← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 48 OF 143

Sashe 48

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Sai da yai sallah magariba a unguwar sannan ya isa gida yana ta jin babu dadi a abunda Maryam tai ma Ataa and ganin Muhseen na bata magani ma it pain him domin yana ganin kamar cutar da ita kawai Muhseen zai yi, yana da tabbaci zai iya kare kansa daga duk wani abu da zai kusantar da shi daga Zina amman ba shi tabbaci wani zai iya kare kansa daga hadawa hallakar zina, ba kuma duk wannan yake damunsa ba, babban damuwarsa zuwan Ataa gidan saboda nemawa mahaifiyarta maganin kodar da aka cire mata wanda shi ne sanadi duk da ba da saninsa da amincewarsa aka cire ba, yanzu kuma idan wani abun ya same ta ai duk saboda shi ne. Babban plan din da ke gabansa na ya taimaki mahaifiyar Ataa ne ya nema mata magani ta samu lafiya sannan ya nemi yafiyarsu wata kila zasu yafe masa, amman ya kasa tunkarar Ataa kai tsaye da hakan, saboda tana fada masa magana son ransa a duk lokacin da yai maganar mahaifiyarta shi kuma girma kai da jin kai ba zai barshi ya iya tsayawa ya fahimtar da ita ba.
Horn daya yai aka bude masa gate ya shiga cikin gidan ya faka motarsa a inda ya saba fakawa, sannan ya bude motar ya fito ya nufi kofar shiga falon, wutar falon a kunne take sai dai tv a kashe kamar yadda ya fita ya barshi amman ya an gyara komai na falon wanda hakan ke nufin mai gyara gidan ya zo ya gyara ya tafi, dakin Rahma ya fara nufa ya tura ya shiga, sai ya same ta kasa kwance ta dafe cikinta zuwa awanzunta tana wani irin daukar rai kamar zata mutu, wayarta na nesa da ita a kasa, da alama kubucewa tai a hannunta ta fadi kasa, hawaye na ta fita a idonta. A firgice ya karasa kusa da ita ya rikota yana taba fuskarta.

“Rahma minene?”

Kasa magana tai sai ta bude baki tana fitar da numfashi daker, da sauri ya dauke ta ya fito da ita ya saka a mota kamin ya shiga motar ya kwalawa mai gadin kira ya ce ya bude masa gate, @360 ya fisgi motar ya fita daga gidan ya dauki hanyar babban asibiti, kamin ya isa hankalinsa ya tashi sosai yana ta ganin kamar Rahma mutuwa zatai a motar, sai duk yaji tafiyar ta masa tsawo yana jin kamar ana mayarda shi baya. Yana isa emergency aka karbe ta kasancewar asibitin ta manyan masu kudi ce ga kayan aiki a take aka hau bata taimakon gaggawa, shi kuma ya kasa tsaye ya kasa zauna sai da ya ga an fito da ita daga dakin an kaita wani dakin an saka mata oxygen an saka mata wata allura a hannu, komai likitocin ne suka mata ba kamar nan da ake cewa mutum ya dauki mai jinya yaje ya kaishi a masa hoto ba, su da kansu suka dorata a wani gado suka kaita wani dakin aka dauki hoton jikinta gaba daya sannan aka dawo da ita wani likitan ya shigo ya debi jininta ya fita. A lokacin ne Aliyu ya samu natsuwa har ya kira Mama Fulani da Ammy da kuma Momy ya fada musu kamin ya kira familyn Rahma su ma ya fada musu. Zauna yai kusa da ita ya kai hannunsa yana shafa fuskarta dayan hannunsa kuma cikin hannunta yana murzawa a hankali, kallo daya zaka masa kasan yana cikin tashin hankali rudani da tsoro a lokaci daya.
Ba ayi minti talatin ba sai ga Mama Fulani da Ammy a asibitin sun zo, hankalin Mama Fulani ya fi tashi fiye da na Ammy ita kuma ba dan Rahma ba sai dan Aliyu da ta san zai tashi hankalinsa saboda Rahma, domin shi Mama Fulani take kallo ba Rahma ba.

“Jiki ai da sauki”

Mama Fulani ta fada.

“Eh da sauki gaskiya tun da yanzu sun saka mata oxygen zata samu saukin numfashin, kuma sun mata hoto ko minene za su ga ni ai”

Ammy ta ce.

“To wai miya faru ne da ita?”

“Wallahi ban sani ba, ina komawa gida na same ta a dakinta kwance kasa ta dafe cikin tana daukar numfashi”

“Allah ya sauwake"

“Amin”

Ya amsa yana picking din calling don da Mommyn Rahma ke masa, cikin sautin kuka ta ce.

