← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 122 OF 143

Sashe 122

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Mama pls for me? Ai za ki iya min komai ko?”

Ta gyada kai cikin damuwa.

“To pls ki yi magana da ita as my mother kuma saboda grandchild dinki ba wai as abunda kika aikata cikin rashin sani ba”

Yawun bakinta ta hadeye ta tashi ta nufi bandaki cikin yanayin damuwa.

*Manage pls*
“Ina ganin zai fi kyau idan ka hakuri ka bi matarka Aliyu, ko kuma ka kira Momy ko Ammy ka rikesu su yi ma mahaifiyarta magana idan zata yarda ta barta na wani lokacin idan cikin yayi kwari”

Tana zaune bakin gado take fadin wannan maganar bayan ta fito daga wanka, Aliyu ya dago kansa daga kan wayarsa ya kalleta.

“Ko na bita hankali ba zai kanwata ba Wallahi, kuma kin san ba ni wanda zau shige min gaba yai min ruwa da tsaki a wannan lamarin sai ke”

“Ba zan iya ba Aliyu, Wallahi ina tsananin jin kunyar kaina balle kuma na hada ido da Ataa ko mahaifiyarta, da ace komai be faru ba da yanzu ba haka ba”

“Amman Mama”

“Aliyu ba zan iya ba, dan Allah ka je ka samu Ammy ko Abbahku kai masa wannan maganar”

Ta amsa masa kai tsaye da dukannin gasjiyarta, taya ma zata iya zuwa ta ce zata roki abar Ataa saboda cikinta? Yarinyar da ta gama wulakantawa ta aybanta. Ai wannan ya zama rashin kunya ma. Aliyu be sake cewa komai ba, ya mike tsaye ya fice, har ga Allah baya son tafiyar Ataa a garin nan yanzu ya san duk yadda zai bata kulawa a nan dole a can sai ya daga mata kafa wani abun ma ba a gaban idonsa za tai ba, gashi tafiya ce ba nan kusa ba, waya sani ma ko ace sai taga kowa da kowa tukuna za su dawo? Ba wai baya son haduwarta da danginta ba ne, shi yadda za a jigilgila cikin ne baya so. Yana son cilasta Mama Fulani tai ma Nana magana ne saboda bakinta da na Nana ya hadu a wani gurin na nunawa Ataa kulawa, ko da ba zata yarda ba akalla yasan Nana zata san cewa Mama Fulani ta damu a yanzu, and hakan da za tai a yanzu matakine na murje ido ta nuna komai ba komai ba ne yadda za a zama abu daya, amman ya saka samun hakan daga gareta, ya sani abunda Mama Fulani ta aikata ba daidai ba ne, shi kanshi baya ganin laifinta ko ganin kuskurenta har sai yanzu da yake kokarin gyara na shi kuskuren. Cikin mota ya koma ya zauna ya kira wayar Nasir tana yin ringing  yai picking kamar mai jiran kiran.

“Babban Baby gani a hanyar gidanka fa da Madam”

“Gurin me?”

“Zata zo ta ga Ataa ne kasan ba su taba haduwa ba, and tana son taya ta murna samun ciki”

Yar dariya Aliyu yai shi kanshi Nasir sai da yai dariya sannan aliyu ya dora da.

“Bana gida ni da ita muna nan gurin Mama, Nasir ina son magana da kai”

“Ayyah bari na sauke ta gidansu yayarta zai na same ka a can”

“Alright”

Aliyu ya kashe wayar yana ta kallon garden gidan da ke facing din inda motarsa take fake. Fita yai daga motar ya nufi bangaren Ammy sai kuma ya samu kansa ya kasa shiga ciki sosai yake jin kunyar Nana shi kanshi har Mamakin abun yake, domin ko iyayen Rahma yana sakewa da su da su ne kai tsaye zai iya nuna musu baya son matarsa tai nisa da shi balle kuma ace tana da ciki abunda yake kauna.
Har ya ciro wayarsa ya kira Ataa sai ya tuna da be saka mata line a ciki ba, a take ya aikama Nasir text, sannan ya juyo zai dawo part din Mama Fulani kuma sai ya hango Muhseen ya shiga can sai kawai ya nufi gate yana ta sake sake a ransa, he can't face Nana kai tsaye ya fada mata haka and idan Mama Fulani ba zata iya zuwa tai magana da Nana ba ba zai iya rokon Ammy ba, domin a ganinsa idan har Nana da Mama Fulani ba su samu fahimtar juna ba shi kan shi yana cikin matsala. Bakin gate din ya fito ya tsaya yana danna wayarsa, number Rahma ya kira tai ringing har ta katse ba a daga ba, ya sake kira ba a daga ba ya san wannan baya rasa nasaba da fushin da take da shi, sai kawai ya aika mata da sako. Jin motsin mutum da yai bayansa, zuciyarsa ta raya masa Ataa dan yasan ita kadai zata masa haka duk duniya sai kawai ya saka hannunsa ya rikota ta baya ya juyo da ita, sai ta saka dariya.

“Mi ya kawo ki nan?”

“Naga lokacin da ka zo gurin Ammy ai sai kuma ka  koma”

Kallonta yai sai kuma ya kalli gate din gidansu Kamal a take zuciyarsa ta raya masa cewar Kamal zai iya fitowa ya ganta, and abunda ya fi tsana a yanzu wani wanda ya tana son Ataa ya ganta ko, a duk lokacin daya tuna cewar Ataa ta furta masa cewar tana son Kamal sai ya ji ba dadi.

