← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 96 OF 143

Sashe 96

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Dan Allah amin sadaka da wannan a bawa mabukata”

Da hannu biyu liman ya karba yana bude baki cikin tsananin mamaki domin ba kasafai Aliyi ma ya cika tsayawa ya gaisa da mutane ba balle kuma har ya mika wani abun da sunan taimako.

“Masha-Allah Mashallah, Allah ya saka da alheri Alhaji Aliyu Allah ya biya bukata ya kara bude ya sakawa rayuwa albarka, Wallahi ka taimaka a wannan hali da mutane suke ciki ai taimakon ake bukata ta ko'ina”

Har cikin ransa ya jidadin addu'ar liman after Momy dake masa addu'a kullum sai kuma Nana da ta taba masa a asibiti yau ma an sake masa, duka biyu kuma sanadin taimako ne ta uwa kuma ta kauna ce, sai ya ji natsuwa da kwanciyar hankali sun rabi ruhinsa. Cikin gidansa ya koma ya bude freezer ya dauko ruwa ya sha kadan ya aje sauran ya dawo saman cushion ya kwanta kamar wani sabon ango haka yake jin kansa gaba daya ya manta da komai da ke tare da shi Ataa kawai yake gani da kuma irin rayuwar da zai yi da ita, lokaci zuwa lokaci yake murmushi yana shafa kansa da fuskarsa, har mamakin yadda farinciki ya cika masa zuciya yake. He don't think zai iya biyewa Momy ko wani ma cewar after aurensu za tai karatu shi ji yake kamar kar kowa ma ya kara ganinta daga yanzu, he i can't wait ya ga ta zama halalinsa ta yadda zai rumgumeta a kirjinsa ya sumbace ta. Tashi yai zaune ya nufi dakinsa ya doro wata alwalar ya fito ya nufi masallacin dazun yai sallah, mutane sai kallonsa ake ko zai sake rabawa wasu kuma dan ya san da su, har da masu ba shi hannu ya gaisa da su, a da he can't shake his hand with anyone indai talaka ne amman a yanzu sai mika musu hannunsa yake suna gaisawa kamar ya manta waye shi.

Yana shigowa gida ya sake shiga dakinsa ya dauko wasu kudin ya saka aljihunsa sannan ya fito ya shiga motarsa horn daya aka bude masa gate sai ya tsaya daidai gurin mai gadin ya ciro kudin da za su kai eight to nine thousand ya mika masa, a take mai gadin ya washe baki ya fara zuba masa addu'a shi kan be shi ta kansa ba ya dauki hanyar gidansu Momy.
Har ya faka motarsa bq din su Ataa yake kallo ji yake kamar ta leko ya ganta, ya dauki lokaci a haka sannan ya bude motar ya fita ya shiga part din Momy sai wagen bq din yake kmar ance masa fitowa za tai.
Hannu ya kai ya tura kofar falon ya shiga fuskarsa da murmushi kamar ba shi ba, duka suna zaune falon suna ci abinci a plate daya da Momy, Amina Siyama da kuma Husna. Tuwon shimkafa ne miyar kuka da man shanu sai kamshi yake.
Suna kallonsa ya sakar musu murmushin farinciki, Momy ta ce.

“Ai na dauka ka bata a jirgin ne, tun safe ba a samun wayarka kuma ba ka shigo ba”

Sai yanzu ya tuna wayarsa a flight mode take. Zauna yai a kujera yana dariya.

“Momy kin san me Wallahi na manta sam wayata a flight mode take kuma ban cire ba, kuma da wani dan abun ne ya rike ni bayan na sauka a nan”

Da dai daya kannensa suka rika mika masa gaisuwa yana amsa musu, sannan ya saka hannunsa aljihu ya ciro kudi ma su yawa ya mikawa Amina.

“Gashi nan ku raba”

Ya sake saka hannunsa ya ciro wasu kudin ya mikawa Siyama.

“Idan kin gama cin abinci ki kawai mai gadi”

“Wow Ya Aliyu na cikin farinciki ni na maka albishir fa”

“Thank you Husna i love you”

Ya fada yana murmushi.

“I love you too Yayana”

Sannan ya kalli Momy ya ce.

“Thank You Momy”

“For what?”

“For everything”

Murmushi tai ta cigaba da cin tuwonta.

“A zubo maka?”

“No Wallahi bana iya cin komai tun jiya da aka fada min har yau bana jin yunwa”

“Taf to Yayana idan aka daura maka aure fa”

Husna ta fada. Dariya yai ya kwantar da kansa jikin kujerar domin ba zai iya fadar abunda yake ji a yanzu ba ma balle kuma idan ta zama halilinsa.

“Momy wannan Assabar din ne ko?”

Momy ta kalli Siyama tana bata amsa.

“Eh In-Sha-Allah”

“Amman ba yi ai iv ba ko sai gobe gobe fa Friday?”

