Sashe 130
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Ina gama sallah asuba na kunna butar ruwan zafi na hada masa tea, ko da ya shigo ina saka masa sugar. Be sha ba sai da ya bani na fara sha sannan ya sha, sai ya tashi ya shiga wanka ya fito ya shirya nima na shiga nai wanka na shirya. Har airport na raka shi ina jin kamar kar ya tafi saboda na saba al'amurarransa kuma ina ganin kamar tafiyar tasa bata zame masa dole ba, wata kila saboda ya baro ni ya dawo ne tace wani bata da lafiya. A lokacin da zai fita motar sai da nai masa kuka domin har ga Allah ban jindadin tafiyar da zai yi ina jin kamar na bishi amman ba hali.
“Ki samu layin kasar nan ki saka a wayarki ki kirani kinji? Ba zan dade ba zan dawo matukar jikin nata da sauki zan dawo na ga sauran yan'uwanki”
Ya fada min murya kasa kasa, ni kuwa ina lafe a kirjinsa ina hawaye.
“I love u ki kula min da kanki pls”
Ya fada bayan ya bude motar ya fita sai na gyada masa kai ina hawaye.
“I love you”
Na fada masa kamar ba ni ba, dawowa yai cikin motar ya saka bakinsa cikin nawa na tsotse yawuna sannan ya cire ya sunbanci goshi sai kuma yai kasa ta hannunsa ya shafa cikina.
“I Love you More”
Haka muka rabu ina jin kamar idan ya tafi ba dawowa zai yi ba.
ALIYU POV.
Da zahar jirginsu ya sauka Lagos, hutun awa daya yai wanda hakan ya ba shi damat kiran Momy da Mama Fulani ya fada musu cewar ya dawo yana Lagos kuma zai kama hanyar sokoto saboda Rahma bata da lafiya, Momy ba tai mamakin jin cewar bata da lafiya ba daman ta san za a rina wai an sace zanen mahaukaciya, ta san inda ta ji Ataa na ta ciki kuma ga rufin asirin da suke takama da shi na kakanta ne dole ta kwanta ciwo.
Daga Lagos ya hau jirgi zuwa sokoto, daman tun yana nijar yayi waya da Nasir ya sanar masa a samar masa ticket a cikin jirgin da zai je sokoto yau, ta online Nasir ya masa komai.
Da magariba ya sauka sokoto, sai da ya kira Husna ta kawo masa mota sannan ya nufi masallacin gurin yai sallah, after ya gama sallama ya sai da ya dan jira sannan Husna ta iso, daga airport din ya wuce asibitin Uduth, kamin ya isa ya kira wayar Rahma wata daga cikin yan'uwanta suka dauka suka fada masa dakin da take.
Ya shiga asibitin a lokacin da ba a shiga sai dai sanayyarsa da wasu likitocin ciki har da Doc Bukar ya saka an barshi ya wuce tare da Husna. Daga Rahma sai kanwarta Zulfa da mahaifiyarta ne a dakin. Hankali a tashe Aliyu ya shigo domin tun jiya jikinsa na bashi ba lafiya ba. Idonta a rufe suke amman tana jin muryar mijinta ta bude ido tana kallonsa, Mahaifiyarta na amsa gaisuwar Aliyu ta fice daga dakin. Sai ya rage daga kanwarta Zulfa sai Aliyu sai Husna.
Cikin sanyin jiki Aliyu ya karasa inda take ya zauna a saman kujerar yana kallonta, gaba daya bakin idonta ya bace bat, sai farin kawai shi ma kuma kamar ba daidai take kallo da shi ba, fuskarka da fatar jikinta sun bushe sosai kamar wacce ta dade bata da lafiya.
“Mi ke damunta?”
“Ciwon kodar ne, sun ce idan ba a canja mata ba a yan kwanakin aka mata dashen wata zata iya mutuwa, amman Mommy tace zata bada tata daya, gobe da maraice ma za a fita da ita zuwa inda za ayi aikin a London”
Juyowa yai ya kalli Zulfa cikin bacin rai.
“Akan me ba za a kirani a fada min bata da lafiya tun a aka kawo ta asibitin? Da ban kira ba da ba za a kirani a fada min ba kenan? Ni fa mijinta ne ina da hakki da yawa akan ta, kuma hakkina nema mata lafiya ba na iyayenta ba”
Zulfa ta yi shiri bata ce komai ba, sai ma saurin ficewa da tai daga dakin ganin yadda ran Aliyu ya bace sosai. Husna ma ficewa tai gudun kar ita ya shafe ta dan tasan halin yayanta be iya bacin rai ba.
