Sashe 133
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Shine abunda ya fito daga bakin Mama tana dafe da kirji, na san ta ji mutuwar kamar yadda na ji, abun kamar daga sama kuma babu dadi ko kadan. A nan suka shiga tambayar wacece ita, Mama ce ta fada musu ni kan sai wani sabon kukan ya kubuce min, har ga Allah ban jidadin mutuwarta ba, dan tsabanin da muka taba samu da ita sai ya dawo min sabo ina ta ganinta a fuskata. A cikin dare aka fadawa Mai Martaba halin da ake ciki na mutuwar Rahma, a waya ya kira Daddyn Rahma yai masa gaisuwa da kuma Abbah da sai aka sadashi da Daddyn Hamma shi ma yai masa gaisuwa sannan yai ma Hamma din, mu kuma aka ce mu shirya domin zuwa gaisuwa, a daren ban yi banchin kirki ba saboda tunanin Rahma ina ta ganin kamar ba da gaske ne ba, sosai na ji mutuwarta kamar wani ginshike nawa na rasa, har na soma jin ciwon kai na kama ni, da safe sai ga ni da mura, tun da nai sallah ban koma ba bachin ba, saboda tunani ashe Allah be yi zamu zauna a guri daya ba, balle ma na ga kishinta domin ni dai bana jin ina da kishin ma amman na san nata na musamman ne a yanayinta da yadda na karanci halinta.
Ko da goma tai dukan mu muna airport, wani abu sai kudi, babu zancen siya mana tickets na zuwa Nigeria, da jirgin Mai Martaba muka tafi, ni, Mama sai kuma wasu cousins dinta mata biyu, maza biyu wadanda Mai Martaba ya turo su walkice shi su yi masa gaisuwar.
Mun sauka sokoto cikin lokaci wani abun burgewa muna sauka motocin da za su dauke mu suka iso, a wani gidan suka so su kai mu mu huta kamin muje gaisuwar sai Mama da kanta ta ce a sauke gidan Momy su kuma Mazan sai su tafi can din su huta, haka kuwa akai ni da ita da wasu yayyunta mata aka sauke mu gurin Momy su kuma mazan aka wuce da su. Mun tarardar gidan da taro sai dai ba taro irin nan farinciki da walwala ba, domin kana kallon fuskarta duk wanda ke gurin kasan ba taron jindadi ne ya tara su ba. A cikin gidan kuma mata yan karbar gaisuwa, ganin taron ya karya min guiwa na san nima wata rana haka za'ayi nawa, ayi na kowa.
Husna da Siyam su kai mana lale marhabun duk da kasancewar suma basa cikin walwala sosai sai dai sun yi murna da ganina suna ta dauki ba kuma murna na marmari na kawai ba har da murnar cikin da na ke da shi. Mama Fulani kan ba wani sakewa sumi sumi da ita kamar ta Allah, Ammy da duka yaranta suna nan, har ma da su Maryam da Rukaiya duka suna nan.
Kar ka so ganin yadda Momy taks ta kokarin dawainiya da ni, sai kace wata mai tsoron ciki ko kuma wacce bata iya komai, abinci ma idan za a kawo min sai an tambayi wanne na ke so gudun kar a kawo min mai saka ni tashin zuciya. A ranar kawunai na da Mama suka koma da kuma cousins din da suka rako Mama, bayan sun yi gaisuwar a can bangarensu Iyayen Rahma, ban za ci Mama zata iya zuwa tai gaisuwar rasuwar Rahma ba, sai gashi ta maida komai ba komai ba, kana kallon mahaifiyarta zaka san a firgice take, irin figirtar nan na rasa wanda kake so a lokacin da ba kai tsammani ba, mahaifinta kan ya sha jinin jikinsa kamar ba shi ba, sai kallona suke ta yi daga shi har Mommyn Rahma.
Bayan mun dawo daga gaisuwar ne su suka kama hanya, ni kuma aka bar ni nan a gurin Momy wai sai an gama karbar gaisuwa. Ina zaune saman carpet ni kadai a dakin ina salatin Annabina na ji shigowar mutum, ban waiga ba amman na san ko wanene tun daga kan kamshin turarensa, ta kuma yadda yake takowa zuwa inda na ke a hankali har ya iso. Ji nai an rumgume ni ta baya, sai na sauke ajiyar zuciya a hankali ni kaina na san na yi marmarin Hamma sosai tun a lokacin da na zo garin nan idona suke kai kayin ganinsa, amman ban saka shi a idona ba ko gaisuwar da su Mama da yan'uwanta suka masa ina kyautata zaton sai indai a can gidansa suka same shi ko kuma ya shigo ni ban ganshi ba ya fita domin tun shigowata gidan ban ji ko alamun motsinsa ba sai yanzu. Gafen kumatuna ya sumbata.
