← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 143

Sashe 91

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wata kyakkawar muryar mai dadi sauraro ta yi min sallama ta bayana, sai na juyo na ina amsawa tare da kallon mai sallamar. Bakin mutum ne cikin shadda ruwan kasa da hularsa mai haske taba ni ka ji hadisi sajensa ya kwanta gwanin sha'awa kama ganinsa ka san irin ustazan nan ne da ko kallon mata basa son yi.

“Dan Allah ina ne gidanku?”

“Lafiya?”

“Lafiya Kalau nuna min kawai na ke son ki yi”

“Can mai jan gate”

Da hannu na nuna masa kasancewar ina daf da gidan ne.

“Na gode”

Sai kawai yai gaba ya bar ni a gurin tsaye da mamaki, da kallo na bishi har sai da na daina hango shi sannan na karasa gate din na buga aka bude min na shiga ciki, harabar gidan na ke hangowa ina son tantance abunda na ke hangowa Doc Bukar ne tsaye da Daddy suna gaisawa, har na yi kamar ban gansu ba zan wuce sai Doc Bukar ya kira ni.

“Aisha....”

“Na'am”

Na amsa sannan na juyo na doso inda yake tsaye, har kasa na risina na gaishe da Daddy ya amsa min da far'a yana nufi kofar falon ya bar ni da Doc Bukar tsaye muna gaisawa.

“Daman na zo gurin Aliyu ne kuma ba ya ne sai ga Daddy ya shigo muka gaisa”

Na yi shiru ban ce komai ba sai gyra littafaina na ke hannuna.

“Daman kullum ina son na zo mu gaisa sai Aliyu ya ce ba ki gidan, ya mai jiki?”

“Al-hamdulillah”

Ganin ina masa ciki ciki kuma babu sakewa a tare da ni ya saka ya bude motarsa ya dauko kudi ya miko min.

“Gashi ki gaida Mama”

Kasa Karba nai, daman ko lokacin da nake bara ina neman kudi dalili ne wanda a yanzu babu shi.

“Aa na gode”

Na juya na nufi bq din na bar shi a gurin tsaye, sai da na shiga na cire uniform dina na saka wata doguwar riga sannan na ji tashin motarsa a lokacin Nana ta fito daga bandaki.

“Kin dawo”

“Eh Nana ya jikin na ki?”

“Al-hamdulillah, Hajiya ta dawo?”

“A a wani abun ne?”

“Idan ta dawo ki sanar da ni, ya kamata mu tafi wani gurin kuma tun kamin mu saba da nan”

“Wani gurin zamu je kuma Nana?”

“Eh In-Sha-Allah”

“Amman miyasa?”

Bata ba ni amsa ba Siyama tai sallama ta shigo wai na zo Daddy yana nemana, Hijab dina na dauka na saka na bi bayanta jin kiran Daddy da kansa na sam abu ne mai muhimmanci, har part dinsa ta shiga da ni yana zaune kasan carpet da kofin ruwa a gabansa da waya har biyu yana dannawa. Ko a. Lokacim da ya amsa min sallamata bw kalle ni ba ya amsa min ne kawai sai Siyama ta mike ta fita ta barni. Kaina a kasa lokacin daya aje wayar ya soma min magana.

“Abunda ya faru ya riga ya faru ki manta da komai kuma ki dauka komai be faru ba, mu tamkar ya muka dauke ki dan haka za mu iya yi miki komai kamar yar da muka haifa, ki janye maganar Momy ko ta Muhseen ko ta Aliyu, na ba ki kwana biyu ki je ki yi tunani ki fada mana wanda kike so, sati mai zuwa auren kuma ba zai hana ki karatu ba za a miki auren ne saboda ki samu natsuwa kowa ma ya samu, Momy za tai maganar da Mahaifiyarki idan ta dawo gobe wannan tsakanina da ke ne”

Sati daya? Kamar wata yar tsana? Kamar ua sati daya? Sum gaji da mu ne ko kuwa dai suna son tsawwalawa mana ne ko kuma wani abun ne da dabam.da wannan tunanin na taso na dawo bq kaina a kulle.
ZAKI

By Khadeeja Candy

42...

A daki na samu Nana zaune ta rafka tagumi tana kallon kofa kamar mai jiran shigowata. Nima damuwar ce a fuskata na maganar da Dddy ya fada min yanzu, sai dai na yi kokarin moye tawa damuwar tare da tambayar abunda yake damunta da kuma dalilin barin gidan da take son mu yi bayan na fara karatu a yanzu abunda na rasa shekaru da dama.

“Nana miyasa kike son mu tafi? Momy ta roke ki da mu zauna kuma karatun da na fara dainawa zan yi Nana idan muka tafi”

Hawaye na gani a fuskarta.

