Sashe 61
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Dagowa yai ya kalleta kamin ya kai hannu ya karbi wayar ya buga ta da kasa iya karfinsa a take wayar ta watse Ataa kuma tai ihu tai baya a zatonta wani abun zai mata.
*ZAKI
By Khadeeja Candy
30...
Daga gidansu Rahma gidansa ya dawo, sai ya tsaya a cikin mota ya kwantar da kujerar baya ya kwanta hannayensa rumgume a kirji. Gaba daya wunin yau be masa dadi ba, tun da yake a rayuwarsa be taba samun kansa ciki matsala irin wannan ba. Rahma a gafe ga Ataa and now Muhseen, sai a yanzu yake nadamar sanar da Momy abunda ya faru tsakaninsa da Muhseen da bata cilasta masa ya kira shi ba, da ransa be bace kamar haka ba. Ya dade a zaune cikin motar sannan ya bude ya fito ya shiga cikin gidan kai tsaye dakinsa ya wuce, ya kwanta be tashi ba sai kusan sallah magariba, tufafin jikinsa ya cire ya shiga bathroom yai wanka tare da alwala ya fito ya sake shiryawa cikin wasu tufafin ya feshe jikinsa da expensive perfume sannan ya fito ya sake shiga motar ya dauki hanyar gobirawa, a masallacin unguwar ya tsaya yai sallah kusa da wani mai siyardar nama, bayan ya gama ya shiga wani babban shago ya zabi waya mai tsada ya biya da ATM dinsa sannan ya fito ya shiga motarsa a cikin motar ya fiddo wayar ya kunna sannan ya soma driving da hannu daya. Har ya isa family house dinsu Arkilla, kusa da inda ya fasa wayar ya faka motarsa ya sauke gilashin motar yana kallon yadda wayar ta watse, da duhun magariba amman ko'ina haske ne kamar rana, ya dade yana kallon gurin sim dinsa da memory yake son cirewa ya saka a wannan wayar amman baya son taba wayar gaba daya ta fice a ransa. Fita yai daga motar ya nufi kofar falo ya shiga, Siyama kawai ya samu a ciki tana kallon rawar babban yaro a plasma tana koyon yadda suke, sai dai ganin Aliyu ya saka ta saurin zaunawa tare da canja channel din da take kallo zuwa wata dabam.
“Sannu da zuwa Ya Aliyu”
Sai da ya karewa falon kallo sannan ya ce.
“Ina Ataa da Husna?”
“Ataa tana asibiti Husna kuma sun fita ita da Anty Amina Momy ta aike su”
“Waya kai Ataa asibiti?”
“Kuka tai yi shine Momy ta saka Anty Amina ta kaita”
“Je waje ki dauko min sims dina da Memory”
Shine abunda ya fada sannan ya nufi dakin mahaifiyarsa, zaune ya samu Momy gaban madubi tana cire gulagulan hannunta, a gafen gadonta ya zauna yana cirewa wayar murfi, bata ce masa komai ba har Siyama ta shigo ta kawo masa sims din da memory ya karba ya saka a wayar sannan ya kunna.
“Ga abincin dare can zaka je ka kaiwa Ataa asibiti”
Momy ta fada bayan Siyama ta fice daga dakin.
“Momy ba za a bawa Siyama ko Amina ta kai ba?”
“Kai na ga dama, ka ce kana son taimakawa yarinya amman kana kokarin bata kanka a gurinta, wata rayuwa kake daukarwa kanka wace zata kara saka yarinyar ta tsane ka kuma ta yarda cewar da hadin bakinka aka cutar da ita, fasa waya a gabanta daka mata tsawa, ko zare mata ido ba ba zai kara maka komai a gurinta ba sai tsana”
“Ba saboda ita na fasa waya ba”
Ya bata amsa yayinda yake kunna wayar.
“Saboda Muhseen ko? Kana jin cewar ka ragu saboda ka kira Muhseen ka bata sun yi waya right? Shi bata waya suyi magana wani laifi ko abun jin zafi”
“Momy Muhseen kanena ne, be kamata yai min haka ba”
“Shikenan dan yana kanenka ba zai iya cewa ka kaiwa wani yai waya da shi ba? Wannan wane irin jin kai ne da kai haka?”
Yayi shiru be ce komai domin yana tunanin duk abunda zai fadawa Momy ba fahimta za tai ba, Mama Fulani ce kawai take fahimtarsa har ta goya masa baya, kuma bata taba masa magana akan wannan ba.
“Zaka je ko na tashi naje da kaina”
Dagowa yai daga kallon wayar da yake ya kalli Momy wacce ta daure fuska.
“Zanje Momy amman kamar kina fushi da ni, kuma kin san ina damuwa idan ke da Mama kuka fushi da ni”
“Bana jindadin yadda zamantakewar ku da Muhseen yake sam, ita ma kanta na san ba dadi take ji ba, tana kyale ku ne kawai saboda babu yadda za tai”
“Momy matsalar ba daga ni ba ne daga Muhseen ne ya cika son shiga rayuwata ne kawai”
“Ka gani ba, wannan halin na ka shi yake bashi haushi yake ba kowa ma haushi, kai baka taba yarda cewar ka yi laifi ba, baka tana yarda ace kaine mai laifi sai jin kai da son wulakanta kowa, babu abunda ka rage a halin Fulani kuma Wallahi wannan dabi'un ba su da ce da kai ba”
“Momy kawai kina son ganin laifina ne ki bawa Muhseen gaskiya bayan shi ne yake abunda be da ce”
“Na sani wani lokacin yana yin abunda be dace ba, amman ka fi zurfafa sama da shi, and dole na bawa Muhseen gaskiya na kare shi kamar yadda nahaifiyarsa take maka, ba zan taba yarda ka ce zaka ciwa danta mutunci ba ko ka wulakanta shi ba, ku rika abu kamar ba yan'uwan juna ba, kana ikirarin kai babba ne amman baka iya kawar da kai daga ganin wani abun ka ka kyale?”