“Fada min kina nan lafiya?”
“Lafiya kalau, tun dazun muka zo amman ban ganka ba”
“Ina ta kokarin boye kaina dan kar na yi arba dake har sai idan ke kadai ce, saboda ina mararin na rumgume ki na jiki a jikina kuma ba zan iya haka abun a agaban mutane ba”
Ya fada ba tare da ya sake ni daga rumgumar da yai min ba.
“Mama ta tafi”
“Na sani na gode da ta bar min ke”
Mun dauki lokaci a haka yana rumgume da ni ta baya, sannan ya sake ni ya mike tsaye ya zauna bakin gadon Momy, juyowa nai na kalleshi sai wani irin kaunarsa da tausayinsa suka dirar min a zuciya lokaci daya, ya rame sosai kamar ba shi na har idonsa sun fada kamar marar lafiya.
“Hamma baka cin abinci?”
Kallona kawai yake ba tare da yace komai ba.
“Bari na saka Husna ko wata ta hada maka wani abu ko kuma idan akwai fura ka sha idan baka son abu mai nauyi”
Ina mikewa tsaye sai ya riko hannuna ya dawo da ni kusa da shi ya zaunar ya ja ni zuwa kirjinsa ya rungume ya lumshe ido, ina jin yadda zuciyarsa take bugawa da sauri.
“Na gode Allah da be dauke min Rahma ba sai da ya ba ni ke, kuma yai min tukuici da wani dan ko ya, ni kada na san halin da na ke ciki kuma ni kadai na san iya abunda na ke ji a zuciyata”
Ya fada yana kara matseni a kirjinsa, rashi akwai ciwo sosai na san irin yadda Hamma yake ji a yanzu saboda ni ma na taba rasawa ba ma sau daya ba. Sai da ya ji kamar muryar wata a kusa da kofar dakin sannan yai saurin sakina ni kuma na mike tsaye cikin tsoron kar wacce ke maganar ta shigo ta gan mu a tare. Wata kanwar Momy ce ta shigo dakin da sallama ni na amsa mata sai ta miko min kofin fura.
“Ga shi inji Yaya ta ce ki sha”
“Na gode”
Na fada bayan na saka hannu biyu na karba, sannan ta juya ta fice. Zaunawa nai kusa da Hamma na mika masa furar wacce aka damata da kirdirmon nono.
“Ka sha”
Ba min musu ba, ya karba ya sha sai dai ba da yawa ba, ya mikon min sauran.
“Shanye”
Na sha rabin kofin sai na aje ina ta kallonsa, gaba daya ya koma kamar ba shi ba, so silent fuskarsa ma abun tausayi kallo daya zaka masa kasan cewar mutuwar Rahma ta taba shi ba kadan ba, ni ma da ban saba da ita ba ta taba na shiga damuwa kuma nai kuka balle kuma shi da yake mijinta kuma su kai rayuwa da ita.
“Ina auna yadda kika rasa babanki da dan'uwanki ne, kuma ki kaita dawainiya da mahaifiyarki, gaskiya Ayusher kin yi kokari kuma ke jajirtacciya ce, wani lokacin ana jarraba bawa saboda a gwada imaninsa da kuma irin hakurin da zai yi, ban yi tsammanin tunanin Rahma zai addabe ni kamar haka ba bayan rayuwarta, amman idan na tuna ki da abunda yake cikinki sai na jidadi kuma nai ma Allah godiya”
Ya fada a hankali yana ta kallona da murmushi a fuskarsa sai dai ba murmushin farinciki ciki ko na jindadi ba irin murmushin nan na godiya ga Allah da kuma jin zafin wani abun a lokaci daya. Shigowar Momy ce tasa na dan ja baya shi kuma ya mike tsaye yana saka hannayensa aljihu ya fice, ni da Momy da kallo muka bi shi har ya fice sannan Momy ta karaso cikin dakin ta dauki kofin furar da ta aiko min tana dubawa.
“Ba ki shanye ba?”
“Eh na sha rabi”
“Ki daina barin kanki da yunwa, na san ba za ki iya cin abu mai nauyi ba wata kila shiyasa na tanadar miki da furar”
“To Momy”
“Zauna”
Ta nuna min kujerar da ke facing din gandon, bayan na zauna sannan ita kuma ta zauna bakin gadon.
“Ataa ki matar aure ce a yanzu ina fatar kin san da haka?”
Na gyada masa kai ina maida idona kasa.
“Ke yarinya ce na sani, amman daga lokacin da kikai aure zancen yarinta ya kare sai dai a kira ki yarinya saboda shekaru ko kuma wani abun da za ki na shirme ko rashin tunani, ballantana yanzu da kike dauke da juna biyu”
Na kasa yin kasa da kaina saboda kunya.