“Koma ciki nima Nasir na ke jira”

“To mu jira shi tare miyasa ka fasa shigowa ciki?”

“Kunyar Mama na ke ji, ke ma ki je ciki Mama Fulani na son magana da ke”

“Ni?”

“Yes shiga gida mana”

Ya fada mata calmly yana kallon cikin kwayar idonta, wani irin kaunarta yake ji cikin ransa.

“I Love you”

Ya fada mata a hankali, sannan kama hannunta ya rika sai kuma ya saki ya tura hanninsa ya bude mota kofar gate din, har ta juya ta shiga Muhseen ya fado masa a rai sai yai saurin bin bayanta.

“Babyna karki je yanzu zo ku yi magana da ke a mota”

Gaba yai zuwa gurin motar ta biyo, jinginawa tai jikin motar shi kuma ya tsaya daga gabanta yana kallonta from head to toe wani dadi yake ji wai cikinta ne a jikinsa.

“Babyna gobe Mama za ta tafi ko?”

“Eh amman da ni zata tafi ai”

“Ni kuma ki yi yaya da ni?”

“Sai na je da kai”

“Ba a zuwa da babba yawo”

“Sai ka zauna har mu dawo”

“Za ki iya tafiya ki bar nan?”

Sai tai shiru, tai kasa da kanta.

“Babyna kin ga kina da ciki? Kuma cikin nan sabo maganin ma yanzu za ki fara sha idan na siyo, kuma kin ga ciki yana son kulawa musamman sabo, bana son ki yi tafiyar nan dan Allah”

Ta lake kafada tana turo baki.

“Ni gaskiya ina son na ga yan'uwan Mamana kuma su ma za su so ganina ai”

“Ciki be so jigila ai da yawan zirga zirga idan yana yaro, ba za ki iya kula da shi yadda ya kamata ba”

“Ai sai muje tare idan ba ka yarda da ni ba”

“Daman ai ya kamata na je saboda na san iyalinki kuma su ma su san ni amman wannan cikin ne ya saka na canja tunani”

“Ni gaskiya ina son na je, kuma Nana ba zata ji dadi ba idan ban je ba”

“Ba na ce ki daina ce mata haka ba?”

“To Mama”

“Idan na ce zan biku yanzu ai ya zama rashin kunya, kuma idan muka je can ba guri daya za mu tsaya ba, kin ga dole kije nan kije nan ana nuna miki dangi, Wallahi Ataa cikin nan a jikiki kawai yake amman jinshi na ke a cikin cikina, ni da akwai yadda za ayi da an maida min shi ke kije ki yi ta abunda kike so, ba ki san yadda na ke jin cikin nan ba ne”

Ya fada cikin yanayin damuwa, domin har ga Alla shi gani yake idan tai wata wahalar zai iya rasa cikinsa. Dariya tai masa sosai kamin ta ce wani abu suka ji horn a bakin gate din gidan, mai gadin ya bude wanda hakan ya bawa Nasir shigowa cikin gidan da motarsa. Ataa ta maida dubanta gurin motarsa har ya faka motarsa kusa da Ta Aliyu ya bude ya fito, Aliyu can't take his eyes on Ataa sai da Nasir ya fito daga motar sannan ya juyo yana kallonsa.

“Madam congratulations”

Aliyu ya kalli Ataa wacce tai kasa da kanta tana jin kunya shi kuma yai murmushi yana saka hannunsa aljihu.

“Ina wuni”

Ta gaisheshi cike da kunya.

“Lafiya kalau ya jikin na ki”

“Na ji sauki”

ta juya da sauri ta nufi bangaren Mama Fulani a lokacin ne Muhseen ya fito daga part din ita kuma ta shiga.

Aliyu ya bude motarsa ya dauko takadar maganin ya mikawa Nasir.

“Zaka saka a binciko mana wannan, na so na siya asibiti kuma ban samu dama ba”

“Ka ce kana son mu tattauna”

Nasir ya fada bayan ya karbi takadar.

“Yeah zancen tafiyar nan ne Nasir bana son zuwanta, kuma na rasa yadda zan shawo kan abun, ga shi kuma Mama Fulani ta ki yarda tai magana da Mahaifiyarta, and you know Momy ba za tai ba”

“To kai miye damuwarka da zuwanta? Ba abun farinciki ka ne ba sai ka je ka ga danginta su ma kuma su ganta”

“Na sani ai, Nasir cikin anan kasan karami ne”

“Aliyu ba akanka aka fara ciki ba, wannan ba ma reason ba ne kuma ka san ba ka isa ka samu Mahaifiyarta da wannan maganar ba, dama daya ce da kai ka bita ku tafi ka ga danginta idan ma da kai ba za a barta ta dade ba, sai ku dawo abun ku sai kuma ta haihu, amman idan za ka iya convince dinta da yarda ta zauna then fine”

“Ai ba zata yarda ba ne”

“Kai ma ai kasan yadda take dauki ganin yan'uwanta kamar yadda kake daukin cikinta”

Aliyu yai murmushi domin shi kadai ya san abunda yake ji akan cikin nan nata.

“Gobe fa za ayi tafiyar”

“Shirinka ai ba shi da wahala sai ka shirya kawai ka bi su”

“Babba da ni”

“To ya ka iya kauna ce sila”

Dariya Nasir yai yayinda Aliyu kuma yai murmushinsa da ya saba.

***      ***      ***
Chapter 122 · 0% Book details