Sashe 132
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
“Ita ta rubuta ta, a lokacin da ka kirata bata iya magana ta miko min, na tambayeta ta waye tai min alamu da kai zan bawa”
Kallon takadar Aliyu ya rika yi na few minutes kamin ya kai hannu ya karba jikinsa na ta rawa. Sannan ya nufi motar ya shiga, Muhseen ne ke tukawa har suka isa gida sai taba takardar yake ya kasa budewa. A can gurin Momy ma an cika da mutane yan'uwan Daddyn da Momy, har Daddyn da kansa da wasu abokansa da suke kusa da kusa suna tare, har da yan'uwan Mama Fulani da suke yola wadanda suka zo ta jirgi. duk wanda ke gurin tausayin Aliyu yake, sai da magariba Mama Fulani ta iso ita da su Maryam da Ammy gaba daya gidan aka kwashe ba a baro kowa ba.
After Sallah isha'i Aliyu ya shiga bangarensa da ke cikin gidan ya kulle kansa a cikin dakin ya bude takardar cike da fargaba ya fara karantawa.
_Zaka karanta wasikar nan ne wata kila, bayan ba raina domin na san ba sakan cewa ina asibiti ba, da farko zan fara taya ka murnar samun haihuwa da kai, kuma nai maka godiya na rufa min asiri da kai da hakurin zama da ni na tsawon lokaci, ina jin a jiki kamar ba zan rayu ba wani lokaci ba, amman ina rokon yafiyarka kuma ka nema min yafiyar Ataa da yafiyar Momy da duk wani wanda ka san na taba alaka da shi, ka nuna min soyayyar gaskiya Aliyu ta hanyar yi min addu'a bayan raina, Allah ya hada fuskokin mu a aljanna. I love you so much ina maka fatar alheri a sabuwar rayuwar da ka fara da Ataa, na san ka nuna min so, amman ni yanzu tawa ta kare, ka yafe min Aliyu kuma ka yafe wa mahaifiyata so na ne ya saka ta aikata maka komai, ka yi hakuri na san kana so na amman babu wanda ya iya kaucewa mutuwa, tarin dukiya ko lafiya bata amfani mai ita ba matukar mutuwa ta kusance shi, ka yafe min Aliyu_
Fuskarsa shakaf da hawaye ya gama karanta wasikar. Kansa kamar zai bare idonsa ya kumburo kamar ba na shi ba.
“Na yafe miki Rahma na yafe miki, Allah ma ya yafe miki”
Ya furta sannan ya mike tsaye ya shiga bandaki ya wanke fuskarsa ya fito harabar ya memi Abbah, can gefe ya koma da shi ya karbi number Mai Martaba saboda yana son kiran Ataa ya nema ma Rahma yafiyarta. Dakinsa ya dawo sai da ya fara gaisawa da Mai Martaba sannan ya gabatar masa da bukatarsa, sannan ya kashe wayar bayan Mai martaba ya tabbatar masa da za a fada mata, after like thirty minutes aka kira shi da line orange na can nijar wata bakuwar number wacce ba ta Mai Martaba ba.
Yana yin picking ya ji muryar Ataa kasa kasa kamar marar lafiya, sai da suka gaisa ya tambaye ta ko bata jindadi ne ta fada mishi lafiyarta kalau.
“Ya jikin Rahma?”
“Babyna jiki da sauki sosai ta ce a fada miki tana gaishe ki kuma na nema mata lafiyarki, tsabanin da kuka samu a baya”
Aliyu yayi kokari wajen ganin yayi magana da ita normal ba tare da muryarsa ta canja kuma ba tare da nuna akwai damuwa a tare da shi ba, sai dai kana jin muryar kasan baya cikin walwala. A maimakon Ataa ta tace ta yafe mata sai kawai ta fashe da wani kuka da cikin wayar har Aliyu ya kasa saurare ya kara wayar a kirjinsa yana hawaye.
Mutuwa....! 💔
Allah kai mana kyakkyawan karshe, Allah ka jikan Babana da Rahma😭😭😭😭💔
*AG cera ya zo domin ya temaki garkuwan jiki da kuma lafiyar jiki. Sinadari ne wanda ze magance matsaloli da dama wadanda suke hana garkuwan jiki aiki yadda ya kamata ko kuma yake rusa garkuwan jikin ita kanta.
