← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 45 OF 143

Sashe 45

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

“Pretty karki sake wanka Garden kin ga ke macece ba namiji ba, i'm sorry dazun na kasa dauke idona akanki kina da kyau gaskiya ba zan boye miki ba kina da abun da ake so a jikin mace kin san ni bana gani nai shiru, amman dai karki sake wanka a garden”

Kunya ce na ji ta rufe ni, ni har na manta da zancen ya ganni ina wanka dazun amman yanzu ya tuna min sai na ji babu dadi.

“Bana son wanka a bandakin mai gadin ne shiyasa”

“Be ma dace ki yi wanka a can ba, shi ma ai namiji ne, idan za ki yi wanka ko wani abu ki shiga bangaren Mama ki yi”

“Ai kasan Mama Fulani ba zata yarda ba, dukana ma za tai”

“To ki shiga bangaren Ammy ko kuma ki zo nan idan ina nan zan fita naje part din Mama Fulani har ki gama, amman karki sake wanka a garden”

“Tau”

Na fada a ladafce sai yai murmushi.

“Good girl”

“Aisha.... ”

Kamar daga sama na ji kiran da muryar Aliyu, yadda ya kiran sunan sai ka rantse da Allah shi ya rada min shi, juyawa Ya Muhseen yai yana kallonsa ni kuma na saki mopper na nufo kofar dan ganin mai kiran duk kuwa da muryar mai kiran na karantar da cewar a hasale yake. Aliyu ne tsaye a kofar falon fuska a hade.

“Fito”

Ya fada a tsawace.

“Mama fulani ce ta ce na gyara part din Ya Muhseen”

“Fito na ce kar na sake ganin kin zo nan”

Ta fada da kakkausar murya.

“Kamar ya?”

Ya Muhseen ya tambaya, sai Aliyu ya watsa nasa harara.

“Haka kawai zata zo nan ta kebe da kai da sunan wani sharan daki”
ZAKI

By Khadeeja Candy

24...

Kadan-kadan yake tuka motar yana ta kallo har na soma tsarguwa na takure guri daya, sai yai murmushi ya kai hannunsa ya bude wani dan gurin ya dauko wata yar karamar kwalba mai kamshin gaske ya miko min turare a cikin mai shegen kamshi na kamfanin Awwaba scent ya miko min.

“Wannan turaren tun da na siye shi ban yi amfani da shi ba, amman dai kanwata ta fada tace yana da kyau sosai”

Ina karbar turaren kamshi ya baibaiye tun kan na bude.

“Yana da dadi?”

Na gyada masa kai alamar eh sai yai murmushi.

“Miyasa baki son yawan magana ne? Ni fa labari na ke son ki ba ni”

“Labarin me?”

Na tambaya ina dago kai na kalleshi sai ya sakar min murmushi.

“Mi ya kawo ki aikin garin Abuja, maman ki ta saka ki?”

“Aa ni na saka kaina, bata son zuwan nama ma”

“To miyasa kika zo? Kina ganin sha'awar Abuja ne?”

“Mutum ya taba sha'awar abunda be taba gani ba?”

Ya daga kafadunsa.

“Maybe kin san wani idan yana jin labarin gari sai yaji yana sha'awar zuwa wata rana”

“Ban taba sha'awa ba, ban taba tunanin zuwa ba, ni da bani da lokacin fira ma wa zai ba ni labarin Abuja?”

“Kamar ya kina zuwa makaranta ne acan?”

“Aa na yi karatun primary daga bakin class 4 na daina zuwa har yau”

Kallon yai da mamaki.

“Mi ya hana ki zuwa”

“Ba komai”

“Ba komai hakan nan kawai zaki ki zuwa makaranta? Ba ki son karatun ne?”

“Ina so”

Shiru yai ya cigaba da tukin can kuma ya kalleni ina ta wasa da kwalbar turaren daya ba ni ya ce.

“Gashin nan na ki na son gyara kin taba gyara shi?”

“Eh ina wankewa”

“An taba wanke miki a shago?”

“Bari na biya da ke shagon da ake wankewa Ilham sai a wanke miki na ki”

“Da gaske?”

Na fada ina wara ido daman na dade ina sha'awar a wanke min gashi a shago.

“Yes yar fara”

Ya fada yana dariya ni kuma nai murmushi, ban kara ce masa komai ba shi ma be ce min sai dai ina lura da yadda yake ta kallona har muka isa gaban wani katafaren shago mai hotunan mata da gashi irin nawa su da kitso wasu kuma an gyara musu ya sauko har gadon bayansu. Sai da ya fara fita sannan ya zagayo ya bude min motar na sauko ina rike da turare sai ya mika hannunsa ya karba.

“Kawo a aje turare har mu dawo”

Ba musu na mika masa sai ya maida kwalbar cikin mota ya rufe motar sannan na nuna min hanyar shagon da hannu.

“Muje”

Ni ce a gaba shi yana baya har isa bakin kofar shagon, sai ya kai hannu ya bude min kofar na shiga sannan ya shigo shi ma, dukan wadanda suke shagon kabilu ne ba hausawa ba, da yaren turanci yai magana da su sai wata ta zo taja hannuna ta kai ni wani kebantaccen daki mai kamar falo an gyara ko'ina kamar kana gida, kujera ta ja mi na zauna gaban wani katon madubi shi kuma ya zauna a kujerar dake bayana ya dauki magazine yana dubawa. Wani garin tawul ta dauko ta dora min a wuya sannan ta cire dankwalin kaina tana fadin.

