← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 116 OF 143

Sashe 116

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Na gyada min kai, da sauri na tashi na bar cin abin ma na shiga nai wanka ina fitowa ya shiga kamin ya fito har na shirya daman can shine ba mai wahala ba ne, shi ma agaggauce ya shirya muka fito tare muka shiga motar. Ba zan iya fadar ungwar da muka je ba, domin ban san ko'ina a cikin garin Abuja ba, sai dai zan iya kwatanta da unguwar manyan mutane domin ta wani bangaren ma tana kama da Las Vegas irin rayuwar nan ta ba ruwa ko da kowa. Gaban wani katon gate Aliyu ya faka tsaya ya danna horn sai ga wasu manya kuma kanttin maza sun bude masa gate din, da sauri na rike hannun Aliyu sai yai murmushi ba tare daya kalleni ba, manyan motoci a cike a gidan na alfarma, bayan motocin ya faka motarsa ya fito ya zagayo inda nake ya bude min na fito daker domin ni gaba daya tsoro ya gama kama ni. Hannuna ya rika ya nufi wani guri da ni da alama shi m be san kan gidan ba, domin kuwa sai da ya kira wayar Abbah ya fada masa mu na waje sai aka turo dogare ya zo ya tafi da mu.
Cikin wani irin katon falon muka shiga mai kama da fada, komai na falon mai tsada ne da tsari irin manyan sakuna. Ganin hoton Mai martaba sarkin Agadaz yasa hankalina ya kwanta na fahinci cewar a gidansa ne muke, na yi zaton a falon za mu tsaya sai na ga mun shiga wani falon mai kamar wacan, haka muka wuce falo uku sannan muka iso cikin wani madaidacin falo, a nan na hango sarkin hakimce a akan kujera, babu rawani a kansa kamar jiya sai dai yana sanye da alkyabar sarauta irin mai tsadar nan ga takalmin sarauta kafarsa, Daddy's Rahma na gefe zaune kasa daga dama kusa da Abbah, da sauran jikokinsa, Nana kuma na gabansa kanta a kasa tana ta sheka kuka gwanin ban tausayi da alama gafararsa take nema.
Karasawa nai gurin Nana na zauna na dafata Aliyu kuma ya zauna kusa da Abbah yana mikawa mai martaba gaisuwa shi kuma ya daga masa hannu kawai.

“Ina jin kunyar ka Mai Martaba saboda abunda na aikata, ban san cewa na aikata babban laifi ba har sai da na rasa a kusa da ni na fara shiga damuwa da bakinciki......”

“Shin abunda kika be zame miki darasi ba?”

Mai martaba ya tambaya da kansa.

“Ya zame min, na rasa komai saboda babu kai a rayuwata, na rasa gata na rasa muhallin, abincin da zan ci sai na yi bara mai martaba, gida gida na ake bi ina rabawa na zauna, har na kai ga wanda aka ga wanda aka wulakanta ni kamar karya, kuma maciji ya tsare ni, Ataa tai ta dawaniya da ni da ta kai ni asibitin sai akai amfanin da rashin kowa na mu aka cire min koda aka sakawa yar wanda ya wulakanta mu saboda rashi, Mai Martaba da koda daya n ake rayuwa saboda rashinka da kuma dangina a kusa da ni, Mai Martaba aka a kulle Ataa a gidan yan sanda saboda ba mu kowa, na rasa na da na biyu da na haifa a gurin baran kudin neman min lafiya, Mai Martaba shin duka wannan ba darasi ba ne? Da ban bijire maka ba da ban ki bin umarninka ba da duka wannan abun be same ni ba, ba ban bata maka rai bada nawa bacin rai be kai haka ba, da ban gudu na barka na bar dangina ba da wani be isa ya wulakanta mu ba”

Ta fada cikin daga murya tana kuka sosai nima kukan na ke ina rike da hannunta.

“Da duniya tai miki wa'azi miyasa ba ki koma cikin danginki ba?”

“Saboda zuciya na fada ba zaka taba yafe min ba, ba zaka taba karbarta ba, masarautar da na saka a kunya na gudu na bari, idan na shiga wahala na dawo be kamata ta karbe ni ba, ban cancanci ko kallon fuskarka nai ba Mai Martaba, amman na barwa Ya ta mawasiya na fada mata bayan raina ta neme ku ta nema min yafeyarka da duka dangina”

Shiru Mai Martaba yai na tsawon lokaci kamar baya gurin, falon yai tsif baka jin ko da numfashin kowa.

“Ban taba jin na tsani jinina ba, ban taba jin kin jinina ba ko da ko zai kashe wani ya sake kashe wani jinina jinina ne, kuma ina jinsa a cikin jinina..... Bayan neman ki da masarauta tai na kwana biyu, sai na goge sunanki a babin nema har a bada, na bar abunda kika aikata da kuma son ki a zuciyata,... Na yi tunanin idan wahala ta same ki za ki tuna da danginki ki dawo..... Da ace yau mahaifiyarki ta fadi ta mutu da ta mutu da bakincikin da kuma bakincikin guduwa ki barta, babu daren da bata begenki... Idan kowa ya taru sai ta ce kowa yana nan amman ban da Asma'u... Shin kaunar uwa kadai be isa ya saka ki nemi danginki ba......?”