“Fada min addreshin asibitin ga kanwata nan da take Abuja zata zo ta duba mana jikinta”

“Jiki da sauki fa ta samu bachi ma”

Haka ya fada sannan ya fada mata inda asibitin take ya kashe wayar, sai ga wani likita ya shigo ya ce duk su fita basa son ganin kowa akan marar lafiyar, daman a ka'idar asibitin ba a aje mai jin marar lafiya su suke masa komai ba a kwana a asibitin da sunan jinya suna da nurses da suke kula da marar lafiya da ko mai jinyar ba zai iya kula da shi haka ba. Gaba daya suka fito daga dakin suka bi bayan baturen likitan zuwa office dinsa domin ya fada musu yana son magana da iyayenta ko mijinta, a lokacin da suka shiga office din sai suka samu ba likita daya ne a ciki ba, likita biyu suka tarar yan Nigeria bayan wannan baturen da suka shigo tare da shi, a bayan teburin likitocin an laka wani katon majigi mai kamar kwanfuta an laka wasu hotuna a jikin abun. A visitors chairs suka zauna shi kuma likitan ya nufi inda computer take ya cire hotunan jiki ya dauko wasu ya laka da wani dan pen na hannunsa ya nuna musu inda matsalar Rahma take yana musu bayani da halshen nasara. A bayanin da likitan yai da wanda sauran likitocin sukai babu wanda Aliyu ya fahimta, ba dan baya jin turancin ba, sai dan jin abun wani banbara gwai, wai kodarta ta kone as how kodar mutum zata kone? Ba ma lalacewa ba? And duk duka yaushe aka saka mata kodar da za a ce ta kone? Gaba daya rikecewa yai ya tashi ta sauri ya fice daga office din ba tare da ya jira likitan ya gama bayanin ba.

Ammy ba ta wani dade asibitin ba bayan likitan ya gama musu bayani suka fito suka samu Aliyu tsaye a waje duk ya bi ya rike kamar ba shi ba, shi kansa ya san Allah kadai ya iya haka, ace koda ta kone, gashi kodar ce daya ta rage mata wacce aka dasa mata sai kuma ace ta kone, kamin ma ya samu wata aiki ne, and ba zai zama ace ko da yaushe sai an dasa nata koda ba idan an samu wata rana ba za a samu ba. Mama Fulani ce ta tsaya da shi tana ta bashi magana tana kokarin kwantar masa da hankali, har wata kanwar mahaifiyar Rahma ta shigo taje ta duba, yasan dokar asibiti ba a kwana da sunan jinya amman a haka ya karya dokar ya zauna a kujerar ya saka matarsa a gaba yana ta kallonta hannunsa cikin nata, ji yake kamar ya cire ta mata ciwon a take ta tashi, jikinsa nata raya masa mutuwa za tai ta bar shi, and all what he was thinking idan ta mutu ba zai iya rayuwa ba, taya ma zai rayu babu Rahma? Haka ya saka ta a gaba yana ta kallo, misalin 12 ya aikawa Nasir da sakon abunda yake faruwa, da Nasir ya kira shi kuma sai ya kasa dauka, sai kallon wayar yake gaba daya ya rike ce ya rasa inda zai saka kansa, gaba ya saka ta yana ta kallo har garin Allah ya waye, bachi be leka idonsa ba ko da wasa. A wani masallaci dake nesa da asibitin yai sallah asuba gaba daya addu'arsa Rahma yai ma, daya fito daga masallacin sai ya zauna cikin motar ya kifa kansa jikin sitarin motar yana ta sauke ajiyar zuciya idonsa na masa mugun nauyi. kiran Nasir ne ya shigo wayarsa amman ya kasa picking har tai ringing ta katse aka sake kira, gaba daya kasala yake ji yana jin shi ma kamar ba shi da lafiyar. Sako ya turawa Nasir na addireshin inda yake, sannan na kwantar da kujerar ya lumshe idonsa, cikin mintunan da ba su fi ashirin ba Nasir ya iso gurin, babban masallaci ne amman hakan bw hana shi gane motar Aliyu ba, domin irin ta bata da yawa a garin Abuja. Yana bude motar Aliyu ya bude idonsa da suka kada sukai ja yana kallonsa.

“Ya jikin nata?”

Aliyu yai shiru be ce komai ba sa yawo yake da idonsa kamar marar gaskiya. Nasir ya dafa shi.

“Aliyu ka kwantar da hankalinka...”

“Wane irin na kwantar da hankalina? Kodar ta fa aka ce ta kone, ko baka gane ba?”

“Na gane, amman me likitocin suka ce?”

Aliyu be ce masa komai ba, ya jinginar da kansa jikin sitarin yana sauke ajiyar zuciya. Can kuma ya dago ya kalli Nasir.

“Saboda kodar nan ta zalinci ce ko? Shiyasa ta kone? Ko kuma saboda Ataa ta ce ba zata taba amfanar Rahma ba? Ta mana Allah ya isa fa”

“Gaskiya ne Aliyu zalinci kawai ba ban da addu'ar da tai muku ta isa ta saka wani abu ya faru, domin ita wacan da aka cirewa ba mu san halin da take ciki ba....”

“What if na bata hakuri?”

Nasir yai saurin tarar numfashinsa.

“Karka tinkareta kai tsaye yanzu tun tuni ya kamata kai wannan kuma ba kai ba”

“No baka san yadda nake ji ba ne a yanzu Nasir, bana son na rasa Rahma”

“Ai ba cewa akai zaka rasa ta ba, amma
...”

“No hakuri zan bata Nasir”

Ya fada yana jan murfin motarsa ya rufe. Cikin saurin Nasir ya nufi tashi motar ya shiga ya bi bayan Aliyu.

ATAA POV.

Na tashi da safe da zazzabi da kuma rashin kuzari, dukan abunda ya faru jiya sai ya zame min kamar mafarki ciki kuwa har da maganar da Muhseen yai min. Bayan na gabatar da sallah asuba na dauki jakata na nufi garden na shanya duka kayana da suka jike sannan na shiga part din Mama Fulani na fara gyara falon, na nufi dakin Ammy na gyara mata nata falon, ina cikin saka air freshener na ji tana fadin
Chapter 48 · 0% Book details