“Wow.....”

Har Kamal ya dago ya kalleni ta cikin madubi ni kuma nai murmushi sai shi ma ya mayar min. Sai da ta fara raba kaina gida hudu ta gyara ko wane bangare sannan ta saka na taso daga wannan kujerar na koma gurin wata na ta shafa mai.....
Mun kusan awa daya a shagon sannan aka kammala gyaran gashin, kamar wata ba indiya haka na fito gashin kaina ya kwanta irin yadda na indiyawa yake yi, yana ta sheki ni kaina sai da ya burge balle kuma Kamal da ke ta kallona ba ko kyata ido. Wayarsa ya saka yana ta dauka ta hoto, ita kanta wace ta gyara min gashin sai da ta dauki hoto a wayarta, sannan ya biya kudi muka fito yan matan da ake ma gyaran gashin sai kallon nawa kan suke, domin kowa ya ga nawa gashin yasan cewa nawa ne ba kamar su da ke sakawa fake ba. Wannan karon ma shi ya sake bude min motar na shiga ya rufe sannan ya zagaya ya shiga mazaunin direba ya tashi motar muka hau titi.

“Kina da kyau sosai Mamana”

Ya fada ba tare daya kalleni ba, ni kuma na kalleshi ban ce komai ba ya maida dubana gurin titin.

“Har yanzu baki bani labarin dalilin zuwanki Abuja ba”

“Aiki na zo yi"

Na fada ina shafa gashin kaina da ke burgeni ina jin kamar ba nawa ba ne.

“Mu yan asalin yola ne, fulanin yola ne mu, mahaifina ma'aikacin gobnati ne mai rufin asiri, a hannunsa na taso ina da yayye maza biyu da mace daya ni ne na hudu kuma ima da kanen biyu mata, a unguwar da nake zaune babban yayanmu da Matarsa ne a gidan da kuma Mahaifiyata da kannena sai dai kowa bangarensa dabam, yayana dan majalisa ne a nan Abuja”

Na kalleshi.

“Ka ce min kai talaka ne ashe ba haka ba ne”

“Yes ni talaka ne kamin yanzu, a lokacin da muke yola mun sha wahalar rayuwa, domin mahaifinmu ya rasu a lokacin da muke da bukatarsa, karatu ya so ya lalace sanadin hakan, amman talakawan nan da nake fada min na unguwarmu su suka hada kudi suka komai na makaranta domin suna ganin kimar mahaifina sosai, dattijon arziki haka suke kiranshi, da taimakon da suka min na kawo a inda na ke a yanzu, kin ga ko ai dole na san darajar su”

Yana fadar hakan ya faka motarsa gefen titi ya juyo ya kalleni.

“Fada min ke fa?”

“Ni ba yar kowa ba ce, babana ya rasu ina da kane Lukman shi ma ya rasu, daga ni sai Mamana muka rage”

“Ayyah sorry"

Ya fada cikin yanayin da ke nuna tsantsar tausayinsa a kaina.

“Kika ce ke kika kawo kanki aiki a nan miyasa?”Ban boye masa komai ba face zancen cire kodar mahaifiyata shi ma saboda ina tsoron kar Mama Fulani ta ji ne ta koreni dan sanan ba zata yarda cewar danta ya cirewa mahaifiyata koda ba, sai nai ma Kamal wata karyar da cewar ulcer ce take damun mahaifiyata na ke nema mata kudin magani, tsantsar tausayin da na gani a idon Kamal da fuskarsa ban taba ganinta a fuskar wani mai ganin tausayina kamar haka ba. Da kansa y ciro tissue paper ta gaban motarsa ya miko min.

“Share hawayenki”

Na karba na share hawayen da suka ki su tsaya min saboda tuna da irin rayuwar da na baro da kuma kalubalen da ke gabana.

“Kin yi kokari sosai Ataa kin zama jaruma, aiki a titi kula da mahaifiya ba abu ne mai sauki ba ko a gurin babba balle ke da ba zaki wuce 16 to 17 years ba, amman ina yan uwanki ba ki da kowa wanda zai iya kula da ku bayan rasuwar mahaifinku? Ya kamata ace sun kula da mulallinku ba su bar ku kuna ta bara ba”

“Ban san inda kowa nawa yake ba, mahaifina be taba firar kowa da ni ba, haka ma Mamana bata taba fada min wani abu daya shafi danginta ko dangin mahaifina ba, iyakar abunda na sani suna nijar”

Ajiyar zuciya ya sauke yana ta kallona sannan ya tashi motar ya hau titi muka cigaba da tafiyar, be sake ce min komai ba sai kallona yake har muka isa gida, a bakin gate din su Mama Fulani ya faka motarsa ya mika hannunsa baya ya dauko ledodin da aka saka masa a bayan mota ya miko min.

“Ungo wannan na ki ne”

Kin karba nai.

“Aa Mama Fulani zata iya min fada idan ta gani?”

“Ai ni na baki kuma yanzu da na aje motata a gida zan shigo cikin gidan a nan zan ci abinci rana”

Na saka hannu biyu na karba, sai ya saka hannunsa aljihu yan bandir din dari biyu ya miko min.

“Ungo wannan ki aje mana, za mu fara tarawa kudin maganin Mama”

Kallonsa nai baki a sake sai nai saurin girgiza masa kai.

“Aa ba zan karba kudi ba, idan Mama Fulani ta gani dukana za tai kuma aikin da nake saboda na tara kudin na ke za su iya idan na tara na wata uku”
Chapter 45 · 0% Book details