Kansa ya mayar gurin wyar yana ta taba ba dan kuma yana bukatar tabawarba sai dan be san abunda zai cewa Momy ba, har tai fadanta ta gama ta fice daga dakin be ce gama be sake cewa komai ba. Bayan ajiyar zuciya daya sauke ya fito daga dakin ya nufi dinning inda Momy take hada kulolin abinci da kwadon da saka plate a ciki da spoon ta mika masa.
“Idan ka je kuma ka daka mata tsawa idan bata karba ba”
Murmushi yai ya karba ya nufi kofa Siyama kuma ta dauki ragowar kulolin ta saka masa a mota har ta juya zata koma ya kirata.
“Shigo muje idan munje can za ki rika kayan”
“To”
Ta fada tana bude front seat ta zauna shi kuma yai ma motar key suka kama hanyar asibitin. A inda ake faka motoci ya faka motarsa sannan bude motar ya fito ya bude gidan baya ya dauki kwandon plate din da karamar kula Siyama kuma ta riko mayan kulolin guda biyu ta dora daya saman daya. Security din na ganin zubinsu ya san ba irin zubin mutanen da zai tarewa kofa ba ne, da kansa ma ya bude musu ward din Anas room suka shiga. Aliyu ne a gaba domin shi ya san inda dakin yake Siyama na biye da shi a baya har suka isa cikin dakin.
Tura kofar kawai yai ya shiga ba tare da sallama ba, sai dai yana kokarin sakin fuskarsa duk da ba murmushi yake son yi ba. Zaune ya samu Ataa saman gadon da mahaifiyarta take kwance tana bachi, Doc Bukar kuma na zaune saman kujerar da ke fuskartar Ataa yana nuna mata abu a laptop dinsa, babu Hijab a jikinta sai dankwali gashin kanta a waje ta rike shi tana wasa da shi tana kallon video a laptop. Haka kawai sai Aliyu ya ji babu dadi samun su haka, baya son ganin Ataa da wani namijin a yanzu dan gani yake kyaunta zai iya jan hankalin wani namijin ya cutar da ita. Duk yadda yai kokarin sakin fuskarsa sai zuciyarsa tai masa ba dadi. Kusa da Doc Bukar Siyama ta aje kulolin hannunta sannan ta karbi na Aliyu ta aje kasa, da gangan Aliyu ya kasa cewa Doc Bukar komai sai kokarin danne bacin ransa yake.
“Aliyu ka shigo”
Doc Bukar ya tambaya yana rufe laptop din da murmushi a fuskarsa.
“Eh”
Mike tsaye Bukar yai yana fadin.
“Ka yi waya da Muhseen din?”
“Na yi”
Yadda Bukar yaji Aliyu na amsa masa magana da a take kuma babu sakewa ya san ransa ne a bace sai dai be yi zaton ganinsa da Ataa bacin ran nasa ba, a zatonta wani abun ne dabam yake damunsa.
“To ni zan wuce yar Fulani sai jango ko?”
“To sai da safe”
Ataa ta fada murya kasa kasa shi kuma ya juya ya fice yana murmushi. Duka duka yaushe aka Ataa ta zo asibiti da har zata sake da Doc Bukar haka shine abunda ya tsayawa Aliyu a rai.
“Ina Hijabin ki?”
Ya tambaya da kamar fada, har Siyama ta kalleshi.
“Gashi”
Ataa ta fada tana dauko shi daga gefen Nana ta maida saman jikinta. Har ya bude ba ki kamar ya sake cewa wani abu sai kuma yai shiru ya maida dubansa gurin Nana.
“Ya mai jiki”
Siyama ta tambaya.
“Alhamdulillah da sauki”
Ta fada tana kallon Aliyu da fuskarsa ke daure. Juyawa yai ya fice daga dakin ba tare da ya sake cewa komai ba. Siyama tai saurin binta tana ma Ataa Allah kyauta. Rai a bace ya shiga motar yana ta mamakin yadda maza suke sakewa da mace da sun ga kyau su yi ta rawar jiki.
“Mtssssssss”
Yaja tsakin daya saka Siyama kallonsa kadan tai saurin kawar da kai, tana tunanin abunda tai ba daidai ba da har ya saka shi tsaki. Be shiga cikin gidan ba ya tsaya bakin gate ba tare da ya danna horn ba, Siyama na ganin hakan ta san baya son shiga ciki ne, sai ta bude motar ta fita shi kuma yai ribas ya juya, yana driving wayarsa tai ringing kallonta kawai yai ya dauke kai rabon da yaji ringing din waya indai ta shi ce har ya manta, dan shi baya son ringing sai dai ya bar waya a silent ko vibration. A bakin gate din gidansu Rahma ya faka motarsa sai a sannan ya kai hannu ya dauki wayar yana duba yadda Nasir da wata bakuwar number suka jera masa missing calls hudu ya saka wayar vibration sannan ya shiga text ya aikawa Rahma sako.
RAHMA POV.