← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 143

Sashe 40

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

“Saboda kawai ta daina min kallon azzalumi ne, ko akwai wani abun bayan wannan?”

“Kai ba ka sani ba ni ya za ayi na sani? Make yourself calm Aliyu, this is the right time da zaka taimake ta maybe ta yafe maka, idan mahaifiyarta tana nan kuje ku roki yafiyarta ku nema mata magani”

Ya daga kansa sama yana ta mamakin kansa.

“She got lucky wallahi, da ba ita ta fada min haka ba yau ko? Hmmm”

Nasir yai murmushi.

“Kuma ka damu ko? Ni Wallahi kai ke ba ni tausayi ba ita ba”

Kallonsa kawai yai ya karaso gurin tebur din ya dauki keys dinsa ya fice daga office din.

*Z A K I -it's not free, pay 300 to 0314795884 Abubakar Gt bank, then send the evidence via 08036126660*
21.

Aliyu na fita Mama Fulani ta fice cikin bacin rai, sai ya rage dakin daga ni sai Ya Muhseen da ke ta rarrashina.

“Fada min dukan ki yai?”

“Be min komai ba”

Na fada ina share hawayena idanuwana sun ji ja sosai, domin ba kadan nai kukan ba.

“Be miki komai ba za ki yi kuka? Fada min gaskiya mana, dukanki yai ko?”

“Be min komai ba, kawai kaina ne yake ciwo shine”

“Za mu shirya da ke idan kin fada min abunda yai miki”

Ya fadi hakan yana nuna ni sannan ya juya a fice cikin yanayin da ke nuna yayi fushi da ni. A ganina be kamata na fadi abunda zai iya zame min matsala, nasan idan har na fada masa dalilin kukan nawa wata kila zai iya tambayar mahaifiyarsa dalilin dukana da tai wanda hakan zai iya zama fada a tsakaninsu, idan kuma na fada masa abunda ke tsakanina da Aliyu abu ne da zai iya sakawa a koreni a gidan gaba daya ma, nai biyu babu.
Tabarmar na daga na kabe saboda takawan da Aliyu yai sannan na sake shimfiďata na kwanta a kai ina saka hijabina na rufe kafafuna, sai ga Anty Maryam ta shigo garejin fuska a hade hannunta rike da wayar carja.

“Ke uban wa kike wa rashin kunya? Ya Aliyu sa'anki ne?”

Saurin tashi nai zaure a take jikina ya dauki rawa.

“Ban masa rashin kunya ba”

Ban gama rufe bakina ba ta watsar min wayar chajar a jiki iya karfinta, ban san lokacin da nai tsalle na dire ba, rabon da a saka wani abu a dake ni a jiki har na manta, amman yau saboda rashin gata na zo aiki gidan wasu yar gidan tana dukana akan abunda bata san gaskiyarsa ba. Haka ta bi ta bulale min jiki ko ina ta samu dukana take da wayar idan nai ihu ta ce na rufe mata baki. Ta fini girma da jiki sosai domin ita irin manyan yan matan nan ne masu kamar matan aure masu yaya shida, ba kamar Anty Rukaiya dake da karamin jiki ba.

“Kuma idan na ji muryarki a waje sai na ci ubanki”

Ta fada tana nuna ji da wayar da ke hannunta sannan ta fice ta barni a gurin ina ta murzar jiki ina hade kukana, duk inda ta bulalar ta same ni ya yi min ja kamar na jimu abun ka da mai farin fata, farin ma irin nawa mai ja sosai na jajayen buzaye. A gurin na kwanta ina ta hawaye, domin babu danar nai kuka sauti ya fita ta dawo ta kara min kamar yadda ta fada. Ana gaf da sallah magariba zazzabi ya rufe na rika jin sanyi na sauko min ga bulolin nata min zogi, kaina kuma yana ta ciwo har bana son daga idona.
Ban iya fita karbar abinci a gurin Mama Fulani da Ammy ba, da yake kuma ba ni da gatan da wani zai da mu ban ci abinci ba babu wanda ya zo dubani ko a aiko min da abincin. Haka na kwana a gurin cikin rashin gata da galihu har gari ya waye, ina ta jin wuyar tashi amman ba ni da gatan da wani zai fanshe ni a aiki, na san ba ma za su yarda da uzurin cewar bana jindadi ba. A dan karamin madubin hoda ta na duba yadda idona da gefen kumatu na ya kumbura bulalar ta kwanta min har saman fatar ido. Wani ruwan hawayen ne ya sake cika min ido na fashe da kuka marar sauti ina ta jin kewar Nana da rayuwata da baya, na sani ba mu cikin jindadi amman a haka muke rayuwarmu babu wanda ya taba dukana, amman a nan ga duka ga wulakanci saboda kawai ina neman halalina.
Ganin kamar zan bata lokaci ina kukan yasa dole na tsagaita kukan da ke kara min ciwon kai da damuwa na daura dankwalina na fito ina jin nauyin jikina saboda zazzabin da ke kara sauko min, na nufi part din Mama Fulani kamar yadda na saba, part din na fara gyarawa na ma komai tsaf sannan na nufi part din Ammy na gyara mata falonta, yanayi kawai ta lura da shi ta fahimci bana jindadi.