“Ina ganin kamar zaman gidan nan matsala a gurin na ina ganin kamar son ki ya haddasa wata kiyayya ko kuma fada a tsakanin yan'uwa biyu, Hajiyar gidan nan ta mana karamci iya karanci ba kowa zai yarda ya zauna da irin mu ba, amman ta zauna da mu ta nuna mana kauna, ban san miye alakar Muhseen da Aliyu ba, na san dai yan'uwane amman yan'uwanta kan da ina ne ban sani ba, bana son na zama silar rushewar wasu iyalin bayan barin nawa da nai”

“Nana miyasa kika yi wannan maganar?”

“Na baki shawara auren Aliyu ne a mahangar da na ke ganin ta dace da ke kuma na ke ganin kamar ba zata cutar da ke ba, na san ba ki san so na kuma ba lallai ne ki iya fahimtar komai a yanzu ba wata kila sai gaba, kina da damar zaben wanda kike ganin ya dace da ke Ataa kuma wanda kike jin ya kwanta miki a rai”

“Miyasa kika ce haka?”

“Sayan tafiyarki islamiya, Husna ta shigo da waya tana neman na fada mata ta kin tafi makaranta, an jima kadan kuma sai Amina ta zo wayar ta miko min wai Muhseen yana son magana da ni, hakuri ya fara bani sannan ya fada min cewar ya hakura duk abunda zai raba kan Mahaifiyarsa da Mahaifiyar Aliyu zai iya hakura da shi, duk kuma abunda zai iya shiga tsakanin mahaifinsa da mahaifin Aliyu zai iya hakura da shi, ya fada min idan kika aureshi ba ki auri Aliyu ba, Aliyu da iyayensa za su ga cewar ba ki kyauta musu ba kuma ba mu musu karamci ba, idan kuma kika auri Aliyu kika barshi zai hakura amman ba zai taba iya cire son ki a ransa ba, kuma yasa iyayensa ba za au daina ganin cewar iyayen Aliyu sun yi son kai ba, ya ba ni hakuri ya fada min akwai zumuncin mai karfi a tsakaninsu, kar na bari zumincinsu ya lalace”

Na dan yi shiru ina tunanin wata kila tsoron lalacewar zumincin ne ya saka Momy ta tafi Abuja, ko da yake daman na san tana da ra'ayin zuwa tun a wacan karon da tai min albishirin zuwa da ni.

“Amman Nana wannan abun ya isa ya saka ki ce mu bar gidan nan? Idan muka tafi ina zamu zauna? Babu mai karbar mu sai yawon rabe rabe a titi, haka rayuwar mu zata kare? Ba kowa a tare da mu kuma sai mun yi ba ra mu ci? Kullum wani kalar kabulen muke fuskanta? Indan har za mu bar nan kamata yai ace cikin danginmu za mu koma, Nana ban san kowa na ki ba, ban san kowa na mahaifina ba, miyasa kika gudu kika dawo nan kin kasa fada min kullum sai boyewa kike bayan nima ina da hakkin sani domin ni yarki ce”

“Ba dadi ne ya rabo ni da iyayema ba, shiyasa ba zan iya koma musu ba, na musu tuluci sai kuma yanzu na ce zan koma? Ai abun ma da kunya”

“Mi kika aikata Nana? Butulcin me kika musu?”

Shiru tai na wani lokaci tana hawaye.

“Na yi ma iyayena budulci, kuma na gudu na barsu ina jin kunyar komawa a yanzu ina jin kunyar arba da mahaifina da mahaifiyata waya sani ko su yi min mummanar kalami bayan tafiyata”

“Mi kika yi har ya koreki?”

“Ba korata yai ba guduwa nai a karan kaina”

“Saboda mi nana?”

“Saboda Soyayar mahaifinki, na so mahaifinki kamar na mutu ina ta ganin kamar idan zan yi rayuwa ba da shi ba zan iya mutuwa ko na fada halaka, a Masarautar mu mace ba ta zabawa kanta mijin aure sa dai iyaye su zaba mata, ni kuma nai kuskuren zaba da kaina kuma a ganina ba laifina ba ne idan na zabawa kaina mijin da ya fi kwantar min a rai”

“Masautarku kike ce Nana? Kin saka kaina a cikin duhu ban gane ba”

“Ba zaki gane ba Ataa ba lallai ne kowa ya yarda ba balle har a iya tsayawa a gane, kowa yana ganina a wulakance a kaskance amman ni jinin sarauta ce ni kadai ce ya mace a gurin Sarki Bashiru Muhammadu, ni kadai ce Gimbiya Nana Asma'u a duk fadin masarautar Agadez”

Ba zan na kasa yarda da abunda Nana take fada min ba, amman tabbas labarin nan abun rikitarwa ne.

“Amman Nana muka kare a bara?”

Na tambaya cike da zakuwar son jin labarinta. Numfasawa gai sannan ta ce

Chapter 91 · 0% Book details