← Book details Zaki Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 31 OF 143

Sashe 31

Zaki Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ko ba ita ba be ji zai amsawa kowa wannan tambayar balle kuma ita da yake gani ita da banza duka daya. Gilashin motarsa ya tayar ya soma driving a hankali ya bar a gurin tsaye tana kallonsa har ta daina hangosa.
   Daga Clapperto road ya dauki hanyar arkilla wato family house dinsu wajen Momy. Yanzu kan ya gane dalilin daya kai Ataa asibiti, wato maciji ya tsari mahaifiyarta a can ne Doc Asim ya ganta ya cire mata kodar, amman abunda ya fi tsaya masa a rai zancen bukkar nan, how on earth za ace akwai mutumen da be da gidansa kansa, even ma ace mutum be da gidan kansa ai akwai gidajen haya da zaka iya biyan kudi ka zauna, amman ya za ace a bukka suke zama, samun kansa ya kasa yarda da abunda yarinyar nan ta fada masa. A daidai gate din gidansu ya tsaya ya danna horn sau daya kan kace kwabo aka bude masa gate din ya shiga, a harabar gidan ya faka motarsa ya fiddo wayarsa ya kira Doc Asim, ringing daya ya picking a tunanin Doc Asim zai masa maganar ciwon Rahma ne ya ce ya tashi ko wani abun dabam amman a mamakinsa sai ya ji ya aika masa da wata tambayar ta dabam.

“Yarinyar da ka cirewa mhaifiyarta koda miya kawo ta asibitin ka?”

“Maciji ya tsari mahaifiyarta, suka zo bata da kudin magani ta ji ana zancen koda ta ce zata siyar”

“Ba siyarwa tai ba Asim, cirewa tai da karfin tsiya, da siyar tai yi kudin da zaka bata za su isheta tai rayuwa na wani lokaci”

“Ina shaidar siyar da ita da tai, kuma be kamata wannan ya dame ka ba, kai dai ka ce kana son koda kuma an samo maka ba an wuce guri ba”

“Da na ce ka kawo min ban ce ka zalinci wata ba ai, maciji ya sari mamanta sai ki amfani da wannan damar ka yaudare ta ko? Mahaifiyarta tana raye ko ta mutu”

“Ba ni da masaniya yanzu”

Aliyu ya kashe wayar tare da bude motar ya fito, yana tuna lokacin da yake tare da kanwarsa Humaira har take mikawa Ataa hannu ta ce ta bata wayarta da ta dauka. Be samu kowa a falonsu ba, kai tsaye nufi dakin Momy da yake hangowa a bude, yana shiga ya sameta tana gyaran gadonta, da sallama ya shiga ya zauna a kujear da ke facing din gadonta.

“Momy yau ke kike gyaran gado da kanki?”

“To yau duk da wuri suka fita, kuma har yanzu ba su dawo ba”

“Ai ba kullum za su rika aiki ba, su ma suna bukatar hutu, da dai kin samu mai aiki ai su ma sai su hutu”

Zaunawa Momy tai tana kallonsa.

“Shi gyaran gado shara wanke wanke girki har wani aiki ne? Idan ba su koya a gida ba so kake su je su yi ma mazajensu irin na matarka? Ai ba kowa ne namiji ne irin ka ba”

Yayi murmushi.

“Momy ita ma fa saboda ciwo ne, bata saba da wahala ba”

“Kula da gida da miji shine wahala? Wasu na can Allah kadai ya san abunda suke kamin su samu su ci ma, wasu ba su kaita ba amman suna can sun iya kula da miji, kai yanzu baka san dadi mata ba sai ka samu mai kula da kai”

“Rahma ma tana kula da ni Momy, ke ce ba ki gane ba”

Tabe baki Momy tai

“Dazu mun yi waya da Fulani ashe taje dubai har ta dawo ban sani ba, ta kirani tana ta min fada wai na dauke mata yaro”

“Eh ta kirana kwanan baya tace min zata je dubai ashe tafiyar ba mai dadiwa ba ce, ai mun kusa zuwa Abuja Rahma ma ta fara min maganar”

“Ya dai kamata kan ka koma gurin aikinka, kuma kasan Fulani ba son take kai nisa da ita ba”

“Zan koma”

Sai yai shiru for some minutes sannan ya kalli Momy ya ce

“Momy wai ashe akwai mutanen da basa da gidajen zama har sun kashe bukka? I find it so hard to believe”

“Ban fahimta ba, wa ya fada maka?”

“Mamy yarinyar nan da na ke fada miki, wai ashe gidan da take zaune gidan baban Rahma ne, sai maciji ya sareta da ya samu labari sai ya koreta sanadin hakan aka kai mahaifiyar asibiti ina jin a can ne Doc Asim ya cire mata kodar aka sakawa Rahma, wai can din bukka suke kafawa su zauna”

“Dan wajen Fulani ina ka samu labarin nan?”

Momy ta tambaya jikinta a sanyeye. Sai yai shiru kamar baya son fadawa Momy cewar ya je nemanta ne.

“Just tell me i want to help her, ina zan samu ganin yarinyar nan? An zalince da yawa, tana neman gurin zama ace kuma an yi ma mahaifiyarta haka, mahaifiyar ma tana da rai ko ta mutu? Kuma ace mutumen da ya koreta a gidan macijin ya tsareta a gidan an dasawa yarsa kodar mahaifiyarta, yarinyar nan ba zata taba mantawa da ku ba Dan wajen Fulani kun cucece ta”

Momy ta fada hawaye na sauko mata, zuciyarta ta cika da tausayin Ataa duk kuwa da kasancewar bata taba ganinta ba ko sau daya. Aliyu ya baro kujerar da yake zaune ya zauna kusa da Momy.

