Sashe 100
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Kuka take sosai, tun Muneera na lallabata har ta gaji ta zuba mata ido kamin ta tashi zuwa dakin yayansu inda ya tare da matarsa, after zuwan Muneera da Rahma shi ma ya zo hutu shi da matarsa. Kusan shi yake kula da Muneera da Rahma a lokacin da ya zo garin.
Duk yadda Muneera da Yayanta suka so ta kwantar da hankali ta manta da Aliyu ta zauna a nan sai ta kasa gaba daya ta fita daga hayyacinta sai kuka take ta rasa inda zata saka kanta. Sosai yayan nata ya ji haushi yadda take kuma ta tashi hankalinsa domin shi ma yana ganin Aliyu ya nuna musu rashin kunya da kuma tozarci domin shi ma a ganinsa abunda Aliyu yai be kyauta ba taya ma zai auri wata mace bayan matarsa ba lafiya tana a cikin halin da take bukatarsa a maimakon ya nuna mata kulawa sai ya nemi kara aure wannan ma ai abun kunya ne kuma abun kataici.
Har daga Mommynta sai da ta kirata da kanta ta fada mata ta kwantar da hankali ta zaunawarta a Dubai ta huta amman ta kasa bawa zuciyarta hakuri, a dole suka fara shirya komawarta gida Nigerian a gobe ita da Muneera wacce ta rakota shi kan ba be shirya komawarsa yanzu ba domin be gama shakatawarsa ta matarsa ba.
ATAA POV.
Siyama na gana ina biye sai wata tafiya na ke kamar mai jin nauyin taka kasa, gaba daya kunyar Nana nake ji na kasa sukuni na kasa sakewa har muka shiga dakin da take. Siyama tai sallama ni kuma na kasa cewa komai sai na zauna kusa da kofa kaina a kasa, Siyama kuma tai dariya ta fice.
Gyara zama nai na rike hannyena ina ta wasa da su a cikin gyalena.
“Al-hamdulillah na gode da ya nuna min wannan ranar, yau rana ce mai cike da farinciki a gurina, ban tsammaci zuwanta a lokacin da na ke raye ba, kuma ban tsammanin zuwanta a nan kusa ba, amman sai ga shi komai ya zo ta yadda ban yi zato ba, na gode Allah da yasa ina da rai akai auren nan”
Dagowa nai na kalleta sai na ga hawaye a idonta murmushi kuma a fuskarsa. Sake maida kaina nai kasa domin har lokacin kunya na ke ji ni irin kunyar da na ke daga lokacin da aka daura auren nan zuwa yau har mamaki take ba ni domin ban taba sanin ina da ita ba sai a yanzu. Bayan sallah isha'i Hajiya Ramatu ta shigo bangaren da muke ita da Momy suka gaisa da Nana sai Momy ta ce min na tashi na je part dinta za tai magana da Nana. Ni kuma na tashi na fice ban je part din nata ba na zauna a gurin da ake aje motoci na zauna ina ta tunani ni kadai, cikin kuwa har da tunanin Rahma, ko a wane hali take a yanzu ko kuma zata ji idan ta ci cewar Aliyu ya aure ni, Mama Fulani ma ya za tai na san dai ba zata taba so na ba, ita da Rahma kuma za su iya ci min mutunci ko goranta idan suka ganni wata kila ma har duka sai Rahma ta yi min tace na aure mata miji, ko tana Abujar ma ko tana nan oho. Haka nai ta kawo wacan ina ture wannan har na soma jin bachi a gurin, can kuma su ka fito daga bq din Momy na takawa a hankali tare da kawarta har suka iso gurin motar kawar tata, a lokacin ni kuma na mike tsaye da zimmar komawa Bq din sai Hajiya Ramatu ta rike baki.
“Laa yanzu a nan kika zauna? Ba ki je falon Hajiya ba?”
“Kunya ta ke ji daman na lura da takunta ai”
Ni dai na wuce ban ce komai ba sai watsa na ke da yan yatsuna, lokacin da na shiga bq na yi zaton Nana zata fada min wani abun akan zuwan Momy gurinta amman bata ce min komai ba sai dai tana ta kallona tana murmushi. A katifa daya muka kwanta kamar yadda muka saba sai dai jin kunyarta be hanani shigewa bayanta nai bachina ba har gari ya waye. Misalin bakwai da yan mintuna Momy ta aiko Husna tana kirana, bata jira mun tafi tare ba ta juya ta fice. Ni kuma na mike tsaye na dauki Hijab dina ina kokarin sakawa Nana ta ce.
“Kin yi dacen suruka indai abun ya bi haka za ki jidadin zama da ita”
Na kalleta sai kuma na sauke idona kasa, kamar na tambaya abunda ya Momy ta zo yi jiya a nan sai kuma na dauke kaina na fice daga bq din, kamar jiya yau ma da kunya na shiga part dinta sai na samu tana zaune falo ita kadai tana kwaba fulawa. Har kasa na kai na gaisheta ta amsa min da murmushi a fuskarta.
