Sashe 62
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
“Kin ga ko Rahma ki daina damun kanki da lamarin namiji, namijin ma wanda zai iya mantawa da ke a take, domin yana jin zai iya zuwa ya dauko wata macen ke ya barki a nan”
Cewar Muneera tana wani yatsina fuska. Ikram ta girgiza mata kai.
“Wallahi karki dauki zugar Muneera Rahma, Aliyu yana son ki kuma yana kaunar domin ba ko wane namiji ne zai yarda ya auri mace mai ciwo irinki ba har ya nema miki lafiya, yanzu shekara takwas kuna kokarin shiga ta tara amman be taba nuna gazawarsa akai ba, sai ma nuna miki kauna da yake, Wallahi da wata ce ke kamata ma yai ki ce masa ya auro wata ku zauna tare domin shi babban tukuncin mace a gurin mijinta”
Muneera ta taba hannu tana dariya.
“Lallai Ikram ba ki da hankali, ke baki ganin yadda ya fara gajiya da ita? Wallahi da yana kaunar ba babu abunda zai saka ya ce ba za a cire kodar mai son siyarwa a dasa mata ba, kuma duk inda kodar ta kai sai nemota ya saka mata”
“Wacce ta kone yanzu waya saka mata ita ba shi ba, wai ya kike haka ne Muneera zawarcin nan fa ba dadi ne da shi ba, kin kuma sani dan gashi nan kina yi, akan me za ki rika zugata ta kashe auren ta bar mai son tsakani da Allah ta dawo tana nadama”
“Wallahi babu nadamar da zata yi, ko sakinta yai alheri ne dan zata iya auren wani ta haihu ta barshi shi da baya haihuwar yana rabon ido, ke ce dai baki san duniya ba tunda ba ki taba auren ba shiyasa kike wannan maganar, anyi karatu amman kamar wacce ba tai ba, ni wallahi na riga na san right dina namiji be isa ya juyani yadda yake so ba”
Muneera ce ke wannan maganar tana harar Ikram. Duk abunda suke Rahma bata ce koma, sai dai ta kasa daina hawayen da take saboda kishin da yake damunta.
“A tsakankanin kwanakin nan ina jin kamar na rabu da Aliyu, ko dan na samu haihu kuma na matsar da jikina daga nasa, dan ba zan yarda ya hana jiki da wata yar talakawa kuma ya hada da ni ba, amman sai na ji kamar ba zan iya ba, Saboda ina son Aliyu sosai ya saba min da wasu dabi'unsa da ko bachi bana jindadin yinsa ida yadda baya kusa da ni”
Tana rufe bakinta sako na shigowa yarta da number Aliyu Sweet bae kamar yadda tai saving number sa da dan emoji din heart a karshe. Sai da ta share hawayenta sannan ta bude sakon ta soma karantawa.
_Fito gani gurin gate muje gida_
_Na fi son zama a nan_
Ta mayar masa da amsa a take ya sake aiko mata da wani sakon.
_Na sani, a sokoto za mu zauna amman a gidanmu_
_Ka bar ni a nan kawai_
_Ba ke son kulawata ne Rahma? Ba kya son zama kusa da ni ne?_
_Ina so Aliyu ina so_
Ta mayar masa da amsa tana hawaye sai ya sake turo mata wani sakon.
_Then fito muje gidanmu I'm waiting for you_
“Wai yana bakin gate”
Ta fada tana kallon kanen nata Muneera tai karaf ta ce.
“Mi ya zo yi?”
“Wai na fito mu koma gida”
“Tashi kije, ki fadawa Daddy kawai da Momy sai ki bishi ku koma can idan ma kina son zaman a nan da safe sai ya rika kawo ki”
“Ta je fa kika ce tab hmmm”
Ikram ta kalli Muneera da tai maganar ta ce.
“Karki zuga ta akan abunda kika san gaskiyarsa, namijin da baya fushi idan yai be iya ba, duk yadda yake son ta idan tana masa irin haka zata nisanta sonta ne kawai a zuciyarsa”
Saukar da kafafunta Rahma tai daga saman gadon tunawa da Aliyu baya son jira duk kuwa da tasan ita yana daga mata kafa, sai dai idan yai fushi da ita itace zata shiga damuwa.
“Bari na fadawa Daddy da Mommyn sai na tafe”
“Wai da gaske tafiya za ki yi? Allah mai iko, ni kan kada Allah ya dora min son namiji haka”
Kallonta kawai Rahma tai ta ce
“Ba za ki gane ba ne, Ikram hada min magani na a jaka”
Ta dauki mayafinta ta dora a kafata ta fice daga dakin.
ALIYU POV.
Yana zaune cikin motar yana ta kallon wayarsa ko zata sake turo masa sako amman shiru, bata turo masa ba kuma baya son shiga ciki saboda iyayenta domin ya lura yanzu kamar basa son auren su. Sai dai yana daga musu kafa kuma yana dagawa Rahma kafa a duk abunda take saboda ya dauketa abokiyar rayuwa, a ganinsa idan mace bata jidadin a gidan aurenta ba to a ina zata je ta jidadin? And ya san mata karamar kwakwalwa ne da su shi tunaninsa da nata ba daya ba, shiyasa baya biye mata, idan kuma aka zo maganar mata yana raga mata sosai kuma yana daukarta da muhimmanci yana mata uzuri saboda ya san darajar ace wannan matarka ce, duk wani rashin kulawarsa da wulakanta mutane a waje ne ban da matarsa.
