Sashe 26
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
“Ko ma mi akai mata ai ba mu muka ce ta siyar da kodarta ba, irin talakawan nan da kake gani Aliyu ba su da komai a ransu sai hassadar nai arziki, idan suka ganka da arziki ji suke kamar su kashe ka su kwashe dukiyar, shiyasa tsakaninmu da talaka aiki kawai mu biyashi, wata banza a banza bata isa ta shigo har cikin gidanki ta fada miki maganar banza ba, watan ma kuma talaka!”
“Daddy har da kai ta ciwa mutunci, wai a gidanka ta raba ka koreta ni da kai duk ba musan darajar talaka ba”
“Zan sa a binciko yarinyar da iyayenta sai na nuna mata ruwa ba sa'an kwando ba ne”
Duk abunda ake Aliyu ba ce uffan ba, har Daddy yai musu sallama ya fita, a lokacin ne Rahma ta tashi ta nufi dakinta, shi kan sai da yaji tashin motar surukinsa sannan shima ya mike tsaye ya bi bayan Rahma. Gaban madubi ya same ta zaune tana cire dankunnen da ke kunnenta, kusa da ita yaje yai mata kissing sannan ya zauna gefen gadon yana kallonta.
“Miyasa za ki kira Daddy ki fada masa maganar da bata kai ta kawo ba?”
Da mamaki ta kalleshi
“Wannan abun ne be kai ya kawo ba? Yarinya karamar yar talakawa kamar wannan ta fada min magana son ranta ka ce be kai ya kawo ba? Aliyu ka san me kake fadi kuwa?”
“Amman ai zalintar ta akai? Yanzu kuma sai ki fadawa Daddy bayan kin san zai iya daukar wani mataki?”
“Amman mu muka zalince ta? Daman can matakin na ke son ya dauka shiyasa na kira shi na fada masa, tun da kai ka kasa komai sai ma rike min hannu da kai dan kar na dake ta”
“Sanadinmu aka zalince ta, kodar mahaifiyarta aka cire Rahma aka dasa miki? Kuma kike tunanin ba zatai wani hargagi na huce haushinta ba?”
Juyo tai gaba daya ta kalleshi da kyau.
“Kana magana Aliyu kamar ba kai ba? Lafazin da ke fitowa daga bakinta yana karantar da ni cewar ba kai ne ba?”
Hannu ya kai ya kama hanyayenta ya cigaba da mata magana a hankali kamar yadda yake mata dazun.
“Dear, zan iya juye yi wa mutum komai amman ban da zalinci, an riga an cuci yarinyar nan, kuma kodar nan an dasa miki ita wannan kadai ya isa yasa jin tausayinta waya sani ma ko mahaifiyar ta mutu”
“Tausayi Aliyu? Tausayi? Tausayi fa ka ce? Mi mukai mata da har za mu ji tausayinta? Mu muka zalince ta ne? Akan mi zaka yarda da yarinyar daka soma gani cikin kwana biyu, saman da likitan daya saba yi maka aiki shekara da shekaru? Ban taba ganinka cikin wannan yanayin ba Aliyu, ba ka taba ce min na ji tausayin wani ba, baka taba ce min kana tausayin wani ba, wanin ma talaka irin wannan yar shekara a gidanka”
“Ba tausayinta nake ji ba, ina kallon abunda akai mata ne a matsayin zalinci, and be dace ki saka Daddy a wannan maganar ba, zai iya unkura yi mata wani abu sanadinki, ni fa na yarda da wulakanta kowa na ci mutunci kowa kuma na kyama ci kowa amman ban yarda karfin iko ko dukiya su saka na zalinci wani ba, ba zan iya da hakkin wani a kaina ba”
Kai ta girgiza masa tana murmushi irin mai ciwon nan idonta na cika da hawaye.
“Ban taba yin wani abu ka ce ban yi daidai ba sai yau, ban taba daga hannu da sunan dukan wani ba ka hana ni sai yau, wani be taba fada min mummunar magana a gabanka ka kyaleshi ba sai yau, na fahimcin inda ka dosa Aliyu, ta wanke fuskarta kaga tana da kyau tana da fari tana da gashi na fahimta...”
Mikewa tai tsaye zata fice daga dakin tana share hawayen da suka zubo mata, sai yai saurin rumgumeta ta bayan ya dora kansa saman wuyanta.