Hannunsa ya kai ya kama hannunta, kamar jira take sai ta jimke hannunsa da karfi tana ta kallonta hawaye na sauko mata. So take ta masa magana so take ta nemi yafiyarsa kuma ta fada masa wasu abubuwan amman bata da wannan damar domin an iyakance mata maganar tun daga lokacin da tai wacan faduwar, ashe furta magana ma ba yin bawa ba ne na mahallincinsa ne sarrafa halshe ka iya fadar abunda kake so ma ba ikon mai shi ba ne iko ne mahallincin halshen da mallakin jiki gaba daya. Hannunsa ta ja ta rumgume a kirjinta Aliyu yai saurin ciro wayarsa ya kira Muhseen.
“Muhseen dan Allah ka taimaka min ka zo yau if possible ka duba Rahma kamin a wuce da ita tana jin jiki sosai”
Shiru Muhseen yai na wani lokaci kamin ya ce.
“Gaskiya ba yau ba, sai dai gobe idan an samu jirgi”
“Da safen pls”
Aliyu ya fada idonsa cike da kwalla. Sannan ya kashe wayar, so yake Muhseen ya zo ya duba kamin aje da ita waje, domin ya san Muhseen ya kware a wannan bangaren. Taso yai daga saman kujerar ya dagota ya rumgumeta a kirjinsa sai ta lumshe ido ta sauke wani irin ajiyar zuciya.
“I love you so much”
Ya fada mata hawaye na sauko daga idonta suna sauka saman kanta.
“Za ki warke Rahma In-Sha-Allah, zaki ji sauki ki tashi mu koma gida mu yi rayuwa tare da Ataa In-Sha-Allah”
Shine abunda ya fada mata a hankali yana kara hugging dinta tightly. A asibitin yai isha'i sannan ya dawo dakin ya zauna, shi ya taimaka mata ita ma tai sallah, misalin nine Momy ta zo tare da abincin da Siyama ta duba jikinta ta mata fatan sauki sannan suia tafi. Aliyu kan a asibitin ya kwana rike da hannun matarsa, sallah asuba ce kaiwa ta fitar da shi daga dakin ita yana gamawa ya dawo.
A nan ma shi ya taimaka mata tai sallah, sai dai yadda jikinta yai sanyi ya bashi tsoro sosai. Da kanshi ya hada mata tea da ruwan zafin daya gani a filas da ya kai mata tea a baki sai ta ki sha ta kawar da kanta.
“Ba kya so ne?”
Bata ce masa komai ba tana ta kallonta duk inda yai, hakan yasa ya dawo ya zauna ya rike hannunta, sai kuma ya koma saman gadon ya zauna ya dora kanta saman jikinsa ya rike hannunta yatsunsa cikin nata sai ta jinke yatsun nasa ta rumtse ido. Da dayan hannunsa ya karba wayar da Nasir ke masa sannan ya amsa ta Momy da Mama Fulani da kuma Daddy kamin ya kira Muhseen, jin number sa ba ta shiga yasa yai tunanin wata kila yana cikin jirgi ne ko kuma ya kashe wayar ne. Number Mama Fulani ya kira ya tambaye ta idab Muhseen yana nan sai ta fada masa cewar tun da dare Muhseen ya fada mata zai je sokoto kuma ta ji lokacin da ya fita tun da safe. Kashe wayar Aliyu yai ya jinginar da kansa ya lumshe ido. Sai ga wata likita ta shigo hakan yasa ya sauka daga kan gadon amman Rahma ta ki sakin hannunsa har likitar ta saka mata oxygen ta saita numfashinsa da na'ura mao kwakwalwa, sannan ta fita, sai ya Aliyu ya dawo saman kujera ya zauna yana rike da hannun na Rahama, ya dauki lokaci a haka kamin ya maida hannunta gurin fuskarsa ya Lumashe ido, ya dauki awa daya a haka kamin ya ji hannun Rahma da ke jinke da na shi ya sake ya zamana shine kadai yake rike da hannunta. Da sauri ya dago ya kalleta sai jin karar tsayarwar numfashinta ya ji a computer da ke nuna tafiyar numfashinta. Girgiza ta ya fara yi da sauri a rike kuma a rude bakinsa har rawa yake.
“Rahma Dear... ”
Ya fada a lokaci daya, sai kuma ya sake ta da sauri ya nufi kofa kamin ya karasa Muhseen ya turo kofar dakin ya shigo. Da sauri Aliyu ya rike hannunsa sai kuma ya kasa ce masa komai sai wani numfashi yake sama saman kamar zai fice daga jikinsa gaba daya, kansa ya dora a kafadar Muhseen har sai da ya samu relief na few seconds sannan ya dago ya nuna masa Rahma.