← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 41 OF 143

Sashe 41

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ban sake ce mata komai ba na tashi na ahifa store din na dauko sabulun na nufi garden din, dana isa kurawa kayan ido nai na rasa da wanne zan fara wankewa? Shikenan saboda ba ni da gata duk abunda aka ga dama sai ayi min. Ba ni da wani iko da karfin da zan iya cewa ba zan wanke ba, dan haka na saka tufafin a gaba ina ta wankewa ga rashin karfin jiki na zazzabin da na ke ji, ga yunwar jiya da dare gashi da safen nan ma ban saka komai a cikina ba. Haka na saka kayan a gaba ina ta wanki tun ina yi da dan kuzarina har na koma bana iya komai na gaji sosai amman a haka na tisa kayana a gaba na wanke su tas babu abunda na bari, sannan na bi na shanya su, sai na zuba ruwa robar na laba bayan itacen mangoro guda biyu da suka hade waje daya na boya a gurin nai wanka wai ko zan dan samu karfin jiki, sai dai abunda ban sani ba Ya Muhseen na daga dakin Mama Fulani yana hange ni, sai dai a lokacin da nake wanki ban ganshi ba, wata kila be zo gurin ba sai da na fara wankan, kuma ban lura da shi ba sai da na gama wanka. Kunya ce ta kamani duk sai na ji babu dadi ko ba komai yaga tsiraicina wanda shi kansa na san yasan haramun ne, ban tsaya saka rigata a gurin ba, na dauketa tare da dankwalina na fito daga garden din na nufi garejen, a cikin tufafin Inteesar da Ammy ta bani na dauki wani lace na saka na daura dankwalin sannan na nufo part din Mama Fulani dan bata ragowar rabulunta.

ALIYU POV.

A lokacin daya bar kamfani sai ya dauki hanyar gida, yana ta tunanin maganganun Nasir, tabbas shi kanshi ya san an cuci yarinyar kuma dole zara ji zafi saboda mahaifiyarta akai wa, but he like yadda take fada masa magana kai tsaye ba tare da tsoro ba, idan ya tuna ko wace kalma ta ta sai ya tsinci kansa a kogin tausayinta, yes she's right da ace yar masu hannu da shuni ce da Doc Asim be yarda ko yatsanta ya taba ba balle har ya cire kodar mahaifiyarta, and secondly na ji zafin hawayen da ta zubar da cewar da tai Mama Fulani ta mareta, yasan Halin Mama Fulani daman ba jutuwa take da yan aiki ba, shiyasa duk wacce aka kawo da taje ganin gida bata dawowa, a dayan bangaren kuma yana jin haushin yadda Muhseen yake masa. Iya kokarin da yai ta isa gida ba tare da Rahma ta gane yana cikin damuwa ba, ko da ya isa ya sameta a falo dinning mai dafa musu abinci namiji yana serving dinta, yana daya daga cikin dalilin daya saka take son zama a Abuja a nn ko kofi bata kawarwa mai musu aiki ne namijin dan kabilar igbo yake mata komai ciki kuwa har da dafa abincin da gyara duka dakunan. Juyowa tai ta kalleshi da far'a da alama tana cikin farinciki.

“Dear welcome”

Karasawa yai kusa da ita ya kai bakinsa ya sumbanci gefen kumatunta sannan yaja kujera a kusa da ita ya zauna.

“Na yi waya da Doc Perry gobe zan je na ganshi”

Shiru nai na wani dan lokaci sannan ha kalleta.

“Why ba zaki bari sai nan da kwana biyu ba idan kin huta”

“Ba wani zancen hutu, tunda yanzu na samu lafiya ai zan iya komai, kara kawai na maida hankali gurin neman haihuwar”

Ya gyada mata yana mikewa tsaye kamar be jidadin. A daren da tunani biyu ya kwana a ransa, na ganin Doc Perry da Rahma ta ce za tai da kuma na Ataa wanda be san dalilin na damuwar kansa da tunaninta ba. Ko da suka tashi da safe mai dafa musu abinci ya gabatar da komai a beburin karyawa, a tare ya karya da matarsa sannan na ya shiga dakinsa ya shirya cikin shiga ta manyan kaya ya fito yai mata sallama ya kama hanyar kamfaninsa.
A kamfanin ya wuni duk wani abun da akai baya nan sai da aka gabatar masa da shi ya ganshi kuma ya duba yadda komai yake tafiya kowa ya san da cewar oga ya dawo sannan suka shiga meeting, bayan sun fito ne yake labartawa Nasir zancen ganin Doc Perry da Rahma zata je yi.

“Then why da ba zaka fada mata gaskiya ba? For how long za kai ta aje wannan sirrin ne Aliyu?”