“Shiga kitchen akwai tarugu da albarsa ki gagga min zan shigo yanzu”
Tashi nai na shiga kitchen din sai na samu tarugun ta albarsa a cikin roba an aje kasa ga kuma turmi a kusa, bude turmin nai na yanka albarsa na fara dakawa sannan na zuba ta rugun na dake su a tare, ina karewa tana shigowa sai ta aje fulawar ta kunna fanfon kitchen din ta wanke hannunta.
“Hadewa kikai?”
“Eh a tare na same su”
“Eh ko a tare ne ai za ki iya rabawa saboda wani lokacin ba komai ake hadewa ba, wani abun baya son albasa da yawa wani kuma tarugun ne ba za a saka da yawa ba, shiyasa ake son rabawar, daga yau karki sake hadewa idan kina jajage kinji?”
“To”
Daga haka ta nuna min inda zan murda a jikin gas din sannan ta miko min wani abu mai dan tsawo ta nuna min inda zan matsa wuta ta fito na sai na saka a gas din cikin tsoro nai hakan sai ga gas din ya kama da karfi sai kuma ya nuna min gurin ragewa da kuma yadda zan daidaita wutar. Dayan ma sakawa tai na kunna da kai ta na dora ruwa a kai ta bani boya wacce aka gyara ta ce na zuba a ciki kuma na rufe, sannan ta littafamin yadda zan soya tarugun da albarsa da yadda zan zuba kwai idan ya soyu sannan ta fita ta bar min kitchen din.
Sosai na maida hankali ina yin yadda ta ce sai dadi na ke ji yau zan yi girki irin na masu kudi da kaina, sai dai tsoron gas din na ke ina ganin kamar fashewa zai yi ko kuma ya ja ni idan ina matsawa kusa.
“Tace na soya tarugun da albarsa idan ya soyu sai na rage wutar na fada kwai na kada na saka magi a ciki sannan na zuba kwai ciki kuma kar na motsa idan yayi sai na saka wannan katon cibin na juya shi kar na bari ta karye ko ta yamutse, idan ta yi tace na saka a wannan kular nai haka har sau...... ”
Ban karasa ba fadar abunda ke bakina na ji an riga kunkuru an doro min kai a wuyana.
“Mi kike hadawa?”
Saurin janye jikina nai na juyi ina ta kyarma irin na tsoro.
“Ina wuni?”
“Ina kwana?”
Ya fada yana jan kumatuna, sai nai kasa da kaina. Waiga yai ya kalli kofar kitchen din sannan ya saka hannunsa biyu ya rika fuskata ya sumbace saman lips dina. Sai yai saurin juyawa ya fice yana murmushi, wani irin kazanta na ji kamar na cire bakina gaba daya, da sauri na na zuba omon da ke kusa da fofon na wanke saman bakin nawa da shi ina ta jin kyankyami. Ina dagowa sai na ganshi yana kallona sai kuma kunyarsa ta rufe ni, murmushi yai ya karaso kusa da ni ya sake rika fuskana ina jin kamar na masa magana ko nai ihu sai kuma na kasa yi sai kunya na ke ji wannan karon na iya saman bakina ya sumbarta ba, bakinsa ya saka cikin nawa ya rika jan yawu bakina yana hadewa yana ta wasa da halshensa a cikin bakina daga karshe ya turo min yawunsa kuma ya kwanto da ni hannunsa wanda hakan ya cilasta ni hadewa. Rumtse ido nai ma matse hannuna da jikina ina kokarin kankamewa guri daya, a dole sake ni sai ya bude kofar bayan ya fita daga kitchen din. Kakarin amai na fara yi wai ko yawunsa da suka shiga bakina za su fito na mayesu ashe Aliyu kazami na musamman duk tsabbatarsa ta banza ce, taya ma zaka saka bakinka a cikin bakin wani har ku yi musanyar yawu, ni da bana iya cin abinci a saitin bakin da wani ya ci ma.
Na fi karfin minti goma ina ta kakarin aman sai kyankyami na ke ji ina ta tofarda yawu, sannan Momy ta shigo, ita ce ta lura da tarugun ya wuyu har ya fara konewa ma ni ban kula ba.
“Mi kike har yai haka?”
Na yi shiru ina ta tunanin abunda na ke, sai ta rage wutan ta fasa kwai da kanta ta mika min na zuba, har muka yi breakfast din muka gama Aliyu be sake shigowa kitchen din ba, ni kuma ban daina tara yawu a bakina ina zubawa a gurin fanfan kitchen din ba sai na zuba ruwa dan bana son Momy ta gani. Bayan na gama ita ta gasa tai sauran sai muka dawo falo muka jera komai. A gurin jerawar ma sai da ta gwada min yadda zan yi da kuma yadda zan aje komai a muhallinsa.
Sannan ta zuba mana na mu ni da Nana ta ba ni, sai da zan wuce sannan na lura da Aliyu da ke zaune saman cushion yana danna wayarsa kamar ba shi ne yai min abunda yai min dazun ba.
“Aisha kun gaisa?”
Momy ta kirani sannan ta fada kamin na amsa ya dago kansa ya kalleni fuska.
“Aa”
“To idan kika ganshi ki rika gaishe shi hakan na da kyau kinji, kuma kamin ki karya ki wanke bakinki da brush”
“To ina kwana”
“Lafiya kalau”