Sashe 141
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Wata biyu da kai lefen Muhseen akai soma shirye shiryen biki, tun kan 25 Sept aka soma baki a gidan Mama Fulani ciki kuwa har da su Momy da wasu daga familynta da suka zo bikin, da mutanen yola. Abbah ya gyara ko'ina na gidan an yi sabon fenta an sayo abubuwan tarbon baki da na hidimarsu.
A Abuja aka fara komai na bangaren Mama Fulani ta bangaren Amaryar Muhseen kuma daga Bachi aka fara sannan aka dawo Abuja aka cigaba da shagali. A cikin shagalin biki wani wani labari marar dadin ji ya zo mana, Waenda aka tura su je yin jere Rukaiya sun tararda da karamin gida mai ciki da falo daya da bandaki sai kitchen a tsakar gidan, ma'ana dai irin gidan nan na talakawa masu rufin asiri, yadda Mama Fulani ta sha kuka a ranar abun har tausayi ya bani ba ita ba ba Rukaiya ba ba yan'uwanta ba, Momy ma bata jidadin hakan ba sai dai babu yadda aka iya. Ai ko a lokacin ne Hamma ya hau fada cewar daman can sai da ya ce ayi bincike Mama Fulani tace bincike ba dole ba ne kuma an san iyayensa da sauransu. A lokacin ne Abbah ya kiran Mahaifin yaron yana fada masa awai an je jeren dakin an tararda abunda ba a zata ba, sai Wamban kano yake fada masa cewar ai ba shi ya haife shi ba almajirin gidansa ne tun yana matashi har ya tasa ya koma Abuja yana neman kudi, a gidan man ma shi ba manager ba ne yana cikin amsu siyar da man ne dai a tanki. A ranar Rukaiya suma ne kawai ba tai ba akan bakinciki ita da Mama Fulani. Hamma ne ya saka aka nema masa wani gidan haya mai kyau aka je can akai jeren.
Washe garin ranar da akai Walima akai Dinner, sai da kowa ya halarta sannan daga baya ni naje tare da Hamma, na sha kyau abuna ni kaina na san na yi kyau domin lace din angon blue ne mai fitar da farin mutum, ga kuma tsoraye na aka min suka sauko har bayana, kuma nai sa'a Hamma ya bar ni na fidda abuna sai dai be barni na yafa karamin gyale kamar yadda kowa ke yafawa ba nawa babba ne amman hakan be hana ni yin kyau ba, da man kyau mace ba a fitar da surar jiki ba ne daga kyau tufafi ne da ainahin halittar da Allah yai ma bawansa. An zubar da kudi sosai a gurin karin har nake ganin kamar hakan be dace ba, angwaye da Amare sun sha kyau sosai, duk inda Hamma yai yana rike da hannuna karin ma bayan yayi musu sai ya dawo gurina yana ta min karin ni ko har kunya na ke ji saboda cikin jikina, ban taba daukar cewar Hamma zai iya rawa kamar haka a gaban mutane ba, ba wani rawa yai can sosai ba amman yana takawa a hankali yana wasa da hannuna. Ina tsaye da shi wata cousin sis dinsa ta zo tai masa kari ta dauki hoto da shi, na ji zafi sosai shi kansa sai da ya lura da hakan har yai murmushi. An yi dinner lafiya washe ya kama Assabar sai aka rabu wasu suka tafi Bachi dauren auren wasu kuma suka tsaya a nan Abuja a inda akai na su Rukaiya da Humaira da Zainab da Batula.
A daren ranar da aka daura auren aka tafi da su Zainab da Batula zuwa Agadez tafiyar da akai ta da ni duk kuwa da kasancewar Hamma be so haka ba, ni kuma na lake sai na tafi kuma Momy ta saka baki a dole ya kyale ni a bisa sharadin kwana biyu zan dawo saboda shiga kotun da za ayi. A cikin garin Kaduna aka kai Humaira Rukaiya kuma a kano gidan da Hamma ya kama musu Muhseen kan a Abuja ya tare da matarsa. A gida mai kyau aka aje su su kansu sun san an musu gata, daman mai hakuri mawadaci hakurin zaman auren da Ammy tai ma jureya da tarbiyantar da yayanta da kuma cirewa rai kwadayi sai gashi Allah ya bawa yayanta inda za su huta kuma su jidadi.
Kwana na biyu a Agadez din bayan kai su Zainab da Batula muka dawo tare da Mama da wasu da suka rakota saboda jin cewar zama na karshe ne za ayi, washe garin ranar da muka dawo ya muka tafi sokoto har Hamma saboda case din. Ranar da muka isa ranar aka shiga kotun wani abun da zai baka mamaki har da yan jarida abun ban san taya suka ji ba ko da yake abun duniya baya boyuwa. Alkalin ya yanke hukunci ne akan kwararan shidu da kuma hujojin da aka gabatar a gaban Alkalin.
Hukuncin shekara ashirin da biyar alkalin ya yanke masa daman tun da aka soma case din aka rufe asibitinsa, sai gashi kuma alkalin ya hada da asibitin cewar a rufe ta gaba daya. Kamar wanda akai aka yi ma albishir da mutuwa haka Doc Asim yai da fuska da ya dafe kansa. Mu kan ran mu fes domin yan yanke masa hukuncin daya dace da shi, sai dai Alkalin ya ba shi damar daukaka kara zuwa kotun Abuja idan yana ra'ayi. Ban yi tsammanin zai yi hakan ba, sai ga shi lauyansa ya fadi cewar za su daukaka kara zuwa Abuja domin ayi musu adalci a can.
