← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 134 OF 143

Sashe 134

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Mijinki na bukatar kulawarki a yanzu fiye da ko yaushe, na san ba ki san wata dawainiyar ba, amman kula da abincinsa ya ci ko be ci ba yana wuyanki a yanzu, karki zamana shi kadai zai dinga damuwa da ke, mijinko ya rasa daya abokiyar rayuwarsa hakan kuma ba karamin jefa shi yai a matsala ba, sai da taimakonki zai iya dawowa dai da ya manta komai kamar be faru ba, ki shimfida masa kalar rayuwar da kike son yai kuka ya bi saboda yana tsananin son ki ni na sani, na san ke ma kuma kin san da haka, ki rika yi masa abunda zai kwantar masa da hankali da saka shi natsuwa, hakan ba karamin kara mishi son ki zai yi, a yadda yake damuwa da ke kuma yake son ki idan kina nuna masa damuwarki akan rashin cin abincinsa zai ci saboda gudun damuwarki kuma zai sa ya rage damuwar, tun da akai mutuwar bana jin ya saka wani abu a cikinsa har yau sai ruwa, sannan ki rika yi ma mijinki addu'a a duk sallah musamman a sujadar karshe da kuma bayan tahiya kamin ki sallame, mace mai aure ma ba akarbar addu'arta har sai idan tana yi ma mijinta da kuma iyayenta”

“In-Sha-Allah Momy”

“Kuma ke ma ki kula da kanki, wani abun ba sai ance ki yi ba, ya kamata ace kin san aure kike a yanzu, kuma ke ce kadai a gurin mijinki, mijinki na bukatarki a yanzu fiye da ko yaushe, ina fada miki wannan ne saboda na san zaki iya kuma ke kadai na ke da tabbacin za ki saka shi cikin walwala a yanzu, mijinki be iya so ba, be iya ki ba, ba kuma iya sakawa rai abu ba, idan yana so gaba daya yake so baya ganin aibun abun har sai yayi zurfi a ciki, idan kuma ya tsane abu gaba daya yake tsanarsa baya iya ganin kyaun abu har sai yayi nisa a tsanarsa, idan kuma ya sakawa rai abu yana sakawa sosai ta yadda rashin abun nan zai yi ta damunsa yana cinsa a rai, daga ke har shi ni duk kallon yara na ke muku wani abu dole sai an nuna muku, saboda mun fi ku tunani da hangen nesa, na san ba ki yawance a komai ba, sai dai ke din jajirtacciya ce saboda gwargwarmayar rayuwa da kika sha, da kurciyarki kin fuskanci kalubale kala kala na rayuwa kamin yanzu, kuma da Allah ya tashi miki sakamako sai yai miki duka a lokacin da kike bukatar hakan, hakuri yana da kyau kuma yana da riba sosai duk wanda yai hakuri be ga riba ba to kadan yayi”

Sosai na jidadin magangannun Momy, a natse ta fada amin komai kuma na fahimci manufar da nufi, daga lokacin na sakawa kaina zan iya, kuma na fara jina a matsayin mace mai aure mai daraja wacce zata iya kula gidanta da mijinta da kuma yayanta duk kuwa da irin karancin shekaruna. Idan na waiwaya baya kadan na tuna abunda ya faru da ni irin halin rayuwar da muka shiga da fadi tashi da nai sai na ga wacan rayuwar kamar labari aka ba ni ba ni ce na wanzu a cikinta ba.

“Tashi ki bi mijinki ku kwana a can”

Maganar Momy ta katse min tunanin da nake.

“Ba ki bukatar komai dai ko?”

“Babu”

Na fada ina mikewa tsaye na dauki Hijabina na saka, sannan na fara takawa a hankali har na fito falo.

“Matar yaya ina za ki je?”

Siyama ta tambaya tana kallona da murmushi a fuskarta.

“Gida zamu je”

“Ba anan za ku kwana ba?”

“Eh”

Na amsa mata muryarta da kamar damuwa. Sannan na karasa kusa da Mama Fulani na dan risina na ce mata.

“Mama za mu tafi gida sai gobe”

“To Allah ya tsare”

Ya mayar min tana kallona, sannan na karasa gurin Ammy ita ma nai mata sallama da wasu kannen Momy da yan'uwan Daddy sannan ya fito harabar gidan. Na yi mamakin ganin Muhseen tsaye jikin motar Hamma yana magana da shi, ban san mi yake fada masa ba na ga dai Hamma ya gyada kai sannan ya bude min gaban motar tun kan na karaso.

“Ataa”

Kiran da Siyama tai min ne yasa na juyo sai ta nufo ni da yar karamar dogowar kular silba a hannunta.

