← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 110 OF 143

Sashe 110

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na yi mamaki sosai jin cewar abubuwa da dama ba irin na kasata ba ne, wasu kuma dole sai an canja mutanen da yanayin ma ba daya ba.
    Kwanan mu biyu a hotel din muna huga gajiya sannan muka fara fita yana nuna min wasu abubuwan da kuma wasu guraren, har da gurin shakatawa ya kai da gurin da ake hawan abubuwan wasanni kala kala, sai dai fa komai sai an biya kuma ba a jefar da abu kasa sai dai ka kasa a inda aka tanada dan zuba shara
Sannan babu mata masu saka manyan Hijab ko gyale kowa ka ganinda karamin mayafi yake indan musulmi ne wasu ma musulman ne amman ba mayafa haka suke ta yawa, na ga bakar fata da dama a garin. Ba cikin Los Vegas kawai muka yi yawo ba, har ma da wasu guraren da ke kusa da ita, idan Aliyu ya nuna min wani gurin sai ya min browsing a wayarsa ya fada min gurin da irin muhimmancinsa sannan kuma yai min hoto.
  Gaskiya tafiya mabudin ilmi na karu da abubuwa da dama na ga abubuwa da dama kuma na san wasu abubuwan da a da ban san su ba, mun ci abinci a restaurant dabam dabam, ido ya bude sosai da tafiyar kuma na jidadinta lallau idan dai haka honeymoon yake gobe ma a kara muje wata kasar dabam su ma muga abubuwansu. Tafiyar da mukai ba kadan ta karamin kaunar Aliyu ba, domin ya nuna min kulawa sosai da kauna, duk inda za mu je yana rike da hannu duk kuma wani abun da yasan idan n saka zai min kyau sai da ya siya min, idan kuma na ci har sai na ture, kullum sai ya kira min Nana da Momynsa mun gaisa Mama Fulani ce kawai be yaba ba ni mun gaisa ba, I love you shine furuncinsa a gareni kullum, ko numfashi nai da karfi sai ya tambaya idan lafiya nake, abun har mamaki yake ba kamar ba Aliyu ba ashe dai waje ne wannan bazaranar take a gidan kuma yafi kowa iya tarairaya da nuna kulawa, sai dai idan abun nashi ya motsa na kin magana sai ya share ni nai ta tambayarsa abu sai dai yai min murmushi ko ya ja kunne na ko hanci ya ce nai shiru idan mun koma gida zai fada min. Satin mu hudu a can sam ko mamari komawa gida bana yi domin kullum muka fita wani gurin dabam yake kai ni mai nishadi da shakatawa idan ma ta kama wani lokacin ba za mu kwana a hotel din ba sai dai mu kwana a wata. Ranar da za mu bar Los Vegas mu koma gida sai da na ji kamar nai kuka domin na fara sabawa da garin da ba nawa ba, Aliyu yana ta rarashin na yana fada min wata rana ai za mu dawo.

RAHMA POV

kowa yana ta hada hadar zuwa dinner da za'ayi a yau ta kanwarta Amra ita kan tana makota gidan su Lubna ta boye kanta abun duniya ya isheta, daman tun da ta ji zancen Aliyu ya tafi Honeymoon da Ataa sai ta ji gaba daya kamar bata da lafiya a jikinta yar walwalar da take sai ta daina. Kullum tana cikin damuwa da bakinciki kuka kan babu ranar da bata yinsa, tun tana ganin laifin Aliyu har ta koma dorawa Mommynta laifi a ganinta da bata yi mahaifiyarsa wannan cin mutuncin ba da yanzu be kara auren ba, kuma da yanzu tana can dakinta. Wannan tunanin shi ya hanata sakewa kuma ya hanata sukuni balle har tai murna ko walwala a cikin yan'uwanta da yan biki.

“Rahma kina ta sakawa kanki damuwa dubi ki ga yadda kika koma, kowa yana can yanashirin zuwa dinner ke kina nan kin ware kanki dabam kina ta saka damuwa a ranki saboda da namiji”

Rahma ta kalli Lubna wacce ta dafata tana wannan maganar.

“Lubna idan ban yi kuka na yi damuwa ba dariya kike son nai na yi murna Aliyu yayi aure? Ina son miji taya zan jure ganinsa da wata?”

Ta fada cikin kuka.

“Indai kina son mijinki Rahma dole ki yi hakuri ki koma dakinki, ba dole sai kin tsaya ya zo bikonki tunda dai kin san laifi na ki ne, kin dawo gida kin zauna kina fushi kin bar shi can shi kadai kuma mahaifiyarki ta hana shi ke lokacin da mahaifiyarshi ta zo bikonki kuma ki yi tsammani ba zai yi fushi ba? Haba dai ai Wallahi dole ma ne mahaifiyarsa ta saka ya kara aure, ni dai inda nake ganin rashin kyautawarsa na kin dawowa yai bikonki gaskiya be kyauta ba, sai dai idan aka aunanda tafiyarki Dubai ba ki fada masa ba sai a ga kamar hakan da yai ya dace”

“Ki daina tuna min abunda ya riga ya faru, ki ba ni shawarar abunda zan yi”

“Shawara kawai ki koma dakinki, ko da iyayenki sun nuna miki ba haka ba ki ce ke dai kina son mijinki kuma kina son ki koma dakinki, amman zamanki a nan ai matsala ce kawai domin za ki jawa kanki wata matsalar ne wata kila ma ki janyo ciwon ya dawo gashi har yanzu ba a samu kodar ba”

Shiru tai na wani lokaci sannan ya hade ya wu ta ce.