“Momy trust me, Wallahi ba da sanina akai mata haka ba, duk laifin Doc Asim ne, nima ta ba ni dan tausayi....”

Momy ta kalleshi.

“Da? Dan tausayi fa ka ce Dan wajen Fulani, sai ka ce ba musulmi ba, irin wannan yarinyar ai kamata yai ma a kwato mata hakkinta”

“Gurin wa?”

Ya fada yana kallon Momy. Sai ta share hawayen da suka zubo mata ta ce.

“Seriously yarinyar nan ta ba ni tausayi, yarinyar da take irin wannan rayuwar sai kuma a sake jefata a wata rayuwar ta wahala, ku kuna cikin farinciki ita an saka ta a kunci”

Ya busar da iskar bakinsa, ba dan tausayinta yake ji kamar yadda ya ce wa Momy ba, tausayinta ne gaba daya ya cika masa zuciya, be taba jin tausayin wata halitta mai sunan dan'adam ba kamar yadda ya ji yana tausayin Ataa a yau, and the most annoying part is be san inda take ba, waya sani ko sanadin hakan ta kara shiga wani halin.

A unguwar yai sallah la'asar sannan ya nufo gidansa, yana ta sake saken zuwa kaduna daga can ya bi ta Abuja ya gaishe da Mama Fulani, sai dai daya tuna da cewar idan ma yaje din be san mi zai ce mata ba sai duk wani karfin guiwa na shi ya zube daga ya yanke shawarar samun wani ya bincika masa a can Kaduna din.

ATAA POV.

Ina zaune a inda Maman Salma ta tafi ta bar ni ban tashi ba su kuma ba su kula da ni ba, ina zaune a guri har na iya gane anyi sallah azahar ta hanyar agogon falon daya nuna karfe 2. Ban san wa zan yi ma magana ba cewar ina son nai sallah ba, domin ban ga fuskar kowa a cikinsu ba, duka yan matan ko wacce ji take da kanta dan ko kallo ban ishe su ba, bana jin cewar idan nai musu magana za su amsa min, ina zaune a gurin ina ta rokon Allah ya kawo min mafita sai ga Inteesar ta shigo sanye da uniform din Islamiya tana kallon inda na ke.

“Ke Ammy na kiranki”

Ta fada min sai kuma ta nufi Anty Maryam tana fadin.

“Anty Maryam makaranta zanje yanzu ba kudin na siyo miki tuwon madara”

Ni dai ban jira na ji abunda Anty Maryam din zata fada mata ba, na mike tsaye na nufi kofa na fita da sauri kamar zan fadi. Hanyar da naga Maman Salma ta bi farkon zuwan mu na bi na shiga part din Ammy da sallama, sai ta amsa min da far'arta kamar dazun har hakoranta biyu na makka na bayyana, na sake gaisheta ina risinawa kasa.

“Lafiya kalau ya ma sunanki?”

“Aisha amman Ataa ake kirana”

“Masha-Allah ashe Mamana ce, fatar dai kin iya yankan allayahu ko?”

“Na iya”

“Da kyau to shiga kitchen gashi can sai ki yanka min ki wanke kinji ko?”

“To amman ban yi sallah ba”

Sai ta nuna min bandakin da ke falon.

“Shiga can ki yi alwala”

Na nufi inda ta nuna min, a lokacin da na shiga sai na samu komai tsaf kamar ba a taba shiga bandakin ba, a kasa nai alwala domin na hango akwai hanyar ruwa a gurin sannan na fito na shimfida dankwalina kusa da kofar bandakin nai sallah, sannan na nufi kitchen ina shiga na samu allayahu a kwando na dauka na gyara na saka wuka na yanka kananan sannan na wanke mata na aje kamar yadda ta bukata na fito daga kitchen din.

“Na kare”

“Yauwa sannu ko, za ki iya tafiya”

Na juyo ina ta jin kamar nai zamana a part dinta ko ba komai zan fi sakewa fiye da part din Mama Fulani da ba su san darajar mutane ba. Haka na dawo part din cikin rashin jindadi da na dawo ban samu kowa a falon ba sai tv, a inda na zauna dazun na sake zama sai na raba da kujera saboda na jidadin jinginawa, haka na zauna a gurin har la'asar ba a bani abinci rana ba, da akai la'asar ne na unkura zan tashi sai na ji an turo kofar falon an shigo, waigowar da zan yi sai na ga Muhseen, murmushi ya sakar min ya karasa inda take nake yana fadin.

“Tun da na ganki na ke ta tunanin inda na san fuskar nan take, sai yanzu na tuna da na taba ganinki asibitin uduth ko? Kin tuna?”

Na dan yi shiru alamar tunani sannan na gyada masa kai alamar na tuna.

“Good girl, ashe zan sake ganinki, kin ci abinci?”

Na girgiza masa kai alamar ban ci ba.

“To kin yi sallah?”

Nan ma kan na girgiza masa sai yai murmushi.

“Ba ki magana ne hala?”

Na yi shiru ban ce masa komai ba, na yi kasa da kaina.
Chapter 31 · 0% Book details