“Ban sani ba, iyakar abunda na sani zan iya ajiyarsa har karshen rayuwata, kawai kasa a nemo min Doc Perry ina son magana da shi”

“Haka zaka daukarwa kanka a duk lokacin da zata je ganin wani likita sai ka samu kudi ka bashi a rufe maganar? Anya hakan zai haifar maka da da mai ido Aliyu? Idan ma kai baka son ganin iyalinka ai familynka suna so, muma kuma muna so”

“Matata tana da muhimmanci a gareni Nasir, idan ta san gaskiya ni ne zan fi shiga damuwa domin zata saka kanta a damuwa ne, kuma duk abunda nai mata zata ga na mata ba daidai ba, and kasan Mama Fulani ma zata fara damunta just like Momy daman can ba jutuwa suke da Momy ba”

“Amman wannan kawai ya isa ka kasa kanka a wannan matsalar? Kana ganin idan kai ne Rahma zata zauna da kai? No ina da Tabbacin duk yadda take son ka ba zata zauna da kai ba, shekarar ku takwas da aure Aliyu idan baka fara tunanin samun haihuwa a yanzu ba, zuwa yaushe zaka fara? Lokaci yana tafiya, a yanzu nan gaba kadan karfin ragowa zai yi ba karuwa ba, ya kamata kai tunani”

Aliyu ya tsaya cikawa bakinsa iska a lokacin daya riga Nasir shiga office din.

“Kamin na ga wasu yayan Rahma na fara gani, be kamata ace wani abun ya shiga tsakaninmu ba”

“Haihuwa ita ce shiga tsakani? Kai ba haihuwar ka akai ba?”

“Yes i mean kasan yanzu idan kowa ya gane gaskiyar Rahma zata shiga matsala ta shiga damuwa, kuma muna son junanmu ni da ita, be kamata abunda be riga ya zo ba ya saka mu damuwa”

“Ina da tabbacin da akanka ne Wallahu Rahma ba zata zauna da kai ba, zata fi son ganin gudan jininta fiye da kai, ballantana tana ganin cewar tana yar nai nera zata iya samun wani mai nera ta aura”

“Baka san yadda Rahma take so ba ne Nasir baka san so ba ne”

“Fine, idan kana son ka gane gaskiya ka daina cewa kai da ita ba ku da matsala, ka fada mata cewar kai ne mai matsalar wannan karon idan kunje tare ka biya Doc Perry ko nawa yake so ya fada mata haka, na tabbatar zaka ba ni wani labarin dabam”

Aliyu yai shiru yana nazarin kalaman Nasir. Ta wani bangaren yana ganin kamar be dace ya gwada Rahma kamar haka ba, wani bangaren na zuciyarsa kuma yana ta zugashi akan ya gwada din. Har ya bar office din be samu matsaya daya akan gwadarwa ko kin gwadarwa ba, ya sa dole zata kira shi tace mishi tana asibiti ya sameta a can a gwada lafiyarsu ta bangaren haihuwa kamar yadda ake musu a ko da yaushe, sai dai ba shi tabbaci ko Doc Perry zai yarda da hakan ba har ya aikata domin shi babban likita da kowa ya san da zamansa cikin garin Abuja, matukar kana amsa sunan mai nera to ka san Doc Perry, likita daya kware akan aikinsa kuma yake fadin gaakiya a ko da yaushe, ba iya nan kawai yake duba mutane ba har kasar waje an san da zamansa, sai dai Rahma bata taba damuwa da su je gurinsa ba, sai a yanzu da haihuwar ta fara damunta. A hanya yai sallah la'asar sannan ya isa family house gurin wato gidan Alhaji Hamza. A harabar gidan yai parking amman be fito cikin motarba ya tsaya dannen dannensa har ya hango Ataa ta fito daga Garden daga ita sai daura gaba, kirjinta a cike ga farin daya bayyana kansa a jikinta, gashin kanta a jike da alama wanka tai ko kuma ruwa ta fada, amman idan ruwa ta fada ai dole har tufafin jikinta zai jike, be taba kula da surar mace karamar yarinya kamar yadda ya kula da ta Ataa yau ba, karamar yarinya ce amman tana da abunda yake kauna a jikin mace wato breast ga yawan gashin kai, wanda ko Rahma da take babbar mace bata kaita breast ba, ga gashin kai kamar wacce akai wa dashe ya kwanta har gaban goshinta gwanin sha'awa, and every takunta jikinta motsawa yake fatarta na sheki kamar mai shafa wani kasaitaccen mai. Kasa dauke idonsa yai daga kanta har ta shige garejen ba tare da ta kula da shi ba.

“Miyasa tai wanka a Garden?”
Chapter 41 · 0% Book details