← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 98 OF 143

Sashe 98

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Aliyu ina nufin aure na sunna a daura maka irin wanda aka mana”

“Irin shi akai mana da kanwarki Aisha a yau”

“Aure fa Aliyu? Wallahi ka ci amanata ka cuce ni Aliyu ba zan taba  yafe maka ba, tun ina da rai zaka fara nuna min hakinka ba ma sai na mutu ba?”

“Wacce zata iya zaman aure ta kula da mijinki kawai na aura”

Ta tsinke wayar ba tare da ta sake cewa komai ba shi kuma ya maida wayar aljihu ya nufi cikin gida. Yana shiga wasa da dariya zoyata tsakaninsa da tabansansa ya tashi sai dai duk yadda suka tsarge shi sai dai yai dan murmushi baya cewa komai, daman can haka yake indai ya hadu da abokan wasa sai dai yai murmushi ko yar dariya kadan idan akai wani abun.
  After sallah magariba Nasir ya shiga gari domin ganawa da wasu friends dinsa. Aliyu kuma yana gida gurin Momy sai tunanin inda aka kai Ataa yake, domin ita kadai ce abunda idonsa ke son gani a yanzu, muradin zuciyarsa. Amman baya jin zai iya tambayar kowa ina Ataa ai da kunya. Sai dai ya duba yaga duka sisters dinsa suna nan ban da Amina dan haka ya tambaya.

“Ina Amina?”

“Wai tana can tare da Amarya yau duk abunda akai ba da ita akai ba”

Wata cousin sister dinsa ta fada, a take ya mike tsaye ya fito harabar gidan ya kira Amina.

“Hello Ya Aliyu”

“Kina ina?”

“Ina ina ina kebbi”

“Wasa na ke da ke?”

“Ya ina sama road”

“Ni da Ataa”

“Aisha... Anty Aisha”

Ta kara da Anty gaba daya. Ya san mutane biyu ne a sama road Mama Zuwaira wato kanwar Momy sai kuma Aminiyarta Hajiya Ramatu.

“Gidan wa?”

“Idan Mama Ramatu, amman Momy ta ce karna fadawa kowa inda muke har da kai”

Ya katse wayar ya ya koma cikin falon dan karbo keys din motar Momy domin ya baro tashi motar da duka keys dinsa a main house. A falo ya tsaya ya aika Siyama ta karbo masa key motar Momy, sai Samira ta mika masa nata.

“Ga tawa idan fita za kai”

“No”

Sai da Siyama ta karbo masa na Momy sannan ya fice daga falon ya nufi motarta ya shiga sai da ya cire babbar rigarsa ya jefa seat din baya sannan yai ma motar key ana bude masa gate ya dauki hanyar sama road yana ta tsara yadda zai ce idan ma yaje, daga karshe yai yanke shawarar tsayawa a waje ya kira Amina ya ce ta masa dabarar fitowa da Ataa.

ATAA POV.

Na kasa yarda cewar an daura min aure a yau ai ba yau bane gobe ne Saturday.

“Ko dai ba ni ba Amina ba sai gobe ba”

“Yau akai Daddy ya canja sharawa ne kawai dai ba a fada miki ba ne, amman an fadawa Mama cewa da Nana jiya da dare”

Rungume hannayena nai ina jin komai kamar ba gaske ba, murna zan yi ko kuka sai na rasa na farawa, Amina kan sai murna take har da nuna min hotunan daurin aure da akai yana tare da friends dinsa. Ni dai har bana iya gani da kyau na zama kamar wata dabam ba ni ba, duk wani abu da akai a can gidan sai da Momy ta dibo ta aiko mana, ni dai ko wanar ban iya ci ba yunwar rana ma sai ma nemeta na rasa, sai yanzu na gano dalilin sa a kawo ni nan da Momy tai. Lokaci zuwa lokaci Amina take mita wai ita kadai ce a nan sauran duk suna can suna da hidima. Da yamma Hajiya Ramatu ya hada min ruwan wanka mai kamshin gaske ta sa aka kirana na shiga bandakinta nai wanka ina fitowa ta ba ni wani bakin lace na saka ta fesa min turare sannan ta zaunar da ni a dakinta ta zubo min tuwo ta kawo min wai na ci.

“Na koshi”

“Daure dai ki ci ji idonki duk ya fada tun karin safe fa”

A dole na saka hannuna na soma ci ba dan ina jindadin tuwon ba domin ni ko sinadin miyar ba na ji, aure kawai na ke ta tunani wai an daura min aure, ji na ke kamar na saka kuka kuma babu damar shi gaba daya na ji na damu kuma ba damuwa ba, na saka sakewa a gidan kuma bana jin zan sake a ko'ina ma.
  Bayan sallah magariba ina zaune dakin ni kadai sai ga Amina ta shigo ta matso kusa da ni tana min magana kadan kadan.

“Ta so ki rakani wani guri kamin Mama Ramatu ta dawo”

Da sauri na tashi daman zaman dakin ya isheni ina nema inda zan sha iska na ga wasu abubuwan ko zan sake. Hijab ta dauko ta bani na saka daman ita akwai veil a jikinta sai kawai ta rika hannuna muka fita sai leke leke take kar Hajiya Ramatu ko yayanta ko wasu yan gidan su gamu, muna kawowa babban falon Wata yarinyar Hajiyar ta ta ganmu.

“Ke ina za ki je da ita?”