“Ba kyau ba ne matsalar, ina auna irin halin da na samu kaina ne a lokacin da aka fada min cewar za ki iya rasa ranki idan ba a canja miki koda ba, na ji tsoro sosai Rahma, kullum fargabata kar na rasa ki, na shiga damiwa sosai wanda hakan yasa na fadawa Doc Asim ya samu ko koda ta nawa ce zan siya, amman ban san cewa zalintar wata zai yi ya kawo min ba, ni kenan da nake tsoron rasa mata ina ga ita da take tsoro rasa mahaifiya tana da daraja ga yayanta Rahma ko da kuwa talaka ce”
“Babu ruwanmu da rayuwar wasu, abunda muke so shi muka samu, whither ya zalince ko mu muka zalince ba matsala ba ce, tun da mun samu abunda mu ke bukata, Aliyu bana son na sake jin maganar yarinyar pls”
Juyowa yai da ita ta yadda zata fuskance shi irin fuskartar da zata famince ko wace kalma da zata fito daga bakinshi.
“No ba haka ya dace ba, idan har ba mu bata hakurin zalincin da akai mata ba, be kamata ba, be kamata mu kara mata da wani abun ba, Daddy zai iya yi mata wani abu, and maybe Doc Asim ma ba zai kyaleta ba”
Kallonsa take tana ta kokarin fahimtarsa amman sai ta kasa, zuciyarta nata raya mata cewar Aliyu ya fara son yarinyar nan ne, hawaye ne suka shiga nata zirya ta fasa cewa komai, ganin hakan yasa shi saka bakinsa cikin nata ya tsotse bakinta tas sannan ya matso da ita baya suka zauna bakin gado ya rumgume ta.
ATAA POV.
Tunda aka tsayar da maganar zuwa aikina Abuja na fara koyon wanka akai akai kamar yadda Maman Salma ta fda min cewar Abuja ba a kazanta, baa gulma ba a wasa duk abunda ya kai mutum shi yake yi, wani lokaci a rana sai nai wanka biyu ma, wankin baki kuwa ba a magana, akai akai na ke saka gawayi ina wanke bakina gudun kar na je ace yana wari, yadda na ke ta jin labarin Abuja a gurin Maman Salma sai ji duk na gagara na je kamar wacce zata je wani guri gurin jindadi ba aikatau ba.
Sai duk wannan zumudin da murnar da nake idan tuna cewar zan tafi na bar Nana sai hankalina ya tashi na ji babu dadi, duk kuwa da nasan cewar ina bukatar aikin, kuma idan har na daure nai na san zan samu kudi kuma, kudin za su mana amfani sosai. Sai kullum Nana cikin nuna bata son tafiyata take, tana ta ganin kamar idan nai nisa da ita zan dawo na tarar ta rasu ne.
Ana saura kwana biyu mu tafi Abuja kamar yadda Maman Salma ta fada mana, na shirya ni da Farida na raka ta bayan unguwarmu gurin kitso, ba mu dawo da wuri ba, kasancewar mun tararda mutun hudu suna jiran kitson, ga shi idan muka hadu da Islam mai kitso abun ba dama gurin fira da dariya, muna hanya ana kiran sallah la'asar muna tafe muna fira har muka iso gidan sai dai yadda na tararda gidan wan wulgar mana da kayan dakin Nana ya sa ka gabana faduwa, a tunanina ko mahaifiyar Farida ce tai mana haka domin bata son zaman mu a idan, yana daya daga cikin abun ya saka na ke son na samo kudi ko dan mu tashi mu bar mata gidan.
“Muna zamanmu Malam zai janyo mana masifa, ai bari ya dawo sai ya san matakin da zai dauka tun wuri dan ni ba zan yarda da zaman mutanen nan a cikin gidan nan ba, wannan iskanci har ina?”
Irin kalaman zagi da na ji suna fitowa daga bakinta ya saka na fahimci ba daga ita har ba ne. Da sauri na nufi dakin da Nana take ciki sai na sameta ta zaune tana kuka.
“Lafiya Nana miya faru?”
“Wasu mutane ne suka shigo cikin gidan nan suna nemanki, aka nuna musu ni saka ce na fada miki karki sake zuwa ki fadawa Rahma wata magana marar dadi, idan kika sake sai sun wulakanta ki, wacece Rahma kuma?”
Ta karasa tana tambaya ta.
“Matar da ta koreni aiki ce”
“Fada kuka yi?”
“Kawai dai mu samu dan sabani ne, ta ce talaka ni kuma na fada mata bakar magana”
“Ataa dan Allah ki kama kanki, kin ga dai ke ba yar kowa ba ce, kar ki janyo mana wata matsalar muna neman abunda za mu ci”
“In-Sha-Allah ba zan sake ba, wacan din ma kuskure aka samu”
“Ina son ki min alkawari idan kin je Abujar nan, duk abunda za a miki za ki yi hakuri ki hade, ba za ki saka shi a ranki ba”
“Na miki alkwari Nana”