A ranar ruwa ne kawai ban zuba kasa na sha ba akan dadi da murna, amman na yi farinciki sosai kuma na yi ma Allah hamdalla, wani abun da ya kara min jindadi da sunan Hamma be fito a ciki ba, hakan na nufin ya saba siyarda kodar kuma wai Hamma ne kawai ya siyarwa ba, domin idan har zai fadi sunan Hamma to zai fadi na sauran manyan ma da ya siyarwa.
Cikina na cikin wata na tara aka fara zuwa kotun Abuja na daukaka karar da yai a wannan karon ma ba mu muke zuwa ba wani lauyan ne yake wakiltar mu.
Asibitin da na ke awa likitar ta fada min Edd na, tun daga ranar Hamma be sake ba ri na tafi makaranta ba fita ma baya bari nai kullum ina gida idan yana gurin aiki kuma yana yawan kirana wai ai wani lokacin ba a lokacin da suke fada mutum ke kaiwa ba wani sai yafi wani kuma ba zai kai ba, siyayya kayan sakawa ta babu abunda be siya min ba, na jariri ne kawai be yi ba wai ba zai siya na mata a haifa masa namiji ba ba kuma zai siya kayan maza a haifa masa mace ba dan haka sai idan na haihuwa zai hada komai na jariri sai dai ya siya wasu kadan da maza ko mata duka za a iya saka musu. Nikan fargabar inda zan haihu ya hanani sukuni ina ta jin tsoro ta yadda da ko ya za su fito cikina duk girman cikina a ce ta nan da zai fito a duk lokacin da na tuna sai hankalina ya tashi, ni da ko motsi cikin yai sai na ji tsoro balle kuma ace haihuwa, wannan yasa na matsawa Hamma akan ya mayar da ni gida gurin Momy na haihu a can ko kuma ya kai ni Nijar gurin Mama amman ya ki har cewa yake wai ko haihuwa nai a gurin Mama Fulani zan zauna ni kan hakan be min dadi ba domin zan fi son zama a gurin Mama ko Momy.
yana gurin aiki na kira shi a waya na fada masa bana jindadi ina jin cikin yana min motsi sosai kuma ina jin ana sukana a baya, da sauri ya zo ya dauke ni muka tafi asibitin, sai aka ce mana ba haihuwar ba ce haihuwar dai tana kusa amman ba ita ce, haka muka kwaso muka dawo gida tare da maganunguna da suka rubuto mana. Sai gani washe gari kamar ba ni na yi kwaliyata na chakire kamar ba ni ba, bakina ya sha lipstick ga wani uban turaren dana zuba na sha doguwar rigar shadda ta na yi daurin dankwalina ture ka ga tsiya. Sannan na shiga kitchen na girka mana jalof din shimkafa da vegetables, ban na sauke na dawo dakina na dauki cingan na saka a bakina sannan na fito falo na zauna rike da wayata ina duba whatspp.
Ina jin lokacin da Hamma ya faka motarsa ya fito ya murdo kofar falon ya shigo hannunsa da leda.
“Sannu da zuwa”
“Kai kai kai Babyna wannan kwaliya fa? Acancan ai wannan kwaliyar kamata yai ace tukuici za a baki, kuma ba abun a baki tukuici ba ga ki da tulelen ciki, da na taba ki kadan ki fara kuka kina cewa bani da tausayi”
Dariya nai na unkura na mike tsaye na mika masa bakina mukai wa juna kiss kamar yadda muka saba sannan na karbi ledar hannunsa.
“Gaskiya kin yi kyau babyna”
“Na gode”
“Just”
Na kanenn masa ido kamar yadda yake min sai ya kyalkyale da dariya ya rikoni ya zagaye hannayensa da cikina.
“I love you, sarkin raki”
“Aiko ina da kokari”
“Za mu gani idan za ki haihu”
“Ai ba zaka gani ba, idan zan haihu sai dai na baka labari”
“No ba zan yarda ba, ba za ki haihu hannun namiji ba kuma a gabana za ki haihu da ni za a shiga, kin san fa ance akwai likitocin da suke ketawa mace haddi idan za ta haihu kuma ni ba zan yarda wani ya ganki ba, sai dai mace yar'uwarki”
Murmushi nai daman na san za a rina yadda yake yawan nuna kishinsa ba zai iya yarda wani mijin ya karbi haihuwa ta ba, ko jiya da muka je asibitin sai da ya saka aka nemo masa mace ta duba ni. Muna cikin cin abinci yake labarta min an saka auren Amina da Husna on 14 Oct.
“Eyyy kamin lokacin na haihu sai na yi gayu”
“Da goyon?”
“Kai zan bar ma shi ai”
Yayi murmushi.
“To Maryam fa?”
“Maryam har yanzu dai bana jin ta samu wani da ta samu da Mama ta fada min”
“Kai har ta bani tausayi Wallahi, ba dadi ayi ta ma wasu aure ana wuce ka”