah yake jarrabani, kuka nai mai isa ta sannan na tashi na doshi gidansu kawata Farida. Ina shiga ta yo kaina da gudu ta dafani.

“Ataa ina kika shiga? Mi ya same ki wannan irin ramar fa? Duk kin yi baki kamar ba ke ba”

Kasa amsa mata nai sai kawai na fashe da kuka.

“Ataa ina kika shiga? Hankali Nana duk ya tashi kullum zancen ki take”

“Nana tana nan?”

“Gata a can”

Ta nuna min wani tsohon kitchen dinsu, da gudu na nufi kitchen din ina shiga na samu Nana kwance sai kawai na fada jikinta na fashe da sabon kuka na rumgumeta kankan ina jin kamar wani zai rabani da ita. Ita kukan take ni da ita sai aka rasa mai rarrashi wani, Farida ma da ke tsaye jikin kofa tana kallon mu kuka take.

“Haba Ataa ke kuka ita kuka sai ki saka zuciyarta rauni ai”

Maganar Farida ce tasa na tsagaita kukana na share hawayena ita na saka hannuna na share mata hawayenta. Ta rame sosai wata kila ko abinci bata samu sosai ya akai ma ta bar asibitin ta dawo nan?
Ganin na daina kukan yasa Farida ta fita ta bar ni daga ni sai Nana.

“Nana ina Lukman?”

“Yana gidansa na gaskiya, sai idan Allah ya hada mu”

Wani sabon kuka na ji na cika min ido, sai tausayinta da shakuwarta da Lukman ta rufe ni, daman daga ni sai ita sai Lukman muka rage, yanzu kuma ya tafi ya bar mu mu biyu kawai.

“Ina kika je Ataa”

“Karar wannan likitan na kai gurin yan sanda akan rashin kula da ke da yai da kyau, sai ya juyar da abun a kaina suka rufe a cell sai da wata mata ta fitar da ni”

“Ranar da kika bar ni ban iya kwana cikin asibitin nan ba, sai na saci kafa da suna zuwa bandaki na gudo na dawo gida, a nan na tararda gawar dana, na nemi taimakon mutane akai masa wanka aka siya masa likkafai akai masa sallah aka je makabarta aka binnesa, a ranar mai gidan nan ya turo aka kore mu, da safe ana kewaye masa gurinsa dan kar mu sake zama, Farida ce tasa muka dawo nan ta ba ni kitchen dinsu na zauna a nan nake ta rayuwa da tunaninki, na dauka ma ke ma kin mutu kin bar ni ni kadai”

Na kama hannunta hawaye na min zuba kamar yadda ita suke mata zuba.

“Ban mutu ba Nana, kuma ba zan tafi na barki ba, kuma In-Sha-Allah za ki samu lafiya sosai, zan nema miki magani In-Sha-Allahu”

“Aa ba sai kin nema min magani ba, dawainiyar da kikai da ni ma Allah ya miki albarka, da kuciyarki kin fada cikin wata rayuwa mai tsananin wahala da sarkakiya, kina fuskantar kalubale kala kala na rayuwa”

“Idan ban nema miki lafiya Nana wa zan nemawa? Ba ni da wani wanda ya fiki a gurina, ganinki kawai yana sani kwanciyar hankali”