Daya bayan daya yake maganar yana kallon Nana.

“Ina jin kunyar kaina Mai Martaba, ina ina nadamar abunda na aikata, bakincikin guduwa na bar ku yana nan a zuciyata, kunyar haduwa da ku ta saka na yanke kaunar daga neman yafiyarku a raye har sai bayan rai na, Ka yafe min Mai Martaba ka tausayawa min dan Allah, na sani ko yanzu ina daf da mutuwa saboda lafiyata bata ishe ni ba”

Duk da yaren buzanci suke wannan maganar ita da Mai Martaba... Shiru ya sake yi na wani lokaci sannan ya ce a katse.

“Na dade da yafe miki Asma'u, na dade da fada a gaban kowa kuma na fada a zuciyata cewar ko ina raye ko a mace na yafe miki duniya da lahira”

Da gudu ta tashi taje ta fada jikinsa ta rumgumeshi tana kuka, sai yai murmushi kowa da ke falon sai da tauyasa kuma yai murmushi ban da Daddyn Rahma da baya cikin natsuwarsa. Kuka sosai Nana tai nima nai sannan muka share hawayen mu ni da ita. Bayan komai ya lafa muna kokarin shiga natsuwar mu ne. Mai Martaba ya sake gyaran murya da yaren hausa da baya fita sosai ya ce

“Na yi hakan nan ne a gaban ku saboda ku ma ku zama shaida kuma nasan dukanku za ku son jin gaskiyar alakata a Asma'u to yanzu kun ji, ina son kowa ya zama shaida na yafewa Asma'u abunda tai min, Allah ma ka zama shaida na yafe mata duniya da lahira”

Tsakanin ni da Nana sai na rasa wa yafi wani farinciki ni ko ita. Daddyn Rahma ya daga hannunsa alamar yana son yai magana da kai martaba sai gumi yake cikin asiri.

“Mai Martaba na ce kan sai zancen nema mata hakkinta a gurin Doc Asim na cire mata koda da yai”

Kallonsa nai yadda yake maganar muryarsa har rawa take.

“Allah sarki ashe rana zata zo irin wannan dakai da bakinka zaka bude baki ka ce a nemawa Nana hakkinta? Bayan duk irin cin mutunci da wulakancin da kai mana? Waenne kalar mutane ba ka turo sun zo sun watsa mana kayanmu sun koramu ba saboda kawai mun raba a kangon gidanka ka ce mu muka janyo maka maciji a gida ka karemu ka wulakanta mu, idan har za a hukunta Doc Asim to har da kai za a hukunta domin kodar da aka cirewa Nana yarka aka sakawa”

Na fada cikin kuka. Sai shi ma ya fashe da kuka sosai kamar ba shi ba.

“Wallahi Allah ya sani idan na san cewa ku zuri'ar Mai Martaba ne ba zan taba muku haka ba, Wallahi ko shara kuke agidan Mai Martaba ba zan iya wulakanta ku ba, walle har ace jininsa habawa..... Ba hali na ba ne, ko korar da aka muku ni sau daya na fada na ce a fada muku ku nemi wani gurin ku zauna, Wallahi Hajiya ce tai ta turawa aka rakura muku, ita ma kuma basan cewa jinin Mai Martaba ba ne da ba zatai muku haka ba, Wallahi tun jiya da na fada mata abunda ya faru tana can kuka take yanzu haka..... ”

Yadda yake kuka abun ko kyau babu domin babban mutum be sha'awa da kuka ballantana shi da yake wani rakeken kato, ni dai sai kallonsa n ake da takaici a raina.

“Wanene Doc Asim to?”

Jikan Mai Martaba ya tambaya cike da mamaki. Ni kuma sai na amsa masa

“Wani ne, wani likita ne wanda na kai Nana asibitinsa lokacin ba mu da kudi sai ya ce zai mata tiyata kyauta ya cire dafin maciji a jikinta ashe yaudarata yai ya cire mata koda, ya bani wata takardar na saka hannu ashe ta siyarda kodar ce ban sani wai saboda ba ni da ilmin komai, sai da ya tambaya ba mu da kowa na ce nasa eh shine ya cire mata koda, haka mukai ta jinya bata warke ba, sai na kaita wata asibiti aka duba aka ce kodarsa ce ya cire na kai kararsa gurin police yasa aka rufeni wai ina son bata masa suna, sanadin hakan Nana ta tashi mutuwa har sai da Allah ya kawo wannan Aliyu ya taimake mu ya kaita asibiti ya ba mu ci da sha da gurin zama”

Har lokacin da nake maganar cikin kuka Daddyn Rahma ma kuka yake yi.

“Wannan ba tsakanin mu da shi ba ne, tsakaninsa da Shugaban kungiyar likitoci ne”

Shine abunda Mai Martaba ya fada a takaice fuskarsa na nuna bacin ransa karara....

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
Chapter 116 · 0% Book details