Cututtukan zamani daban daban sun sa mutane gaba kuma magance su yana da wahala; irin ciwon Sugar, hawan jini, ciwon sanyin kashi, ciwon gabobi da sauran su. Haka ma cutukka irin wadanda suka shafi fatar jikin wadanda sun hada da kyasfi, pimples, takurewar fata, rakainuwar fata da kuma haske da kyallin fata duka ana shan AG cera kuma yana temakawa wajen magance illolin nan. Mutane masu fama da rashin karfin jiki wajen kwanciya da iyali da kuma mata masu fama da yawan ciwon mara lokacin al'ada ta karshen wata suma baa bar su a baya ba. A takaice dai AG Cera yana temakawa wajen magance cuttukka daban daban wadan ke damun mutum. Domin karin bayani ku tuntuni mu a wannan number +60167474649 ko kuma ku ziyarci shafin mu http://agnutritioninternational.com.*
Kuka na ke sosai jikina na raya min cewar Rahma ta rasu daman tun a lokacin da ya tafi na ke jin ba dadi, yanayin yadda na ji muryarsa ma na san ba lafiya ba, domin alamu ya nuna ba ya cikin walwala duk dai ban san ainahin abunda yake damunsa ba, sai dai jin cewar Rahma na neman yafiyata na san mutuwa ce kadai zata saka ta neman yafiyata, idan kuma ba haka ba, wata kila kuma Aliyun ne ya nema mata da kansa saboda ta mutu.
“Babyna kukan ya isa haka”
“Hamma ba a boyon mutuwa, idan ma ta mutu da gaske ba zan iya dawowa da ita ba, kuka ba ya dawo da wanda aka rasa, da yana dawowa da ya dawo min da Babana da Lukman, amman duka na rasa su kuma kuka da bakinciki be dawo da su ba, zan yi kuka saboda tausayinta ne da kuma kai”
“Bana son kukan ko tunanin ya janyo miki wata matsala, ke kadai kika rage min a yanzu sai abunda yake cikinki, idan na kara wani rashi ban san ya zan yi ba, rashi akwai ciwo sosai gashi ba zaka iya dawowa da wanda ka rasa din ba, akwai ciwo sosai ka rasa wani abun da kake so a lokacin da kake tsananin bukatarsa, akwai ciwo rabuwa da abokin rayuwa da ka shirya yin rayuwa da shi”
Hannu na kai na share hawayen fuskata, na san yadda Hamma yake ji saboda be taba rasa kowa ba a rayuwarsa sai yau, mahaifiyarsa mahaifinsa duka suna raye, wani karin gatan ma sai Allah ya kara masa da Mama Fulani da Abbah duk shi kadai, ni ko na san zafin rashi saboda na rasa mahaifina da dan'uwana kuma na san zafin babu saboda ana tashi a cikin babu din, shi ko be san babu ba sai akwai kuma be san zafin rasa komai ba a rayuwarsa sai yanzu.
“Fada min kina nan lafiya kalau”
“Lafiyata kalau, kuma na yafe mata abunda tai min wanda na sani da wanda ban sani ba, Allah ya jikanta yai mata Rahma”
“Amin na gode, cikinji fa yana lafiya?”
“Komai lafiya kalau, zan fadawa Mama yanzu”
“Okay ki kula min da kanki pls”
Na gyada kai kamar yana gabana sannan na aje wayar akan gadon na zauna bakin gadon ina ta kuka, ban taba tsammanin jin labarin mutuwar Rahma zai sakani shiga damuwa ba balle har nai kuka, amman sai ga ni ina kuka kamar wacce na rayu da ita na tsawon lokaci na shaku da ita, a yau duk wata kiyayya da kishi da jin haushi ta kare, mai rabawa ta raba. Kaico mai rai ba abakin komai yake ba, lokaci daya idan Allah ya so kama ka sai ka raina kanka har makiyinka ya tausaya maka. Sai da na ci kuka na koshi sannan na fito falon Hajiya wato kakana idona a kumbure da kuma sauran hawaye na nufi inda Hajiyar take zaune na mika mata wayarta wacce ta ara min na kira Hamma da ita.
“Lafiya kike ko?”
“Rahma ce ta rasu”
“Wace Rahma?”
“Matar Hamma”
“Innalillahi wa'inna ilaihirraji'u”