“Ni ko mutun biyar suka daura min aure ya wadatar ni dai a daura din kawai dai shine matsalata”

Ya fada kai tsaye a gaban Momy. Yadda take ganin Aliyu yana nuna son Ataa daga lokacin da tai masa maganarta zuwa yau kamar wanda be taba aure ba aka hada shi da wace yake so kuma a dauke masa yin komai haka yake.
Misalin takwas Daddy ya dawo, bayan ya shiga part dinsa ya huta Momy ta kai masa abinci y ci sai Aliyu ga shiga gaishe shi, nan ma fuskarsa da Murmushi tana nuna farincikin da yake ciki.

“To sai ka rike yar mutane da amana kuma kai adalci dan kasan ba ita kadai ce ba, kar son wata ya saka ka danne hakkin wata ko nunawa ta kiyayya, ka ji tsoro Allah”

“Na gode sosai Daddy In-Sha-Allah Allah zaka same mi mai adalci da rike amana”

“Allah ya hada kanki ya kawarda fitini kuma ya ba ku zama lafiya”

“Amin”

Ya amsa sannan ya taso ya dawo part din Momy, sai kusan sha biyu dare ya bar gidan a harabar gidan ya tsaya ya dade yana kallon bq sannan na koma gida, da farinciki ya kwana ya tashi ya kuma dawo gidan Momy, duk yadda ya so ya saka Ataa a ido yau be saka ta kasacewar islmiya kuma ta labe a bq abunta ta ki fitowa.
Haka ya sake wuni a gidan domin ba shi da inda ya fi nan, ga zuciyarsa kuma ta kwadaitu da son ganin Ataa kamar wanda be taba ganinta ba.
After sallah isha'i Daddy ya dawo, ko hutawa be yi ba ya kira Aliyu a waya ya fada masa yana son ganinsa, a natse suka gaisa da Abbah before ya dora da.

“A masallacin juma'a na Muhammadu Maccido da ke amir yahaya za a daura auren, dazun muke magana da Alhaji Sulaiman na fada masa tun da ba gayyato mutane za'ayi sosai ba kara a daura auren a friday kawai a huta”

“Daddy gobe Friday fa?”

A rikice Aliyu ya fada yana kallon Daddy da wani irin farinciki marar misaltuwa.

“Yes”

“Daddy thank you so much Allah ya saka musu da alheri”

“Amin”

Daddyn ya amsa yana bude jaridar hannunsa. Daga haka ya taso ya dawo part din Momy, sai murna ta kaure a falon shi da kanensa da Momy domin suna son farincin dan'uwansu duk kuwa da irin hade musu fuska da yake sai dai sun san yana son su kuma yana musu duk abunda zai saka su farinciki. Be bar gidan ba sai kusan goma na dare, har ya isa gida zuciyarsa bata daina zumudi da son ganin Ataa ba, ji yake kamar ya hanyo goben ya matso da ita ta zama yau ma a daura musu auren tun a yau ba sai gobe ba.
Sai da ya huta ya sha Lipton sannan ya kira Nasir na sanar da shi komai kuma ya fadawa Nasir da sanar da wasu friends dinsa, shi kuma ya turawa wasu da kansa a take aka fara kiran wayarsa kowa ya ji abun daga sama. A cikin daren Aliyu ya sake buga wayar Nasir ya fada masa ya idan zai zo dauren auren ya zo masa da expensive ready-made da shoes da cap, yana da sabbin tufafi a nan wadanda be tana sakawa ba, amman ya fi son yai siyo wasu saboda dalili zai jindadi da natsuwa.

MUHSEEN POV.

Ji yai kamar ya rumtse ido ya bude ya ga komai na duniyar nan ya tarwatse cikin kuwa har da auren da Aliyu da Ataa da jin labarin na hana shi sukuni da walwala, wani irin bugawa zuciyarsa take da ace akwai abunda zai yi ya hama faruwar auren a yanzu da yayi, domin sai a yanzu yake jin cewar yayi ganganci kuma yayi sake na saurin sakarwa Aliyu ragama. He can't believe ya rasa Ataa kenan har a bada, taya zai rika kallonta a matsayin matar Aliyu a cikin familynsu?

“Be ma kamata tun farko nai hakan ba, shikenan shi ya samu kyakkyawa kuma wacce na ke so, ya ji dadin kara fadin rai”

Ya fada yana wulgar da kofin tangaran din dake hannunsa a take kofin ya fashe. Wani irin fushi da bakinciki yake ji marar misaltuwa kamar ya haukace yake jin kansa gaba daya ya kasa natsuwa ya saka sukuni.

Ta bangare Mama Fulani ma fada kawai take ta inda take shiga ba ta nan take fita ba har da cewa zata shirya taje sokoto sai da Abbah ya taka mata burki, gaba daya ta hana kowa zama lafiya ciki kuwa yar da yayanta haushin auren da zaba daura gobe ya addabi zuciyarta.
Ammy ce kawai da yayanta suke murnar abun domin ta san cewar Ataa ta samu mijin daya dace da ita kuma wanda zai kula da ita, abun har mamaki yake ba su yadda Aliyu ya fada son Ataa a haka, a daren ita da yayanta kwana sukai suna ta zancen masu cewa daman sun lura da kaza da kaza suna ta yi.

ATAA POV.
Chapter 96 · 0% Book details