← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 65 OF 143

Sashe 65

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ta fada yadda take pronouncing o din is like tana koyawa mutane karatu ne. Shi ya rika kwandon yai gaba ita kuma ta riko kulolin karama da babba ta bi bayansa zuciyarta na raya mata cewar ya kyasa da ita. Kai tsaye suka wuce ciki tana biye da shi har suka shiga dakin da mahaifiyar Ataa take. Inda taga ya aje kwandon ta karaso ta aje kulolin tana kallon Ataa wacce ke zaune saman gadon hawaye shar a fuskarta a zatonta ita ce bata da lafiyar.

“Sannu ya cikin”

Ta fada tana wani lankwasa harshe kamar wata bakanuwa. Hannu Aliyu ya saka aljihu ya ciro wallet dinsa ya zaro dubu uku har zai dora a saman gadon asibitin ya ce ta dauka sai kuma ganin Ataa yasa ya mika mata da hannunsa.

“Aa ka barsu kawai”

“Karba mana bana maida kudi”

Hannu ya kai ta karba.

“Thank you”

Ta furta tana juyawa ta koma tana ta sauraren ta ji Aliyu ya kirata ko ya biyo bayanta amman bata ji ba har ta fice. Ko be tambaya ba yasan an shiga tiyata ne da Mahaifiyar Ataa tunda Momy ta fada masa Muhseen ya zo kuma gashi be tarar da ita cikin dakin ba.
Kallon Ataa dake zaune kan hospital bed din Aliyu yai with serious face ya ce.

“Mi akai miki kike kuka?”

Bata ce masa komai ba bayan turon karamin bakinta da tai ta saka hannayenta ta share hawayen fuskarta. Wata kila tsoron tiyatar da aka shiga da mahaifiyarta take ko kuma wani abun akai mata, or maybe Muhseen ya fada mata wata maganar ne marar dadi.“Ga abinci”

Dauke kai tai.

“Bana ci”

A tunaninsa ko tana tsoron kar ya saka mata wani abun ne ko kuma ya cutar da ita shiyasa ba zata ce. Kujerar da ke gefen gadon ya janyo ya zauna ya dauki plate din ya zuba jalop din da sannan ya bude dayar kular ya zuba farfesun kazar da ke cikin ya saka spoon ya soma ci, abinci yake ci amman idonsa akan Ataa ne har ya ci rabi ya mika mata sauran.

“Karbi ki ci”

“Na ce bana ci”

“Idan na ce ayi abu yi ake ba a musa min karbi ki ci na ce”

Kallonsa tai hawaye na mata zuba.

“Ai babu wanda ya isa ya cilasata kai yi Aliyu, sai dai ka cilasta wasu, babu wanda ya isa ya taba wani naka balle ya taba ka, yadda kaga dama haka kake haka kake juya kowa, ka taka kowa ka cilasta ka zalinci wanda ka ga dama saboda kana da kudi ni kuma kana gani na talaka”

“Ba ni na cirewa mahaifiyarki koda ba, lokacin da aka cire mata koda ina a gurin ne kin gan ni ne?”

Ya fada yana kokarin danna fushinsa. Sai ta girgiza kai

“Baka nan, amman kudinka suna nan, ikonka yana nan, isarka tana nan waya sani ko asibitin taka ce? Kai ma baka son talaka miyasa ka sakawa matarka kodar talaka? Karyar soyayya kake mata tunda baka iya daukar kodarka ka saka mata ba, ba tana da iyaye ba miyasa basu bata kodar su ba? Sai ta Nana matar da ita kadai ta rage min a duniya? Kokarin kare kanka kawai kake yi ai Muhseen ya fada taya za a sakawa matarka kodar da baka san mai ita ba? Duk wannan taimakon kana min ne saboda ka san ka zalince ni ka cutar da ni ni da mahaifiyata Aliyu kai azzalumi ne....”

Cikin wani irin fushi marar misatuwa ya jefar da plate din hannunsa ya mike tsaye yana huci kamar zai dake ta, sai kuma yai saurin kawarda fuskarsa daga barin kallon yana kokarin saita numfashinsa. Mikewa tai tsaye wanda hakan yai daidai da shigowar Doc Bukar dakin, tana kallonsa fuskarta da hawaye ta ce.

“Na fada Aliyu ka kashe ni daman mutuwa ta fi rayuwa a yanzu, ka riga ka gama da ni tun da kasa aka cire mahaifiya koda dan zalinci ka sadawa ita ta rayu mu sai mu mutu, ga mahaifiyata can ana mata aiki Muhseen ya fada min zata iya mantawa da komai ciki har da ni har da ni Aliyu, idan kuma bata rayuwa ni ce a cikin matsala saboda zalincin da kuka mana kai da wannan likitan, har abada ba zan yafe muku ba kuma Allah ba zai bar ku ba....”

Ta fada kanta a sama tana kallonsa hawaye ke mata zuba sosai har wani dauke numfashi take kamar zata shude... Jawur idon Aliyu sukai yana kallon Ataa take rabe masa uku ba ko biyu babu ko kyafta ido. Doc Bukar ne ya matsa kusa da su yana Kallon Aliyu sai kuma ya kalli Ataa.

“Zauna”

Ya fada sannan ya kalli Aliyu.