“Ga shi wai Momy ta ce ku tafi da shi”

“Mun gode”

Na fada bayan na karba, ko da na juyo ban ga Muhseen ba balle mafarinsa sai Hamma tsaye yana ta kallona har na karasa, hannu ya kai ya karbi kular hannuna sannan ya matsa daga jikin motar wanda hakan ya bani damar shiga ciki na zauna shi kuma ya rufe motar, ya zagaya bangarensa ya shiga yai ma motar key.
  A hanya ya rika tambaya ko ina son wani abu, sai na ce masa bana bukatar komai, amman duk da haka sai da ya tsaya ya siya min gassashiyar kaza da yoghurt.

“Bana jin yunwa fa”

“Za ki iya bukata da dare ai, kuma ba dan ke kadai na siya ba”

“Dan wa?”

“Babyna”

Ya fada min fuskarsa babu walwala. Har muka isa gida ban sake ce masa komai ba shi ma kuma be ce min ba, har sai da ya faka motar na kai hannu zan bude.

“Tsaya ba ri na bude miki”

Fita yai ya zagayo gefena ya bude min motar na fito sannan ya rufe, ina gaba yana bayana har muka shiga cikin falon, sai ya zauna saman cushion yana ta kallona.

“Na hada maka ruwan wanka?”

“Zo nan”

Zuwa nai na zauna saman kafafuwansa kamar yadda na bukata sai ya rumgume yana sauke ajiyar zuciya a hankali sai dai hakan be hana ni jin saukarta. Mun dade a haka kamin ya barni na daga jikinsa mu shiga daki, rumguma a cikin abunda Hamma ya ke so kuma ni ma nake so domin ina jin natsuwa sosai idan ya rumgume ni hakan kuma yana kara min jin son kusanci da shi sosai. Cikin jikinsa na kwana kamar kullum sa'a daya nai ban farka cin abincin dare kamar yadda na saba ba. A lokacin da muka gama sallah asuba kuma sai na nufi kitchen na bar a dakin yana karatun qur'ane ni kuma na shiga na kunna gas din na sarrafa dan abunda na iya na ruwan zafin tea da suya wainar kwai da dankali sai kuma doya, sannan na bude kular da Momy ta ba mu jiya, farfesun kayan ciki ne a ciki, sai kawai na dora su akan wuta na dumama na juye a wata kular.

“Wow da kanki kike girki, na fada miki bana son wahalar nan da kike miyasa ba ki jin magana”

“Dan na yi aiki ba komai cikin zai yi ba, kuma ni bana son abincin waje”

“To amman sai ki bari idan na gama karatu Quranen na hada ko?”

“Bana son girki na namiji”

Wannan karon yayi kokarin fadada  fuskarsa da abunda ya rasa daga lokacin da akai mutuwar nan zuwa yau wato murmushi shi ma kadan.

“Kin taba jin inda da zai ce baya son abincin babansa”

“Haka dai yace wai babansa be iya girki ba, idan ma yayi babu dadi shiyasa nake turo min shi nai amai”

Na fada ina yatsina fuska, sai ya kara matsowa kusa da ni ya rika hannayena.

“Karki masa karya, na san ba zai ce haka ba, ta ina ma kika ji ya ce haka? Yaushe kika iya karya”

“Yanzu”

Na fada da kamar kunya, sai yai murmushim gefen fuska yana aje numfashi. Shi ya taimaka min na karasa hada komai, sannan muka karya, be wani ci da yawa ba shi ma kuma dan na matsa masa ne, ni kan na ci abincin sosai kamar wacce ta kwana da yunwa, ni kaina har mamakin yadda na ke cin abinci sosai na ke kamar ba cin lafiya ba.

***  ***   ***

Har akai zaman makokin aka gama Mommyn Rahma bata koma normal yadda take ba, damuwa ta taru a ranta ta tsaya mata, ba ita kadai ba gaba daya gidan babu wanda mutuwar Rahma bata taba shi ba, yau duk wani abu da Rahma ta mallaka na jindadi da dangi da kaunar iyaye da miji yau ta tafi ta barsu, mutuwa ta ishi kowa wa'azi, yau iyayenta sun ga Abunda kudi ko iko ko milki ko isa basa badawa wato rayuwa, komai ikon ka da isarka da milkinka baka isa ka hana mutuwa daukarka ba, kamin mutuwarta sun ga abunda ya kamata yace ya zame musu ishara, na juyarwar al'amarin da ba su taba zaton zai zame musu haka ba, duk wani abu da Daddyn Rahma ko mahaifiyarta ko ma ita Rahma da kanta take takama da shi na familyn Ataa ne yarinyar da suka wulakanta suka maida ba komai ba, a karkashin inuwar kakanta suke takama ta gidansu ce, ita din da suke gani ba komai ba Allah ya mayarda ita saman su, wani karin bakinciki ma ta zama ita kadai a gidan Aliyu babu yarsu a gidan balle tai kishi da ita. Yau sun koma sune kasa ta ko wane bangare.
Chapter 134 · 0% Book details