“Zan koma, idan an daura auren Amra gobe hankalin Daddyn ya kwanta zan masa magana, na san yanzu hankalinsa ba kwance yake ba saboda zuwan Mai Martaba Sarkin Agadaz”

Lubna ta wara ido, domin ita ma tana jin labarinsa saboda tashen kudi da siyen kamfaninika da yake.

“Laa ya zo? Ashe dai da gaske zai zo”

Rahma ta share hawayen.

“Eh ai bashi da girman kai, daman Daddy ya ce zai zo domin shi ya bawa walincin aurar da Amra, kuma daman yana bukatar zuwa da kansa yi ma Daddy jajayen rasa babban shopping mall dinsa da kuma duba wasu abubuwam tun yau ya zo ance yana Hotel yana hutawa sai gobe zai je daurin aure idan an daura zai wuce Abuja ya duba wasu abubuwan sannan yaje jigawa da Lagos sai kuma ya wuce, tun da yamma ma Mommy ta shirya masa abubuwa taje ita da Daddyn suka kai masa, hankalin Daddyn yanzu yana can gurinsa amman na san da zarar an daura auren ya wuce Abuja indai ba tare da Daddy za su tafi ba zan samu ganinsa hankali kwance idan ma da shi yaje ai dole Daddyn zai dawo sai na fada musu cewar ni ina son komawa dakina”

“Ba dole sai Daddy kai tsaye ba, idan dai hankali ya kwanta sarkin ya tafi an gama bikin sai ki samu Mommynki a daki ki fada mata ita zata fadawa Daddynku ai”

“Amman kara na same shi ni da kaina dan ya tabbatar da gaske na ke, saboda Mommy zata iya kin fada masa, tunda bata son komawar tawa”

“Ke dai ki gwada idan ka bata fada masa ba ai sai ki same shi da kanki ke ki fada masa daga baya”

Ta gyada kai.

“Zan yi hakan In-Sha-Allah na gode sosai Lubna”

“Karki damu,  kuma idan kin koma ki nuna mata ruwa ba sa'an kwado ba ne, kin dai san ba lafiya ce ta ishe ki ba Wallahi ko bi tai kusa da ke ki fadi ki ce ta tureki dole ya daukar mata mataki ki tai mata bandar kasa”

“Ai ba sai kin fada min wannan ba, ke dai na koma gidan kawai tana yadda ake kula da mijin tana wata kazamarta komai bata iya ba, sai ya san banbancina da ita ai dole”

“Ina son ki kawata, ai kema na san baki da dama kina babbar mace karamar yarinya ta ce zata zubar miki da aji? No-no yanzu dai tashi muje gida ki shirya muje dinner ki cire komai a ranki yanzu mun samu mafita”

Murmushin jindadi Rahma tai ta mike tsaye tana dora mayafinta a wuyanta, tare da kallon kawarta.

“Bari na je na shirya ke ma ki shirya sai na zo mu tafi domin ni motata tana can gurin hadahadar biki ana yi da ita”

“Ba matsala bari nima na shirya”

Daga haka itama ta mike tsaye ya rako Rahma har gurin gate din gidansu suna ta kara tattaunawa kan lamarin kamin Rahma ta wuce gidansu domin shiryawa ita ma Lubna ta koma gida.

ATAA POV.

Kusan karfe ukun dare muka baro can kayan da muka tafi da su da zamu dawo sai mu dawo da jaka biyu, domin a lokacin da zamu je tufafina da na shi a jaka daya ya hade su, tsarabar da mukai a can kuma ta zama a dayar jaka ya zama mun dawo da jaka biyu a amaimakon daya da muka je da ita.
A lagos muka sauka kamar yadda muka tashi a can, na yi zaton ko Aliyu zai bari sai idan mun huta a lagos din sannan mu wuce Abuja ashe duka rana daya ne banbancin awa biyu ne kawai na jiran da mukai, tun da muka sauka a Abuja na soma jin kamar ba ni da lafiya kaina sai ciwo yake jikina yai zafi wata kila saboda canjin yanayi ne domin yanayin can ya fi na nan dadi sa sanyi, wata kila kuma saboda gajiya ne domin ban saba irin wannan tafiyar ba.
Yamma ta yi a nan domin karfe uku ne har yan mintuna a nan Abuja. Muna sauka airport Aliyu ya kira Nasir ya fada masa, ba bata lokaci sai gashi ya zo da motarsa ya dauke mu. Dan kwantawa nai a kujerar baya wai ko zan samu walwala da sakewa kamin mu isa gida, amman sai karuwa na ke jin abun na yi sanyin ac motar ya sa ina jinsa ba dadi kamar nai amai, yawuna ma daker na ke iya hadewa.
Lokaci lokaci Aliyu ya ke dan waigo baya ya kalleni sai na masa murmushi ina kokarin nuna kamar bana jin komai amman hakan be hana shi ya gane ba.

“Baby za muje gurin Mama idan mun huta a can sai mu wuce gidanmu kin ji?”

Na ji ba dadi domin ba son ganin Mama Fulani na ke ba domin bana sakewa da ita kuma na san ba so na take ba har yanzu.
Chapter 110 · 0% Book details