“Da za ka fita na wani lokaci”

Sai a lokacin Aliyu ya kalli Doc Bukar ya sake kallon Ataa sai kuma ya nufi kofa ya fice cikin wani irin bacin rai marar misaltuwa.Ba zai iya fadar lokaci da ya kawo gurin motarsa ba wata kila ma taku biyu yai ko uku ko kuma dari ko dubu shi dai kawai ya samu kansa tsaye jikin motarsa ba tare da ya san ya iso ba saboda tsananin bacin rai da zafin kalaman Ataa, wani irin gudu jinin zuciyarsa ke yana da tabbacin da za a bude kirjinsa a yanzu wata kila da hayaki za a gani yana tashi. Ita kadai ta kai haka duk duniyar nan ta fada masa magana irin wannan mai zafi da daci kuma ya kyaleta ita kadai ce mutum ta farko da ta taba taba martabarsa da duk wani abun daya takama da shi tana a talakarta ta fada masa magana son ranta. Bude motarsa yai ya shiga ciki ya zauna for like 40 minutes sannan yai mata keys ya fita daga harabar gurin. Driving kawai yake ba dan yasan inda zai je ba, gida gurin Rahma ko kuwa gurin Momy? Ko gurin wasu abokansa ko yan'uwa? Kalamanta na ta maimaita kansu a kwakwalwarsa tun yana jin zai iya jurewa har ya kai ga runtse ido yana damke sitiyarin motar, sam ya manta cewar tuki yake kuma babban titi yake na gawon nama, har sai da yaji ya bugi wata motar wata motar kuma ta bugu bayan tasa, da sauri ya bude ido yana kiran mafi kyawun sunan a cikin sunayen Ubangiji wato Ya Rahamanin Rahim. Saurin tsayarda motar yai motar da ke gabansa tai gaba shi kuma ya faka tashi gefe ya fito ya nufi mai motar.

“Malam lafiya kake kuwa?”

Mutumen ya tambaya.

“I'm sorry ina cikin matsala ne”

Aliyu ya fada sannan ya bude wallet dinsa ya ciro sababbin kudi da zasu kai 50k ya mikawa mutumen.

“Ga wannan”

Mutumen ya kalli kudin kamar ya karba sai kuma ya dan tsaya jan aji.

“Ai ba kudi ba... ”

“Idan zaka karba ka karba kawai ba zan tsaya magana da kai ba na fada maka ina da matsala”

Hannun mutumen ya kai ya karbi kudin yana dan nuna kamar be so ba. Aliyu ya juyo ya bude motarsa ya shiga mutane sai kallonsa suke yai mata key ya sake hawa titin yana ta tasbihi saboda samun fin karfin fushinsa. Wani guri ya samu can kusa da ga ďan k'ane hotel ya faka motarsa ya fito yana shakar iskar gurin. Har yanzu ya kasa daina jin kalaman Ataa a kunensa sai dai wannan karon a maimaikon ransa ya bace kamar dazun sai tausayinta ya soma rabar zuciyarsa fiye da da, yarinyar da ke tsoronsa da masu kudi tun da har ta iya bude baki ta fada masa magana irin wannan tabbas tana cikin damuwa da bakinciki, ya sani ko Ataa zata fahimcin ba nan kusa ba kuma ba a yanzu ba. Yanzu ma laifin ba nata bane na Muhseen ne, for what zai fada mata cewar mahaifiyarta zata manta da ita? For what zai mata karyar cewar da hadin kan Aliyu aka cire mata koda? Komawa yai cikin motar a fusace ya dauki hanyar gidansu Momy.

**ZAKI

By Khadeeja Candy

32...

Abinci kusan kala hudu Mama Fulani ta shirya ma bakon da zaizo, ko da tara tai gaba dayansu sun shirya Maryam da Rukaiya sukai wanka Baby ce kawai ta wuce scul. Amman shiru bako be iso har goma da rabi. Sai misalin sha daya Abbah ya kira yace mata bakon ya sauko Nigeria gashi nan ma zai taro shi a airport.

A sannan ne Mama Fulani ta saka su maryam suka kwashi kulolin abincin suka jera part din Abbah, ita kuma ta kunn turaren wuta irin mai kamshin nan sosai na larabawa ta kara kunna dayan ac sannan ya dawo part dinta, a daki ta samu su Maryam da Rukaiya sai kara gyara fuskarsu suke suna fesa turare. Wani dadi ne ya lullube ta ganin duka yayan nata sun fito fes gwanin sha'awa. Suna jin tsayawar mota sukai hanzari yafa gyalensu suka jiyo bayan Mama Fulani dake cikin wata shadda yar mali ta sha paint work gwanin sha'awa.
  Mota biyu ce ta Abbah da kuma wata mai tsada da suka shigo, ta kamfaninsu da ke nan Abuja. Suna fitowa daga motar Mama Fulani na fitowa ita da su Maryam suna musu marhabun bakin Mama Fulani har kunne, a maimakon mutum daya sai suka ga samari biyu dayan sanye da kananan kaya dayan kuma sanye da farar shadda ya nada bakin rawani a kansa kamar wani balarabe.

“Lale marhabun Lale lale marhabun da manyan baki”

Mama Fulani ta fada tana kokarin sauka daga balcony din ta nufi inda suke, sai duk suka saki murmushi suna kallonta.

“Sannu da zuwa”

Maryam ta fada kamin Rukaiyah ta dora da nata. Dayan ne ya amsa yayinda yadan kuma yake ta kallonsu yana murmushi kamar baya jin abunda suke fada. Abbah ne yai gaba zuwa part dinsa yana musu iso sai suka bishi a baya, bayan sun shiga ciki sun huta ne Abbah ya shigo part din Mama Fulani ya kira dan taje su gaisa da su, sannan ya shiga bangaren Ammy ya same ta falonta zaune ita da yaranta suna kallon wani film da ake hassaka a mbc Bollywood.Ganin Abbah yasa Batula da Zainab tashi zaune suna murna domin ba su san da shigowarsa ba sai ganinsa a falon.

“Sannu da zuwa”
Chapter 65 · 0% Book details