Amina tai mata alama da tai shiru kai Hajiya Ramatu ta ji. Ta ja hannuna muka fice daga falon muka bar yarinyar tana dariyar da ban san dalilinta ba. Gaba daya muka fice daga gate din sai da muka yi dan nisa muka kawo gurin wata mota sannan ta tsaya jikin motar ta bude min front seat.

“Shiga”

Kin shiga nai hango Aliyu a ciki rike da wayar da ke haska fuskarsa yana kallona. Amina bata tsaya bin ta kaina ba ta juya da sauri ta nufi hanyar gida, bude motar Aliyu yai ya fito ya zagayo inda na ke, na yi zaton ko motar zai saka ni sai nai saurin rufe gambun motar na juyo na fara takawa sai ya sha gabana yana murmushi. Takowa yake ta yi ina jin baya yana matsowa har na isa jikin motar gabana sai faduwa yake ban taba jin kunyarsa da tsoron a raina kamar na yau ba, domin duk wani tsoro da nake masa na gudun duka ne ko ba cin rai a yanzu kuma ban san na minene ba. Matseni yai sosai har ina iya jiyo numfashinsa kamar yadda yake jin nawa sai nai saurin rufe idona gam, hannayensa ya saka ya kama hannuna ya saka yatsunsa cikin nawa, dayan hannun ma haka yai masa sannan ya jinginar da fuskasa jikin tawa fuskar, hancina da na shi suma goga juna, goshinsa da nawa a hade ya lips dinsa kuma a saman nawa, numfashin da nake fitarwa yake shaka idan ni kuma zan shaka sai ya fido da nasa na shaka a haka muka dauki tsawon lokaci muna musanyar numfashi, jikina sai rawa yake sosai domin ba a taba min haka ba, sanyi na ji a kumatuna, idanuwana na bude sai gashin idona ya taba nasa, na yi zaton shi ne yake hawayen ashe ni ce, a hankali na ji lips dinsa a kasan idona yana sumbatar inda hawayen nawa suke taruwa.

“Ali...Al.... ”

Na kasa kiran sunansa balle na ce ya daina, sulale nai kamar zan duka kasa sai sai yai min masauki a kirjinsa ya rumgume ni tsantsan ko motsin bana iya yi, kaina ma saitin zuciyarsa ina jin yadda take bugawa da sauri. Sai da aka  fara kiran sallah isha'i sannan ya sake ni ya leki fuskata sai kuma ya kama hannuna ya dora a kirjinsa. Ya saka dayan yana murza yatsuna a hankali sai kallon fuskata yake. Ni kuwa numfashina sai gargada yake kamar zai fita daga jikina shigarsa ma daker ne, saurin lumashe ido nai na yi sai na ji sanyin yawunsa a lips dina, halshensa ya saka a cikin bakina, ba tsosar lips dina yake ba ba kuma tsutsa zai yi ba, a tsakanin lip din kasa da na sama ya zira halshen yana goga min dogon hancinsa a hancina. A take na fashe fa kuka saurin dagawa yai da kansa ya matsa baya sai ta juyar da ni ya jinginar jikin motar ya kwanto bayana ya rumgume ni.

“Wallahi ina cikin farinciki Babyna, ban san yadda zan misalta miki ba, ban san yadda zan fada miki ba”

“Hajiya Ramatu tace kar na dade”

Da sauri ya daga daga jikina ya juyo da ni ya rike kunkuruna.

“Ta san kin zo?”

Na gyada masa kai sai ya shafa kansa da dayan hannunsa.

“Kai Amman Amina wawuya ce”

Kumatuna ya sumbata da saman hancina sannan ya ce min.

“Wuce ki je”

Yana ba ni hanya na fara sauri kamar an biyoni har tashi faduwa nai. Da hawaye na shiga gidan ban san da hawayen ba sai da Amina ta tambayi abunda na ke yi wa kuka sannan na tuna da zaman hawayen a fuskata, saurin sharewa nai na dan turo baki kamar an min wani abu.
   Har muka kwanta a dakin da Hajiya Ramatu ta bamu ni da Amina ban daina jin jikina na rawa ba, ina ta mamakin abunda Aliyu yai min sai kyamar bakina na ke saboda halshen daya saka min a ciki daman da na je alwalar isha'i sai da nai ta wanke bakin da amma ban daina jin kyama ba.
   Washe gari muna gama sallah asuba Aliyu ya kira Amina a waya ta ba ni, ni kuma da na karba sai na saka cewa komai.

“Good morning Babyna batar kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau”

“Mashallah, Amaryata mai tsada”

Na ji kunya ta lullube ni kamar ina gansa.

“Ki ci abinci ki koshi kin ji?”

Na gyada kai ba tare da na amsa ba, sai ya ji yayi murmushi mai sauti.

“I love you....”

Ya fada kamar mai rada. Sannan ya kashe wayar, ni dai mamaki ya kasa barina gaba daya ka kasa yarda cewar Aliyu ne.
Misalin takwas na safe a kawo mana abincin karyawa kala kusan uku ni dai dankalin kawai na ci na sha ruwan sanyi domin ko tea din ban ji ina shawa'awar sha ba. Ina kokarin cire tufafina na shiga wanka Amina ta miko min wayarta wai Momy ce.

“Hello Momy ina kwana”

“Lafiya kalau Aisha kin tashi lafiya”

“Lafiya kalau”

“Mashallah kina bukatar wani abun ne?”

“Ana mana komai a nan”
Chapter 98 · 0% Book details