Dan murmushi tai sai ta koma ta kishingida da alama har yanzu lafiyar bata wadace ba, taya ma zata wadace bayan ba a nema mata magani ba, ba a mata maganin daya dace ta sha ba. Babu abunda ke zuciyata sai Allah ya isa da na ke yi ma azzalumi likitan marar imani da tausayi.
A gurin muka kwana ni da ita cikin matsuwa domin ba kitchen mai fadi ba, gashi duk ya kone saboda girkin da akai cikinsa can baya kamin su daina girki ciki, da dare Farida ta kawo mana abinci da alama ma tuwonta ne wanda zata ci ta kawo mana, dan nasan mahaifiyarta ba zata taba dauka tuwo ta ba mu ba, balle yadda ake fama da tsadar rayuwar nan.
Bayan mun gama sallah asuba, Nana ta koma bachi, ni kuma na daddaka gawayin da na shafa a fuskata, na yafa hijabina na fito ba tare da sanin kowa ba, da kafa na taka har unguwar Nasarawa, babban unguwa ce ta manyan masu kudi da yan siyasa gida gida na soma shiga ina tambayar aiki, a ganina samun aikin zai fi min bara, domin bana sha'awar baran tun da na rasa dan'uwana Lukman, amman aikin zan iya samun abinci har na kawo wa Nana.
A haka har na fada wani babban gida mai cike da fulawoyi da manyan motoci, da fari mai gadin gidan hana ni shiga yai, bayan na juyo sai kuma na ji ya kirani.

“Ke zo ana kiranki”

Da sauri na dawo na shiga cikin gidan, shi ya nuna min kofar har na isa gaban kofar na tsaya ina ta kallon inda mutane za su fito. Zuwa can na ga wata mace ta fito wacce kudi da jindadi da rayuwar hutu suka gama bayyana kansu a jikinta. Tana kallona sai ta ya mutsa fuska.

“Me kike so?”

“Aiki”

Na Fada da sauri, sai ta kalli sama da kasa ta dan tabe baki ta juya cikin falon kamar tana magana da wani, bayan yan mintuna mutumen da na taba fasawa mota kuma mutumen da ya taba jefar da rigarsa saboda na taba shi ya fito cikin farar shadda riga da wando, fuskarsa kamar ta ranar nan babu yabo ba fallasa, sai kwarjini da haifa, kallo daya nai masa na sadda kaina kasa, yau kan ban ji tsoronsa kamar yadda na saba ji ba, wata kila saboda uzurin da ke gaba ne, ko kuma dan na kawo kaina a gidansa ne.

“Look at her face, wannan ai ta cika kazanta”

Yai magana kamar ba shi ba, ashe dai yana magana mai sauti har ta fito haka. Cikin sauri da rawar jiki na ce.

“Zan wanke wallahi zan gyara ko a nan aka ba ni ruwa wankewa zan yi”

“Nawa ake biyanki a wata?”

“Ban taba yin aiki ba”

“Ba ki taba ba?”

Matar ta tambaya tana kwantawa jikin mijin na ta, shi kuma ya rumgume yana mata magana kadan-kadan, ban san mi ya ce mata ba sai naga ta dago ta kalleni.

“Zan a baki dubu 8000 a wata hakan ya miki?”

“Ya min amman ina rokon ki fara bani kudin yanzu”

“Saboda mi? Kin taba ganin inda akai haka?”

“Mahaifiyata bata da lafiya, ina son na siya mata magani da abinci, ni kuma na miki alkawarin yin aikin har wata ya kare”

“Na baki kudi ki gudu?”

“Kin fi karfin dubu takwas Hajiya, kuma ni miye ribata idan kin ba ni kudin na gudu? Idan ban miki aikin ba, zan biyaki kudin a lahira, mahaifiyata ce bata jindadi ki taimaka min da girman Allah”

Na fada cikin roko da neman alfarma, amman matar nan ta murje ido ta ce ita bata yarda ba, ba za ta ba ni kudi na gudu ba.

“Ina ne gidanku ina iyayenki suke?”

Na kwatanta mata tare da fada mata cewar ba mu da gida wani guri ne mike rabe.

“Dear Za mu bata kudin, lafiya tana da muhimmanci sosai, naga hakan tun a kan ki, idan ta gudu da kudin ta yi wa kanta”

Mijinta ne yai wannan maganar yana yana shafa bayanta, da alama yana son matarsa sosai. Ita kuma ta lake kafada wai bata yarda ba, ita ba za a bani kudin ba.
Chapter 18 · 0% Book details