Yana hakimce cikin motar Rahma ta bude gate ta fito tana takawa a hankali ta doso inda motarsa take, fita yai daga motar ya bude mata front seat tun kan ta karaso. Hugging dinta ya fara yi kamin ya sumbaci goshinta.
“Ya jikinki?”
“Da sauki”
Ya karbi jakarta hannunta ya saka a motar sannan ta shiga ya rufe kofar ya zagaya ya koma mazaunin direba ya hau titi.
MUHSEEN POV.
He wake up early saboda jirgin da zai bi na safe ne wanda zai tashi da misalin tara na safe. Gashi kuma akwai aikin da yake son yi a nan kamin ya wuce sokoto. Daga dawoalwarsa Dag masallacin da yai sallah asuba ya nufo part din Mama Fulani dan hadawa kansa ruwan Lipton, yana ta kallon Garejin da Ataa take yana murmushi ya san da tana nan da yanzu ta fito ta shiga aiki, bata wani dade sosai a gidan ba amman na saba da ita kamar wacce suka taso tare, zuwan nan ma saboda ganinta ne yasa yake son yaje saboda yayi missing dinta sosai.
Be yi zaton zai samu Mama Fulani a kitchen ba, domin ba halinta ba ne fito tun asuba tai aiki.
“Mama ke ce a kitchen yanzu ni na dauka ma wata yar aikin aka samu”
Ya fada da mamaki karara a fuskarsa. Ita da murmushi ta kalleshi tana sanye da kayan bachi kana ganin fuskarta kasan tana cikin farinciki sosai.
“Ina dai a sake dauko mana wata yar aikin amman tsohuwa na ke so ba yarinya ba”
Dariya Muhseen yai ya nufi butar ruwan zafi ya dauko ya zuba mata ruwa yana fadin.
“Saboda mi?”
“Ai ka fi kowa sani”
“Wai tafiya za ki yi ne hala? Naga kina farinciki kuma kin shigo kitchen tun da safe”
“Aa Wallahi Abbah ku ne ya fada min jiya da dare bayan ya dawo aiki, kasan maganar kamfanin nan da ake son siyarwa”
“Eh wani abun ne”
“Wani abokin kasuwanci Abbah da ke can Agadaz ya ji, ya fadawa Babansa sai suka kira Abbah ku suka ce masa suna son za su iya kamfanin su sabunta shi a cigaba da yin komai a karkashin mahaifinku, shima yace shekaranjiya ya samu labarin kamar wasa sai jiya da rana aka jira da number Nijar sarkin ya fada masa jikansa zai zo ya kara duba kamfanin kuma su tattauna akan maganar yau”
“Wow amman am so happy for Abbah Wallahi”
“For us dai ai wannan dukan mu ne, domin ance mutumen ba shi da keta, sarkin Agadaz ne komai yaransa da jikoki yake wakiltawa su yi shi yana can sai idan wani abun babba ya taso yake zuwa”
“Au sarki ne ma amman wannan ya tara da yawa”
“Kai ance yana da dukiya sosai, shi da iyalansa, ance duk inda zai je da jirginsa ma yake yawo”
“Amman Mama irin wannan anya ma zai ci abincin kin san sun fi son abinci waje fa irin na turawa”
“Abbah kune ya ce a shirya masa dan yafi son abincin gargajiya, ai ba sarkin ne zai zo ba jikansa ne, da misalin goma za su iso shiyasa na soma aikin tun yanzu kamin su Maryam su farka su taya ni”
“Okay ni kuma da 9 zan je sokoto”
“Gurin me?”
“Ba na fada miki Aliyu ya kira ni ba akan rashin lafiyar matar nan mahaifiyar Ataa”
“Wai a ina ya ganta?”
“Oho ai tunda kince a sokoto take kuma yana can ga Momy ma a can nemanta ba zai musu wahala ba”
“Muhseen ku fita daga safgar yarinyar nan dan girman Allah, wai kamar ku za a ce kun tsaya kuna bata lokacinku akan wata kazamar yarinya yar matsiyata irin wannan? Haba dai idan ma kyauta ne yake dibarku ai sai ka koma gida Yola ka zabo kyawawan mata suna nan da yawa yayan manyan mutane amman ya yar talaka ba, dan akasan ba zan bari ka auri yar da ubanta baya iya amsa sunansa a garinsu”
Murmushi yai.
“Mama kenan, yanzu idan wata kaddara ta faru aka ce sai na auri Ataa yaya kenan?”
“Babu ma abunda zai faru, kuma ko ya faru ba zaka aureta ba, kai ni fa na tsani yarinyar nan ko sunanta bana son ji”
“Gashi kuma naga kamar dan ki sonta yake”
“Ai Aliyu ba irinka ba ne Wallahi, Aliyu ya fi karfin yar talaka yar talakan ma wacce tai aiki a gidansu, kawai dai yana kokarin ganin sun rabu lafiya ne kar su bata masa suna kasan talaka da sheri ga hassada”
Wannan karon dariya Muhseen yai domin shi a tashi fahimtar Aliyu ya fara son Ataa tun da har zai iya daga waya ya kira shi dan ayi ma mahaifiyarta aiki, mutumen da you can die in front of him ya wuce ya bar ma. Mama Fulani ta aje wukar hannunta ta fito daga kitchen ta nufi dakinsu Maryam. Wutar dakin ta fara kunnawa sannan ta shiga tashinta.
“Maryam ku tashi mana ku rika min aiki mu yi mu gama ku yi wanka ko shirya”
“Fita za mu yi?”
Maryam ta tambaya tana murza idonta.