“Jiya Fulani ta aiko ta ce karna baki abincin dare da safe, wani laifin kika mata hala?”

Kaina kawai na daga na kalleta, ina bude baki nai magana sai kuka ya kubce min na saki tsintsiyar hannuna na durkushe a gurin ina ta kuka. Sai ta zauna a cushion tana ta kallona cike da tausayawa.

“Mamana ki yi hakuri, duk wanda ya ce zai nemi halal dole sai yayi hakuri, musamman aiki a gidajen wasu, dole za ki iya haduwa da abubuwa da dama, ban san dalilin na aiki a nan ba, amman dai ki yi hakuri wata rana sai labari zai zama kamar ba ayi ba kinji”

Na gyada mata kai ina share hawayena.

“Baki da lafiya ne naga kamar fuskanki ya kumbura”

“Kaina yana ciwo, kuma ina jin zazzabi”

“Me mikai wa Fulani hala?”

“Wallahi ban mata komai ba, kawai dai na fita ne bakin gate ina dawowa sai sai ta mare ni, kuma shine Anty Maryam ta dukeni da bulala”

Na karasa ina kara fashewa da kuka. Sai ta girgiza kai cike da tausayawa.

“Fulani bata da imani Wallahi, Allah ya kyauta”

Tashi tai ta nufi upstairs bata dade ba ta dawo rike da kwayoyin magani ta bani.

“Shiga kitchen ki debo ruwa ki sha”

“Na gode Allah ya saka da alheri”

Na fada ina saka hannu biyu na karba sannan na nufi kitchen kofi na dauka na debi ruwan na balle maganin sai na kasa sha, abun ka da wanda be saba ba, daman can magani da allura bana son su sai dole, daker na iya runtse ido na shanye maganin na fito ina ta bata baki, ko da na fito Anty Zee da Humaira, Inteesar da Batulu duk sun fito dakinsu, dan haka na shiga na gyara ko wane dakin da dakin Ammy sannan na fito.

“Idan kin gama ki zo ki karbi abinci, amman karki bari ta sani”

“To”

Na amsa sannan na fito daga part din na koma part din Mama Fulani dan gyara bedrooms idan yayanta sun fito. Ko da na shiga duka yayanta suna dinning har Ya Muhseen, da alama da gaske fushi yake da ni domin ko inda nake be kalla ba, ba kamar yadda ya saba kallona ya sakar min murmushi ba, har na dauko tsintsiyar da mopper na shiga dakunansu na gyara komai na fito cikin rashin dadin rai na ke na fushin da na lura da Ya Muhseen na yi da ni, domin har ga Allah na damu kuma na ji babu dadi. Sai da gama gyara bedrooms din sannan na fito na sauko kasa, a lokacin Ya Muhseen baya dinning din ba kamar yadda na saba ganinsa idan na gama gyara an barshi a gurin zaune ba, wani lokacin ma shi yake miko min abincin na safe. Inda na dauki tsintsiyar na nufa na aje sannan na juyo da zimmar komawa part din Ammy na karbi abincina domin na san wannan Mama Fulanin ba bani za tai ba, sai na ji ta kirani.

“Ke.... ”

Na dawo da sauri na durkusa a gabanta cikin ladabi na ce.

“Ga ni”

“Shiga dakin Rukaiya da Maryam da Baby ki kwaso kayan durowarsu ki je garden ki wanke, ko daya karki bari kuma ki wanke su tas”

Da to na amsa mata na taso ina tausayin kaina na nufi dakunnan na kwaso tulin wankin ko wanne zai kai kala goma sha biyar wani ma ashiri, sai da na kaisu garden din sannan na dawo na sake dukusawa a gabanta.

“Ina sabulu”

“Shiga store ki dauko”

“Abincina fa?”

“Sai kin gama wankin za ki ci ai tunda kika zabi rashin kunya sai na horaki a gidan nan”
Chapter 40 · 0% Book details