Sashe 140
Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read
Ya fada yana kanne min ido kamin ya fada min cewar mai masa gyaran fulawoyi da gida ne yake gyarawa. Washe garin ranar da muka so ya kama Saturday a ranar a aka kai lefen a wata unguwar masu hannu da shuni da ke garin abuja, lefe na mai amsa sunan lefe da babban gida na masu naira irin dai wanda Mama Fulani take kwadayi kuma take so. Sun yi mana goma ta arziki bayan kayan ciye ciye har da kudi masu yawa suka hadu mana. Ni dai ina so ganin yarinyar domin Hamma ya fada min wai ya ganta a wayar Mama Fulani tana da kyau sosai.
Bayan mun dawo mun huta ina bangaren Ammy na shiga whatsapp dina sai ga hotonta da aka hada da na Muhseen da kuma lefen ana tayata murna a status din Husna na gani, gaskiya kyakkyawa ce sosai fara mai jiki sai dai ba sosai ba, ban yi mamakin kyauta ba daman can irinta yake ai, wato mace mai kyau na san da hakan tun daga lokacin da aka kawo ni aiki a gidansu, kyau na cikin abunda yake burge Muhseen, kuma ba laifi ba ne dan ya so mace mai kyau musulunci ma ya yarda a auri mace dan kyauta.
Daga gidan su Mama Fulani aka aiko mana da na mu kayan baikon Amina, ta bangaren Abbah da yake akai komai da shi, a lokacin da aka kawo mana na mu na sha dariyar Hamma saboda korafin da ya rika yi wai nawa ya fi na shi yawa, kuma haka din ne nawa dabam mai yawa na sa kuma ba mai yawa sosai ba, a waya Momy take fada min wai mai yawan shi ne nawa wata kila ina da kawaye da zan rabawa na jidadin da Momy ta kwarrama ni ta tabbas da ace ina da kawaye a nan Abuja babu abunda zai hana ni raba musu baikon kanwar mijina. Sai dai kasancewar kawayen da nai sabo da su yan makarantar koyon girki ne kuma duk a sokoto suke babu daya a nan.
Sati daya da kai lafen Muhseen aka kawo baikon Rukaiya na ni kadai ba, har Hamma sai da yai mamakin jin zancen ta samu miji domin shi kansa be san wani na nemanta ba, daga ni har shi har su Momy mun ji abun ne daga sama, a ranar da Abbah ya fada masa za a kawo baikon sai da ya kira Mama Fulani a waya yana tambayar anya dai an yi bincike akan mutumen kuma an san waye shi? Ina jin lokacin da Mama Fulani take fadar wai ai yanzu an daina zufafa wannan binciken da ake kuma yaron dan kano ne iyayensa sun zo har da wamban kano (Fake Name) ya fada musu shine babansa kuma sunansa yake bearing, dan haka ba sai an fadada bincike fa, aiki kuma shine manager a gidan man da ke nan Abuja. Tana ta fada masa irin kudin da ya kashewa Rukaiya daga haduwarsu zuwa yau ya kashe mata kudi masu yawa, gashi kuma Abbah yana zancen hade yayan Ammy su uku da Muhseen ai kara a hada da Rukaiya tun da ita din ta samu kuma yace a shirye yake.
Ni kaina na yarda da zancen Mama Fulani cewar mai kudi ne tun daga kan kayan baikon da ya aiko kayana masu yawan da gaske irin waenda ake kaiwa a manyan gidajen, a ranar Momy ta zo har da Daddyn ma da wasu yan'uwan Mama Fulani da ke Yola.
Kamar yadda Hamma yai min alkawarin saka ni a wata makarantar be saba alkawarinsa ba, duk kuwa da kasancewar cikin nawa wata biyar ne ya lokacin har da yan kwanaki a kai, amman a haka ya aminta ya saka ni a Royal Academy, wata makarantar kudi ce da ke nan Abuja ta masu koyon karatu da rubutu da kuma waenda ba su samu damar kare karatunsu ba kamar ssce.
Karfe tara ake zuwa a taso sha biyu ga irin mu ga yan sss2 da 3 kuma suna zuwa da safe misalin takwas su tashi biyu saura. Gaba daya makarantar da turancin ake magana tambaya da kuma bada amsa ko da kuwa tsakanin dalibi da dalibi ne, ma ji tsoro sosai ganin irin ka'idar makarantar sai dai hakan ya saka na kara dagewa da maida hankalin wajen ganin nima na iya turancin kamar sauran, ba musulmai kadai ba ne a makarantar akwai kistoci ma har da waenda ba hausawa ba, akwai matan aure da yan mata a ciki akwai maza akwai mata sai dai bangaren mazan dabam matan ma bangarensu dabam, ko a cikin matan daga ni sai wata haulatu ne muke saka niqab domin ita ma ina jin mijinta irin Hamma ne mai tsananin kishi, ba niqab kadai ba har safar kafa da hannu Hamma cilasta min sakawa yai yi. A dole kuma mai hakan saboda ina son karatun. Shi yake kai ni ya dauko ni idan mun tashi, idan ma ba shi da time sai dai ya ce na jira shi idan ya gama ya zo ya dauke ni, wani lokacin da yar kula ta abinci kamar wata karamar yarinyar yar makaranta ko da yake ba ni kadai na ke zuwa da abincin ba, kuma duk wanda ya gan ni da abincin idan ya lura da yadda cikina ya fara dan tasowa zai san ai lalura ce, domin kuwa cikin nawa na kara girma cin abincin na karuwa abun har mamaki yake ba ni. Sosai na ke son zuwa Nijar gurin Yan'uwan Mama da na Babana na ga waenda ban gani da Waenda kuma na gani na kara ganinsu, duk kuwa da kasancewar sun zo a baikon da akai ma Zainab da Batula na cousins, sai kuma na Humaira da akai kwana biyu da yin na su, aka saka lokacin auren daya da na Muhseen kamar yadda Abbah ya fada cewar yana son ya hade su yai musu auren a tare a bar Maryam kawai ita da bata samu mijin ba.
Karatun da na ke a yanzu ya fara zame min kamar da wahala saboda na hada biyu ne, da yamma ina zuwa wata makarantar islamiya ta matan aure wacce ake zuwa karfe uku a taso budu da rabi, a can ma na yi kawaye amman iyakana da su a makarantar wai kuma a waya da muke chatting. Ga kuma cikina da shiga wata bakwai da shi a yanzu, ba wata wahalar na ke ba bayan nauyin da cikin ke min sai kuma yawan zazzabin da tsandar abinci, sai dai bana nunawa a gaban Gogan nawa saboda na san halinsa yana ganin wani abun zai iya hana ni karatun ko yanzu da be ga wani abun ba yana fadar wahalar tana ma cikin yawa balle kuma ya gono ai a take zai hanani zuwa makarantar.
Wani iko na Allah sai na fi gane makaratun arabiya fiye da na bokon da na riga farawa kuma na dan gane wasu aabubuwan a baya domin na iya karanta hausa tun kam na shiga makarantar, bokon ma ba zan ce bana ganewa ba amman na fi gane na arbiyan fiye da na bokon.